🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺 Story & written By mmn Fareesa GODIYA... godiya ta tabbata ga ALLAH (S W T) tsira da amincin ALLAH su tabbata ga annabi (S A W) da ahlayensa d sahabbansa . GARGADI...banyarda wani ko wata yajuyamun novel ta kowacce sigaba.in kunne yaji ,jiki ya tsira.. BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM P1 Not edited Kyawawan Yan mata ne guda3 ketafiya anutse.suna fira ko waccensu hannunta rik'e da tulu da alama d'ibar ruwa zasu.. Mitsss wadda ake Kira mero acikinsu taja tsaki "sakamakon hango dabar samarin karkarar tasu datayi"hade da cewa Ni wlh banison bi tanan haryar,sbd yarima HAMZA da abokansa kunsan ba mutumin kirkibane bbu abinda ya aje sai yima Yan mata da zawara FYAD'E Kuma mai gari yasani amma ya k'yalesa...yo har matan auren bebariba wlh cewar indo"yyinda RIYANATU dake gefe batace komaiba." K'arasowarsu gab dasu yarima HAMZA yasasu yin shiru hade da yin sauri Dan suwuce lfy"Dan beda mutunci. Yarima kuwa Yana atsakkiyarsu Yana isa da gadarar shi. Wai shi Dan boko Kuma D'an me gari,sbd duk k'auyen acikin samari bbu Wanda yakaisa ilimin boko da wayewa dg shi sai GALI..tun dg nesa idonsa yasauka kan riyanatu dake tafiya cikin nutsuwa da sanyin hali hade da kamun Kai" ..bbu bata lokaci yasaka yaronsa guda yatsaidata.. Yan mata yarima HAMZA na mgn ! yafad'a yana nuna riyanatu dake tafiya bata ko kallesaba,yyinda su indo jikinsu ke kakkarwa sbd tsoro suna kallon riyanatu datak'i tsayaawa...yaron yyi saurin tare gabanta...wata doguwar tsuka taja hade da aikomasa da harara ta wuce abinta... kallon mamaki su indo suka bita dashi , yyinda yaron yanufi gun yarima HAMZA Dan sanar masa. Tun kafin yyi mgn yarima yad'aga Masa hannu alamar beson ji sbd duk abinda riyanatu tayi akan idonsa.. Lumshe ido yyi Yana mugun mamakin wannan yarinyar Yar uban waye ce agarin nan be?" kamarshi yasa atsaida ita tak'i tsayawa sbd ita t isa...mittsss yaja tsaki hade da mik'ewa tsaye da nufin tafiya, yyinda yaransa suka tashi ,ya girgiza Masu kai . alamar beson abisa...salisu abokinsa dake gefe yace Kai gsky yarinyar can Yar renin wayoce wlh lallai mutumin batasanka bane shiyasa...wani munafikin murmushi yarima yyi hade da cewa hmmm yau kau zata sanni Dan wlh yau din nan sai na rabata da darajarta Dan agarin nan bbu macen data isa tamun haka ...bejira amsarsaba da sauran abokansa daketa mgn yabi bayansu riyanatu.. Bangarensu riyanatu kuwa suna barin Gurin su indo suka kama mata fad'a kan miyasa tayi hakan?"bacin tasan ko waye yarima da mugun halinsa Amma hartayi wannan abin.,,,, Cikin dakiya tace be isa yamun abinda ALLAH bemunba bana tsoronsa ko kad'an Dan haka kubar maganar. "Mairo tace inda zakiji riyanatu kije kibasa hakuri sbd gudun abinda zaije yafaru Dan ALLAH" Murmushi riyanatu tayi mai sauti tace hmmm mairo kenan bbu inda zani balle har nabasa hakuri Dan banmasa laifi ba"indo tace Amma dakin sani baki k'i tsyawa...aitariga ta makara tunda har ta rigada tayi mun haka nikuawa ayau Zaki gane bakida wayo ko ke Yar uban waye agarin nan...cewar yarima a hassale cikin fushi" Gaba d'aya suka juya banda riyanatu suna kallon sa...cikin bacin rai riyanatu tace dakata mlm kada kasake hadawa da iyayena ,ubanah na kabarinsa dan ha.....saukar Marin dataji yasakata yin shiru tana kallonsa" nunata yyi da yatsa hade da cewa lallai yarinya bakinki yajamiki ke har kin isa Ina mgn ki mayarmun to wlh yau saikinyi nadamar haihuwarki a k'auyen nan fuuuuu ya wuce abinsa... yyinda riyanatu dake rik'e da kunci tana kuka hawaye ya wanke mata fuska,nan su indo suka ba ta hkr hade da cewa data sani ta tsaya Allah yasa kada yyimata mugun Abu Dan sun tsorata da kalaminshi ,Amma ita bbu hakan atare da ita. Byn sun gama d'ibar ruwan ko wacce ta wuce gidansu jiki asanyaye. Riyanatu kuwa ko afuska bata nuna ma umma komaiba,Amma Abu daya yatsaya mata arai ,shine sai kinyi danasanin haihuwarki agarinan yau...,byn ta aje ruwan," nan tashiga hidimar aza girkin dare Wanda da k'yar umman tahada kudin akasiyo abin bukata sudafa sbd basu dashi. Sai gab da magrib ta ida tuwan ta gyara Gurin tayi alwarlal magrib ta nufi daki ta data Sallah" Itama umma alwarlal ta Fara tana Duke taji anyi sallama"ta d'ago tana amsa fuska asake sbd ganin gali D'an aminiyarta ,saidai jikinta yyi sanyi ganin arikice yashigo gidan Ko gaisawa basuyiba arude yace umma Ina riyanatu?" "Da sauri tace lfy dai ki?" Arikice yace bbu umma ,Dan ALLAH duk yadda zaayi cikin 2 kuyi guda ko kubar garin nan ko kada ku kwana agidan nan... Cikin kosawa umma tace dan ALLAH kamun bayani mana! Sbd mezamubar gd?" "Gali yace sbd yarima HAMZA nason yaketawa riyanatu haddin ta" Inna lilahi wa Inna ilaihir Raju un" umma ta fad'a tana kuka,hade da cewa akan wane dalili,ko kuwa hakanan sbd zalinci anganta arainiya ko??" Cikin tausayinsu gali yashiga sanar da ita komai kasan cewar agabansa yarima HAMZA yyi maganar,Amma be nuna yasan riyanatu ba kuma( Yana sonta be nuna mata)hakan yasa hankalinsa tashi sbd yasan yarima mugun busurune... Sannan yyi ajiyar zuciya yace umma ga shawara ..adedenan riyanatu ta fito dg daki da alamar ta idar da sallar ta nufosu tana kuka.. Da sauri umma taceinajinka" Yace muje gidanmu ku kwana scan kafin da asuba kubar garin sbd wlh kinsan zai iyayin komai akanku sbd ubansa bazaice Masa komaiba " Umma da riyanatu na kuka suka kwashe kayan sawarsu agana,da abinda suke bukata suka saka a buhu ,Saida akashiga sallar isha'i sannan suka kwashe kayan su ,sukabar ledar k'asa d katifa suka rufe gida hade da nufar gidan Inna mariya mahaifiyar gali,yyinda uma gabanta ke faduwa svd batason wane gari zasu ?"kauye ko birni?"Dan xuwarta bunni guda alokacin yayarta nacan to yaxu Kuma batasan Ina yayarta takeba ta mutu ko tana raye.. Da wannan tunanin aran umma,suka iso gidan Inna mariya, yyinda riyanatu keta kuka da adduar ALLAH yakubutar da ita dg sharrin yarima. Byn zuwansu gidan gali ya ma inna bayani ,salati tayi sbd ta tsorata. ta kalli umma tace ki kwantar da hankalinki bintu insha ALLAH zaku kub'uta sbd inaji ajiki na barinku garin nan alkhairi ne babba,Zan Kira wata zuwaira inada number ta agarin kaduna take can zakuje insha ALLAH zata baku masauki ta nuna muku gari Dan gaskiya nabaki goyan bayan kubar garin nan sbd martabar y'ar ki guda aduniya tak... Ajiyar zuciya umma tayi tace to nagode sosai ALLAH yabiya. Inna tace amin byn komai yalafa zan je nasanar da baffan riyanatu, sannan akwai kudi gurunku?" Umma tace eh a"akwai dubu ukku" Inna tace zanbaki dubu5 ,kukara sbd ai Sanaa Zaki samu acan harki maida riyanatu makaranta ko?" Umma tace eh nagode mariya,Amma akwai busashena zasuyi kudi mai kauri kisiyarmun gali yakaimun kudin "inna tace to,yyinda riyanatu keta kallon su tana tunanin zasubar garinsu zuwa wani gari sbd wani banxa Allah yasa hakan shiyafi alkhairi... Nan Inna ta sa gali ya Kira mata ita da wayarsa. Bbu bata lokaci Inna ta amsa tayiwa zuwaira mai abinci bayanin zuwansu riyanatu d mahaifiyar ta , tace ALLAH yaka wosu lfy. Nan Inna ta musu kwatance insun iso garin yadda zasu gane.. Shikuwa gali yaso yaja riyanatu yafad'a mata sirrin zuciyarsa kafin su tafi amma ganin su Inna sai yafasa. Washe gari tunda asalati su umma sukayi ban kwana da mariya,gali yadaukar musu wasu dg cikin kayansu,yyi musu rakkiya sbd duk ana masallaci bbu Wanda yagansu ,dukda atsorace suke. Be barsuba Saida suka yi tfiya mai nisa har suka iso titi suka hau acaba sannan yajuya yafafi cike d kewar su hade d tausayinsu..alokacin har gari yafara haske... Bangaren yarima HAMZA kuwa da misalin karfe 2:00 am yanufi gidansu riyanatu da yaronsa da yasaka yabinciko Masa gdn su. Suna zuwa....😇😇 Yawan comments yawan typing. Share pls BY MMN FAREESA 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & written By mmn fareesa Not edited Dedicate to my lovely sister hauwau u lado😇😇 P2 ....Suna zuwa gidan suka haura ta katanga , yyinda yarima yasanar da yaronsa yatsaya tsakar gd shi yashiga dg ciki. D'akin dake bud'e ya kutsa Kai ciki Yana dariyar mugunta....turus yyi ganin dakin wayam bbu alamar da mutane aciki sbd yahaske ko Ina da fitila"da sauri yafito Yana cewa taf lallai meke Shirin faruwane?" Yallab'ai lfy dai ko?" Cikin takaici yace tabbas akwai Wanda yasanar da ita da iyayenta zuwa na "amma muddin Ina raye akuma garinnan take to dole burina yacika... Fuuuuu suka fice dg gidan rai bace. Zuwa safiya gari yakarad'e riyanatu sun gudu da ummanta,wasu na tausayinsu wasu na tsinewa yarima sbd dalilinsa suka gudu... Koda baffan riyanatu yaji wanna an lbari da kanin ummanta hankalinsu yatshi matuka sunyi nadamar zamansu garin da me garin garin baya adalciko kad'an, D'ansa na bata d'iyan jamaa amma baya mishi mgn ko tsawatar Masa... ############ K'amshine daddad'a ke tashi a parlourn na turarukan wuta dna air freshener"kallo daya zakama parlourn kasan mamallakansa naira tana kuka agurinsu yahadu ya k'awatu. Wasu masu aikine suka shigo da warmers ahannunsu suna jerawa akan dining table din dkae cikin parlourn...wata hamshakiyar mace ce ta fito cikin shiga ta alfarma tana yauki had'e da takun izza,Yar kimanin shekara45 xuwa 47 ." Cikin girmama had'e da rawar jiki sukace ranki yadad'e ankammala! Cikin bada order ta yatsina fuska tace Ina fatan komai very need sbd kunsan my son akwai k'yankyami,Dan munyi waya yanxun yace sun kusa k'arasowa. Wacce ake Kira da hassu tace insha ALLAH komai yyi lfy yadda kikeso hjy...kafin tayi mgn sunji karar motoci da alamar Wanda ake ma liyafar ya iso, da sauri ta sallamesu, sannan ta nufi kofar fita dg waiting parlou tana wani murmushi Wanda bansan ma'anarsaba.. Gaba d'aya body guard d'insane suka Fara fitowa,shikuwa ogan nasu be fitoba.wata haddiyar motace dake tsakkiyar motocin ita aka bude gidan baya...wani fitinan nan kamshi me saka nishadi yafara gauraye Gurin, kafin santala santalan kafafunsa su bayyana sanye da takalmi sawu ciki . ahankali ya ida fitowa... Wow Masha ALLAH nafad'a azuciya ta sbd ganin guy din hmmm ALLAH yyi baiwar halitta agun kyakykwa wane ajin farko dogo fari...suit ne bak'ak'e ajikinsa Wanda suka haska farar fatarsa da agogo baka daure atsintsiyar hannunsa ,yyinda kansa yasha gyara sai salk'i yake lolx.. Fuska bbu walwala yarika amsa gaisuwar ma'aikatan gdn,daketa aikin gaidasa,sannan cikin takunsa na isa yake tafiya tamkar bayason taka qasa..tuni guard's d'insa suka Fara kokarin binsa . da hannu yyi musu alamar ah ah hakan yasasu dakatawa dg binsa.. Adede step din da zai sadasa da waiting parlou yahadu da momynsa... murmushi yyi hade da nufarta Yana cewa i miss you my lovely mom.. Dariya tayi ta rungumesa suka shige cikin parlourn.;;; Kan 2 seater yazauna Yana k'arewa parlourn kallon yaushe gamo"kafin su gaisa da mom Yana tambayarta abbansa. "Tace Yana hanyar isowa gdn" Tamkar wani yaro ya shagwabe fuska had'e da cewa gsky Abba yadena ji Dani gsky mom ,sbd ai dayazo tarata ko yajira zuwana agd in bezo air port ba" Murmushi tayi hade da cewa hmmm my son yanxunfa ka girma sai Shirin aje iyali kake amma kak'i barin shagwaba ko ?" To ai munatare dashi jiranka ,akamasa Kiran gaggawa a office shiyasa. Had'e rai yyi hade da cewa Ni gsky mom Adena maganar na wani aje iyali dududu shekarata nawa daza'amun aure ne?" bacin kinsan ma zeenat din da kikeso ki auramun sai nan da sheraka 2 zata gama skul Kuma ake tada mgnar yanxun . Girgiza Masa Kai tayi tace hakane ALLAH yakaimu lokacin ,yanxun tashi muje kayi lunch ko. Agogon hannunsa ya duba yace NO mom bara nayi wanka tukum"Ina fatan komai yyi mun ?"kinsan bansan kazanta. "Ahankali ta ce oh me hali baya barin halinsa"ABDALLAH komai yyi need kaje kaduba , shiyasa ma nasaka harira ta nemomun mai aikin dazata ruk'a kulamun dakai kafin kayi aure tunda ni Ina office...kafin yyi mgn abbansa yyi sallama. Da sauri yatashi Yana murmushi ya rungumesa, yyinda abban ke dariya Yana d'anbuga bayansa Yana cewa my son Kai baka girma ko?" Shima dariyar yyi yace eh Mana tunda banida kani ko yayaba, yafad'a yana sakin abban ,yyinda mom tayi tamkar bata parlourn. Abban ne yakalleta Kai Duke yace hjy nadawo ,cikin ko inkula tace ok Ni zanshiga ciki kafin yarona yayi wanka ,akwai inners dina dake a toilet ka wankesu su fita kasan na jiyama basu fitaba ....fuska asake Abba yace to ,bacin wanki bbu aikin dazanmiki?" Iya nan ABDALLAH yaji yabar parlourn Yana huci. Tunanani yake azuciyarsa ,dama har yanxun momynsa Bata Dena juya abbansaba ke nan?" Sbd tsawon shekara4 kenan baya k'asar Yana ingila,Ashe bata bariba...wani mugun tsaki yaja afili yace bazan iyaba saina Miki mgn harda abban shima. Wai meke faruwa ne,miyasa take Masa haka??"shikuma Yana binta tamkar shine matar itace mijin ,cikin bacin rai ya isa part nasa. Duk yadda ma aikatan suka yi kok'arin gyara part d'in Amma shi be masaba sai ma yaja tsaki rai bbu Dadi yyi wankan yasaka jallafiyya Fara had'e da feshe jikinsa turarukan sa .yanufi masjeed sbd time din sallar azuhur yyi... ******************** Su riyanatu kuwa byn sun sauka dg acab'an dayakaisu Tasha ,bbu bata lokaci suka hau motar kaduna.saida sukayi tafiyar awa6 amota tukum sannan suka iso kasancewar dg garinsu zuwa nan da nisa sosai. Tun a Tasha suke raba ido abunka da Wanda ke bako, riyanatu ta tambayi wasu dattijai inane unguwar kawo?" Su bak'i ne.... Nan akasamu mai adaidai aka fad'a Masa inda zai kaisu . Har kofar gidan zuwaira me abinci aka aje su,sbd tayi suna agarin duk asanta shiyasa basu wahalaba. Amatukar gajiye da yunwa suka yi sallama asoron gidan da jamaa keta cin abincin Rana da alokacin befi karfe3 ba na Rana. Sai kallon su ake ganinsu da gana d buhu ansan matafiya nesu , sannan Kuma kauyawa dukda ba irin kauyawannan neba sosai sbd riyanatu tayi boko akauyen su. Cikin sakin fuska suka ida shiga ciki da sallama . Ko da zuwaira tagansu tuni taganesu ta amsa da faraa tana musu maraba. Nan taimusu iso ciki suka ci abinci sukasha ruwa , sannan suka yi Sallah. Zuwaira tabasu wani daki karami agdn tace su saka kayansu suyi wanka su huta ,inta gama sallamar customers sunyi mgn . Amsawa sukayi suna mata godiya da wannan karamcin data musu..,,,, Ana idar da sallar yanufi gd. Part d'in mom yanufa fuska bbu walwala yyi sallama can ciki ciki. Mom ta amsa..... Share pls BY MMN FAREESA 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & written by Mmn fareesa P3 """Mom ta amsa tana kallonsa had'e da mik'ewa tsaye tana cewa kada womy son?" Muje ko kaci abinci,fuska bbu yabo bbu fallasa ya amsa da to mom muje.. dining area suka nufa a tare. Zama sukayi kafin tafara serving nasa. Haka yake cin abincin suna fira da mom jefi jefi yake mgn dan shi mutum ne dabaya son yawan surutu da mgn,saidai fa ta lura D'an nata na cikin damuwa Amma taki tambayarsa damuwarsa . da haka ya ida cin abincin ya Mike had'e da cewa mom bara naje part dina munyi da Hafiz zaizo yanxun...katse sa tayi dacewa atsawace hmmm kana nufin Hafiz yafini k'ima a gurinka ,Ina matsayin mahaifiyar ka har wani banxa yafini daraja agunka ,shekara4 bamu haduba Amma baza ka zauna mu gaisa muyi firar yaushe gamo...iye?"nifa banason abotarku da shegen yaron nan Yana fama da tsawo uwa daran Sallah mitss taja tsaki hade da yin kwafa.. Mamaki abdallah keyi azuciyarsa ,shidai yasan Hafiz bashida wani aibu ko wani mugu hali ,hasalima tun tuni Hafiz naba shi shawarar kwarai da fad'a Masa gsky Amma yalura mom batason abotarsu... K'arara take nunawa Hafiz k'ii.. Wai badakai nakeba ?" Kamun shiru! Kafin yyi mgn abbansa yashigo parlourn da sallama, Abdallah y amsa Yana murmushi had'e d hugging abbansa Yana cewa Abba bara naje part d'ina nadawo mu sake gaisawa. Sannan ya juyo Yana kallon mom ke musu wani kallo mai wuyar fassara yace pls mom i am really very sorry! bejira amsartaba yafice Yana tambayar kansa miyasa yafison abbansa da tausayinsa akan mom bacin ance duk d'a yafison uwarsa akan ubansa.. Da wannan tunanin ya isa part nasa" Murmushi yyi sakamakon hango Hafiz dake zaune kan 2 seater . Shima Hafiz tashi yyi Yana dariya had'e da hugging abokin nasa dayake masifar kauna yyi, sannan suka yi musabiha suka zauna had'e da Fara firan yaushe gomo. Abdallah yakalli agogon dakin yace friend time din sallar la'asar yakusafa! Y'ar dariya Hafiz yyi hade da cewa hmmm big man kenan Ashe har yanxun halayenka masu kyau nanan?" zuwanka turai bai canzakaba ko?" Harararsa Abdallah yyi yace Kai Dan iskane wlh to Dan mutum yafita waje sai yacan za halaye . Amma ai kasan akwai masu canzawa,bama wannan ba kasan bikinmu my feedo ,saura 3 weeks Kuma sbd Kai nakara Masa tsawo Dan biki bbu aminin ango ai bazaiyi armashiba, kaga kaima dg nan ai sakasamu wata fine baby ko jone ko?"cewar Hafiz Yana dariyar shakiyanci... Tsaki abdallah yaja had'e da cewa hmmm kaifa matsalata dakai kenan wlh bakada mgn sai ta mata ai gara su ammi suyi maka aure wlh sbd jarabarka kada wata Rana ka Fara kama ya'yan mutane wlh ,sbd nason inkana mafarki da sabbatun....look mlm dallahai gara Ni dakai,tunda Kai boye taka jarabar kake amma saika rik'a basarwa,garama ka falka dg bacci cikin y'an matan dake tururuwar cewa suna sonka ka fitar da guda musha biki kawai.. Harararsa yyi cikin kosawa yace hmm aini har yanxun Banga macen data isa nace inasontaba bangantaba Dan duk basuyiminba ,ita xeenat tursasawar mom ce kawai yasani kulata da kokarin cusata araina Amma taki ta cusun. Shiru Hafiz yyyi danko shi kanshi wani time din Yana tunanin anya mom ce mahaifiyar Abdallah kuwa?" Sallamar zeenat ce ta katse musu firarsu...tuni gogan naku yyi kicin kicin da fuska sbd ganin yadda tabayyana surar jikinta a fili Kuma Wai itace matar dazai aura.. "Sanye take da riga da wando sun matseta kirjinta have waje "ga gashin doki da tayi attached dashi ,tasaka wani siririn mayafi dashi gara bbu,sai fitinan nan kamshi ketashi ajikinta. Hafiz ne yyi kokarin danne dariyarsa sbd ganin yanda Abdallah yahade rai,ya amsa sallamar ta, had'e da cewa ranki yadad'e munyi fushi gsky sai yanxun zakizo ganinmu . Murmushi tayi hade da cewa hmmm wlh ba laifina bane ,Saida na tambayi baby yaushene time din dazai sauka dg jirgi naje airport tararsa ,amma yaki fad'a. ta fad'ar hakan had'e da nufar tana kokarin hugging nasa...wata zabura yyi hade da kaucewa tafad'a kan kujerar ,fuska bbu walwala tace meye haka baby?" Tabe bakiyyi beyi mgn yadubi hafis yabanko Masa harara sbd ganin Yana tarin k'arya akan dariya nason kuccemasa. Cikin basarwa had'e da danne zuciyarsa yace my zeenat ya kk ya su ummi ??" Lumshe ido tayi sbd jin sansanyar muryarsa mesata nishadi,tuni ta nemi bacin ranta ta rasa"ahankali ta ce lfy lau alhmdllh gsky baby kayi kyau Zama ingila ya karbe ka dukda wani time din Muna video call ,amma sainaga kafi kyau azahiri. Murmushn gefen Baki yyi hade da mik'ewa tsaye sbd tuni Hafiz yabasu guri gudun kada yyi katib'ara.. Ya dubeta ,cikin k'osawa da surutunta yace my zeenat zamu wuce masjid dg nan ...amma aizaku dawo Zan jiraka pls shekara4 fa bamu haduba,tayi saurin katse Masa mgn,adakile yace dg masjid akwai inda zani..amma baby b....pls ya isah banason surutu kada kisamun ciwon Kai malama .hmmmm kodai gun wata zakaje ,inkuwa hakn yafaru wlh zatayi nadama yarinyar sbd indai akankane to wlh har kasheta Zan iya yi sbd....stop it Abdallah yakatseta atsawace, had'e da ficewa dg parlourn fuska daure. Tsaki yaja azuciyarsa yace shiyasa banson xaman Nigeria gashi tun ban kwana ba Raina na baci,wlh taci darajar mom shiyasa nike binta ahankali sbd gudun b'acin ran mahaifiyata da wlh sai tagane kuranta ,sbd rashin hankali Wai zata iya kisa mittss yasake Jan doguwar tsuka....Hafiz dake kallon sa yace lfy dai ko AK(haka abokansa ke kiransa) naga kana tsaki ko kaida madam ne?" wata uwar harara ya maka Masa suka fice zuwa masjid, yyinda Hafiz yyi shiru sbd yasan halin abokinsa.;;;; Da dare byn yagama isha'i sannan yanufi part din abbansa. Byn sun gama gaisawa atare sukayi diner da Abba sannan suka Fara fira . Can Abdallah yace Abba Wai Dan ALLAH miyasa baka zuwa bauci Kuma bakason naje??" bacin kasan danginkane acan pls ka amsamun . Shiru Abba yyi hade da Jan numfashi , sannan yashe kayi hkri nima bansan daliliba ,amma very soon zamuje tare amma kada kasake kayiwa mominka wannan zancan kaji?" Cikin mamaki abdallah yace miyasa Abba?" Kallon sa Abba yyi yace kayi hakuri banason tambayar kaji ?"shiru Abdallah yyi Yana tunanin Wai Mike faruwa ne tsakanin Abba da danginsa daya mantadasu baya taimakonsu da d'inbin dukiyarsa". Kallon Abba yyi cikin marairai cewa yace pls my Abba Zan maka wata tambaya " Kallon sa Abba yyi hade da tsaresa da ido yace inajinka" Fuska bbu walwala yace Abba miyasa kake bin umarnin momy saikace Kaine mijin itace matar?"gsky Abba abun namun ciwo inda Momi ba mahaifiyata bace dole karabu da ita,sbd bazanso ganin ana juyaka ba Abba why?"yafad'a cikin 'bacin rai ,idanunsa sunyi jajir, yyinda Abba yakasa mgn dabashi amsar tambayar sa. Cikin huci yace shiyasa banson aure sbd abinda mom ke maka Abba gsky ,dan bazan iya k'yale mace ta juyaniba,Kuma Ni xanmata mgn Abba sai....da sauri Abba yace kul! Kada kasoma kaji abdallan Abba kamana addua komai zai daidaita zata denakaji insha ALLAH yafad'a cikin damuwa. Kallon Abba yyi hade da cewa shikenan Abba baza n mata mgn ba.... murmushi Abba yyi yace ko kaifa my son . Mamaki abdallah keyi azuciyarsa ganin Abba yasaki ransa jin Wai bazaiyiwa mom mgn ba lallai akwai abinda ke faruwa wanda besaniba .... Besake ma Abba wata tambayar ba baci wannan haka sukayita firarsu har mom takira Abba a waya tukum sukayi sallama. Part d'in sa yawuce, direct toilet yashige ,yafi 30 minit sannan yafito yyi Shirin kwanciya yafeshe jikinsa da turarukan sa masu masifar kamshi. Tamkar zeenat najira ta yi kiransa,tsaki yaja ganin itace,saima yarufe wayar baki daya ,dama be dadeda saka sim card d'in sa ba na Nigeria.,,,,, Bangaren su riyanatu kuwa"da dare byn sunyi komai harda Shirin kwanciya zuwaira ta shigo" Bayan ta sallami customers,da sallama ,ta zauna suka sake gaisawa sannan ta musu murnar kubutarsu dg garinsu.. Sannan tace to da farko dai mariya Yar uwatace, sannan nima mijina y mutu inada y'a zatayisaar wannan,ta nuna riyanatu dake zaune kan ta duke. Tana makaranta kwana ajinta5 befi saura kwana 8tadawo hutuba nan dakintane kuke. To yanxun wace Sanaa Zaki iya?" Umma taja ajiyar tace ko aikatau nasamu lfy lau. Zuwaira tace to shikenan ma sai kimun sbd memun wanke wanke tayi aure sati2 dasuka wuce,awata Ina Bata dubu ukku ,Kuma nikecida ta,Zaki iya?" "Umma tace eh insha ALLAH" Zuwaira tace to ita riyanatu tayi makaranta?" Umma tace eh wlh dg aji 3 tabari,anata mun surutu Wai nabarta tana karatu bbu aure saita lalace ta girma ta gand'ame. Murmushi zuwaira tayi tace hmmm in bacin abin mutumin kauye duka riyanatu nawa take,ai batawuce 17 ko 18 ko?" Umma tace eh" Zuwaira tace to shikenan insha ALLAH in sun koma huta sai a maida ita da islamiya ko? Umma tace eh ,acan ta allo takezuwa tayi ihu34 . Zuwaira tace Masha ALLAH. Nan sukayi sallama ta basu guri su sake. Washe gari... Share pls BY MMN FAREESA 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & written By mmn fareesa Wannan shafin nakune halak malak Bilkisu Auwal Fatimatou Queen Kuyi yadda kukeso dashi comments naku yafi nakowa yimun 😄😍❤ K'oRAFI...wasu dg cikin ku suna mun korafin Wai banfadi waye Abdallah ba da Kuma wacece riyanatu ba,musammun mmn shukra novel kunfi K'oRAFI. To kusani gsky banison gajan hakuri kubi komai ahankali zakuji ,dukafa pages3 akayi Amma anfaramun K'oRAFI,duk wadda taji bazata iyaba so pls tadena bina... P4 '''"""washe gari misalin karfe 8:30 am Abdallah yafito cikin bacin rai da damuwa a fuskarsa"straight parlourn mom yanufa yasameta ita da masu aiki a dining area suna shirya breakfast . Koda ta lura da yanayinsa,tuni ta sallami masu aikin .byn sunfita yazo yazauna kusa da ita had'e da aza kansa agefen kafad'arta,cikin shagwaba yace good morning my mom! Murmushi tayi had'e da shafa kansa tace morning my son,yahbak'unta?" Turo baki yyi tamkar yaro yace gsky mom bazan iya Zama cikin dattiba,kwata kwata masu Miki aiki basu iyaba nifa nafison ko Ina nagansa need.... girgiza Kai tayi had'e da cewa pls my son kayi hakuri Zan sake Kiran harira ta sake bincikamun wacce zata ruk'a kularmun dakai,amma yanxun muje nahada maka ruwan wanka ,kafin ka fito nagyara inda kakeso kaji abdallan momy ta fad'a cikin rarrashi... Murmushi yyi yace yauwa kokefa mom ,to Amma gaskiya me tsabta zaa samu ko Kuma marar surutu . sannan gsky momy intazo kiyi warning nata akaina danbanson shishgi.... fuska bbu walwala tace Wai yaushe zaka Dena wannan miskilancin nakane?"damafa jiya da zeenat tazo gunka haka tadawomun da kuka Wai ka shareta kunyi tafiyarku kaida wannan yaron mittsss taja tsaki hade da cewa ni wlh narasa wacce jaraba ce wannan kudai ba gari daya kukeba aiki yakawosa anan iyayensa na kano,dg kunyi skul tare yazo yawani manne maka ,kilama shike turaka ka wulakanta zeenat... Kallon mom yyi"ahankali yace kiyi hkri mom Hafiz bashida wani aibu ko wani mugun hali sai kyawawan halaye, sannan zeenat banmata komaiba, lokacin sallah yyi dalilin dayasa muka fice kenan,dg karshe mom zeenat batada tarbiyya da kamun Kai na ya'yan kwarai... Ya isa haka kayi hakuri zata canza kasan dai uwarta kawatace ko?"to banison jin komai muje kayi wankan. Bbu musu yabita har part nasa. Mom batabar part d'in ba. saida komai yyi yadda Abdallah keso tukum ta fito da niyar aiko Masa breakfast dinsa.,,,,, Bangarensu riyanatu kuwa ,cikin yadda ALLAH suka tashi da safe suka kimtsa hade da Karin kumallo , sannan umma ta Fara aikinta yyinda riyanatu ketayata. Azaman dasukayi da zuwaira dg jiya zuwa yau sun gane mace ce ita mai kirki dason jamaa,sbd duk wani Abu dazasuyi kauyanci akai ,zatayi saurin gyara musu shi cikin aminci bbu tsangwama. ************ Abbane ketsaye gaban dressing mirro Yana fesa turaruka,yanata sauri da alama fitama zaiyi... Abdallah yyi sallama yashigo Yana murmushi had'e da kallon Abban nasa Yana gaisheshi,hade da cewa Abba office zakajene kk sauri?" Juyowa yyi Yana dariya yace ah ah my son!wlh tafiyace ta kamamu harta tsawon 2 weeks Kuma tare da president zamuyita zuwa indiya dg nan mudawo Abuja muyi wani meeting tukum nadawo ,nima da safen nan byn nadawo dg masjid sakon tafiyar ya isomun jirgin karfe,9:am zamu hau... Fuska bbu walwala yace Abba gsky nidai banison katafi dudu yaub kwana na nawa a Nigeria?"murmushi Abba yyi hade da cewa sorry kaji my son nima naso mu zauna sbd inason to bude sabon kamfaninka kafara aiki ,karika fita office Amma insha ALLAH innadawo munyi mgnar.. Yafad'a had'e da daukar wata jaka, yyinda Abdallah yakarba da nufin Masa rakkiya. A parking lot ne yakedubarsa ganin bbu momi amasu rakkiyar ,yace Wai Ina mom bazata maka rakkiyaba??" Murmushi Abba yyi hade da cewa ah ah munyi bankwana ai da ita"Abdallah bece komaiba yyishiru har guards d'in Abba suka bude Masa gdn baya yashiga ,nan yarika dagawa Abba hannu had'e da Masa adduar sauka lfy.. ##### Haka rayuwarsu umma da riyanatu ta kas canance agdn zuwaira mai abinci bbu kyara balle tsangwama har tsawon kwanaki 8 Ayaune Kuma suke jiranxuwan Fatima y'ar zuwaira dg skul kasancewar yau ake hutu .... Zazzaune suke atsakar gd bacin sun gama aikin safe ,zuwaira nata yanka salad na abinci .wata dattijuwar mace tayi sallama , zuwaira ta amsa fuska sake tana cewa ah ah lallai harira b'atan Kai kikayi agidan nan?" Murmushi harira ta yi tace hmmm ah ah wlh naxo mu gaisa ne andad'e baahad'uba ... Nan suka gaisa da zuwaira, sannan umma tace Ina kwana?" Harira ta amsa , had'e da cewa Masha ALLAH zuwaira Baki kikayine agdn?" Zuwaira tace eh Yar uwatace wannan yartace,banan suke ba ,Amma sundawo da zama agarin nan.,, Harira ta ce Masha ALLAH" Byn taci abinci sukayi sallama ta fice.. Harira batafi minti12 da fitaba saiga Fatima da masu daukar Mata kaya sunyi sallama. Da gudu tajeta rungume mamanta ,tana ihun murna, dariya zuwaira tayi tace to auta sakeni karki kadani ga Baki nan munyi Kuma goggonki ki gaishe d ita... Juyowa tayi lahh Ina kwana ?" Waccan kyakykyawarfa mama?"ta fad'a tana nuna riyanatu dake kallon ta. Murmushi zuwaira tayi tace y'ar uwarkice Kuma kawarki....ihun murna tayi had'e da zurawa aguje t rungume riyanatu sbd Fatima akwai son jamaa. Ita riyanatu cikin murna ta tarbeta,kafin kace me,harsun shaku da juna,komai tare suke har aka kwana aka wuni ,tuni Fatima ta Fara kokarin wayar da riyanatu da koya Mata kwalliya duk da bbu abin kwalliyar Dan kayanta basufi kala7 ba ,suma kuma duk sunji jiki,hakan yasa Fatima tabata nata kala4 Kuma sabbi , sannan da kayan kwalliyar ta suke amfani... Hmmmm acikin kwanakin duk Wanda yasan riyanatu a kauye to yaganta yanxun bazai ganetaba,sbd yadda ta canxa. Dama gata da muguwar tsabta ,saidai matsalarta guda batason saka gyale saidai hijab. Lokacin da Fatima ta koma islamiyya duk tadamu sbd ita agd ake barinta Kuma zaman gundurarta yake,Koda umma ta lura rarrashinta tayi had'e da cewa in wata yyi zata sakata Amma bacin wannan aikatau dole su nemi wani abun suyi.sbd sai wata yyi abasu kuma kafin zaka zasu iya bukatar wani Abu gakuma skul da akeson mayarda riyanatu,danma zuwaira na kokari akansu to Amma yau d gobe sai Allah. ************** Mom ce zaune kan kujera ta aza k'afa daya kan daya ,ga lemun kwali gabanta kan center table tana kurba ,tana yatsina, yyinda tayi wani murmushi had'e da kallon matar dake zaune gefen kafafunta kan carpet tace to harira kinji dai dalilin. Kiranki Dan ALLAH kisamo mai tsabta, wacce zata kularmun da yaro Amma ba mai surutuba Kuma banison babba ,nabaki nan da kwana 2 Dan ALLAH kikamun ita muyi mgn nasanar da ita aikinta ,Amma banison mai yawan mgn da surutu gsky sbd my son bayason yawan mgn , sannan Kuma kikawo marar wayo sbd kinsan banison sa ido gsky...inhar kikayi yadda nikeso kinada kaso mai tsoka kema. Ajiyar zuciya harira ta yi hade da cewa to ranki yadad'e insha ALLAH zaasamu Dede yadda kikeso.zan bincika dg yau zuwa gobe insha ALLAH. Kafin mom tayi mgn Abdallah yashigo parlourn da sallama, sanye yake da suit farare ,yyi masifar kyau ,yyinda sallayar dake tsakkiyar goshinsa takara fitowa da Masa kyau ga sajensa yasha gyara sai kamshi take tashi ajikinsa tunkan ya ida isowa kamshinsa ya bayyana. kamar kulum fuska atamke yazauna Yana gaida mom had'e da cewa harira Ina yini?" Baki washe ta amsa tana Masa kirari,yatsina fuska yyi yamike tsaye da nufin barin parlourn, adedenan zeenat tayi sallama sukayi 4 eyes da Abdallah tabe baki yyi hade da kauda Kai yyi haryar dazata sadasa da part nasa.... Mom ta yi saurin dakatardashi gurincewa haba my son !bak'uwa fa kayi zaka tafi kuma" Cikin agree voice yace banason mgn da kowa sbd kaina na ciwo pls mom nafison kebantuwa,bejira asartaba yafice. Yyinda mom ta sallami harira ta fice. Byn fitar harira mom Ta dubi zeenat dake kukace tace oh ni hafsatu mezan gani haka,sbd d'a namiji kke kuka da hawaye??" gsky zeenat kin rako Mata aduniya,shiyasa yakemiki wulakancin daya gadama ,tunda yalura da yadda kikesonsa . To bari kiji shi namiji baa Masa haka ,saikace ke ba rainon hjy kilima bace?" To bari kiji dg yau kirike ajinki ,kina Abu kamar Baki lek'a ajiba ,ainariga nagayamasa kece zabinsa ,Dan haka ko zai mutu sai ya aureki kibaridai ki kammala karatunki tukum ... Ajiyar zuciya zeenat tayi tace ALLAH mom ?" Mom tace kwarai kuwa,Kinga byn kin auresa sai musan y....salamu alaikum cewar Hafiz dake ta sallama su mom basujiba... Da sauri mom ta d'ago taga Hafiz ne,kicin kicin tayi da rai had'e da amsawa fuska bbu yabo bbu fallasa. Bedamuba da hakan ba sbd yasaba ,Kuma duk yaji maganarsu,cikin tuhuma mom tace oh wai tun dazu ne kaketa sallama ko yanxun?" Murmushi yyi yace ah ah shigowa ta kenan Ina wuni mom?" Yacanza topic d'in,amsawa tayi bata kallesaba. Yadubi xeenat Yana murmushi yace madam ya kk ?AK nanan?" Mom ta karbe zancen da cewa Cikin bada order eh amma nahana kowa ganinsa yanxun... Murmushi Hafiz yyi yace to shikenan mom na wuce" Kagaida gd,ya girgiza Kai yafice ,mom tarakasa d harara. Sannan suka cigaba da fira da zeenat. Bangaren harira kuwa tunani ta hauyi byn ta bar gdn hjy hafsatu wato mom akan wata samoma mom. Kwatsam riyanatu ta fado Mata arai ,afili tace to ALLAH yasa uwarta ta amince Dan nakura yarinyar akwai hankali d nutsuwa. Ay tuni harira ta nufi gdn zuwaira mai abinci. Sallama tayi atsakar gd tasamu su riyanatu da Fatima suna ta fira yyinda umma d zuwaira keta aikin yin miyar abincin siyarwa. Gaisawa sukayi sannan harira ta bukaci ,su riyanatu subasu guri suyi mgn ,bbu musu su bar gun. Sannan harira ta Fara dubar zuwaira tace dama wata damace tasamu ,shine nace baranaxo gurunku. Zuwaira tace to munjinki" Harira tace kinsan Alh KABIR GIRMA ?" Zuwaira tace kwarai kuwa"harira ta koramusu bayani game d bukatar mom , sannan tace to aganina in har yarinyar nan zata iya me zai Hana muje da ita ,agayamata abinda zatayi abiyata salin alin Kuma abinda yasa nace haka gsky yaron kirkine bbu wata matsala Dan ko mgn Bata damesaba balle yakalli mace. Shin yakuka gani Dan wlh zata samu albashi mai tsoka sosai . Zuwaira tadubi umma tace to yakikagani ne yanzun. Umma tayi ajiyar zuciya tace..... Share pls BY MMN FAREESA 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & written by mmn fareesa Wannan shafin nakine mmn sultan aminiyar k'warai.😍marubuciyar SON ZUCIYA kiyi yadda kikeso dashi Ina mugun jidke😇😇 Jin jina ga ZUMUNTA novels MMN SHUKRA novels AUREN WATA SHIDDA novels Maimuna.. Bilkisu Auwal Queen Teema Aysha k y Mmn arfart Hanifa isah k Zee hamis wada Inajin dadin comments naku sbd ku nayi typing kuna dabanne azuciyar mmn fareesa👍🏻❤ Mmn fareesa fans page&auran wata shidda fans ku gyara bakwasan comment zandena posting daku.😜 P5 .....Umma tayi ajiyar zuciya ta kalli zuwaira tace kiramun mariya awaya muji me zatace inta amince to nima na amince. Zuwaira tace to shikenan,nan takira number gali tasanardashi tanason mgn da Inna mariya,yace to bara yakai Mata wayar baya gd. befi minti3 ba da yanke wayar yakira, umma ta daga had'e da yin sallama" Cikin murna suka gaisa da Inna mariya da tambayar su bbu matsala daiko ?" Umma tace eh, sannan tasanar da ita mgnar aikin da riyanatu zataje. Inna mariya tace to ai bbu matsala bintu tunda bama aikatau bane Dan aiki neba waniba,amma gsky kiyi Mata fad'a ta rik'e mutuncinta da Kuma gsky dukda nasan halin riyanatu yarinyace. Nutsatstsa amma ki tunarda ita. ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi" Umma tace ameen" Inna mariya tace dama kuwa gobe nikeso Zan turo gali yakamiki kudin tumakinki dubu15 kunyi amfani dasu sannan ki siyawa riyanatu Yan kaya tunda ance gdn masu haline. Umma tace to ALLAH yakawosa lfy.inna mariya tace ameen ,Wai kinsan byn tafiyarku kuwa yadda Iro da baffan riyanatu sule sukatashi hankalinsu,saida naje har gd namusu bayani tukum hankalinsu ya kwanta ,Kuma iro yace insha ALLAH zaizo yarika dubaku tunda ya rasa Yaya HAJARA kema bazaiyi sakaci yarasaki ba...hawaye yazubowa umma sbd jin an anbaci HAJARA y'ar uwarta wadda batasan araye take ko a mace ba....cikin Jan majina tace to ngd sosai agaishe dasu,Koda inna mariya taji muryar umma tasan kuka tayi sbd jin sunan HAJARA.nan sukayi sallama,,, Zuwaira tayi ajiyar zuciya sbd ganin umma na goge hawaye tace kiyi hkri dukda bansan miyasa kikekukaba,Amma yakukayi d ita?" Umma tace bbu matsala duk mun amince, sannan ta dubi harira dake kallon su tana washe baki jin sun amince tace to yaushe zata Fara be?" Harira tace eh yanxun gobe Zan zo muje gdn zaa sanar da ita aikinta da lokacin zuwa da albashinta, sannan afadi ranar dazata Fara. Umma tace to ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi" "Zuwaira tace ameen" Sannan sukayi sallama da harira. Umma ta k'walawa riyanatu Kira....da sauri ta fito dg parlourn mama zuwaira, kallon ta tayi had'e da Kiran sunanta ,hakan yasa riyanatu gane cewa maganar da umma zatamata mai mahimmanci ce,sai ta amsa anutse" Sannan umma ta Mata bayani komai game da aikin da zata Fara... Atsorace cikin jin faduwar gaba tace aiki Kuma umma?"sannan nmj Wanda bansan halinsaba nidai gsky...sai Kuma tayi shiru... murmushi umma tayi sbd yasan abinda riyanatu kesan fad'a be wuce tace tanajin tsoro ba sbd abinda yarima HAMZA yaso yima" Ahankali umma btace duk abinda zakiyi arayuwa kiyi da zuciya d'aya, sannan kada kisaka zargi aranki ko zato sbd mafi akasarin zato karyane riyanatu Kuma baduka aka Zama dayaba ,duk lalacewar duniya da mutane baza a rasa mutanan kirkiba sbd ni inaji ajikina wannan aikin da zakiyi alkhairi ne ko yanxun ko nan gaba , sannan Kuma bawai Ina nufin ki dauwamaba da yinsa aha ah!,insha ALLAH abinda kikasamu inkin yi Yan watanni dashi zamu nemi wata sanaar kibar aikin insha ALLAH.. Ajiyar zuciya riyanatu tayi sbd ta gamsu da zancen umman ta, sannan Kuma mama zuwaira ta kara Mata nasiha..... ##### Washe gari harira ta Kira hjy hafsat tasanar da ita anjima suna nan tafe da yarinyar ,mom tace to sukayi sallama, sannan takira abdallah taji wayarsa busy .sai byn kusan minti25 ta kirasa tace yazo parlourn ta yanxun,kasan cewar Yana gd. Sallama yyi hade da Zama kuda ita,yarik'e hannunta Yana murmushi had'e da cewa my sweet mom gani" Fuska bbu walwala tace my son dawa kake waya?" naji wayarka is carry busy... murmushi yyi yace wlh mom abbane gsky Abba yadawo haka nan cikin familyn sa ....yatsina fuska tayi had'e da cewa dallah rufemin baki tunda gani ai ba wani Abu bane ko?" shiru Abdallah yyi Yana mamakin halin mom....katsesa tayi da cewa yau my son kaga yau Friday ko?"to insha ALLAH me kula dakai dg Monday zata Fara aikinta yau ma zaa kata muyi mgn" Fuska bbu yabo bbu fallasa ya ce ok had'e da tashi da nufin tafiya. Mom tace sai Ina Kuma?" Yace zanje gun hafis ne,! Yauwa mom jiya miyasa kika hanashi shiga guna pls ya marairaice fuska?" Fuska daure tace to ubanah k'arata yakai gunka neka hukuntani kome?" To nahana sbd na isa ne...cikin girmama wa Abdallah yalangabe Kai yace kiyi hkri mom bansan mgn ta zata Bata Miki raiba , yafad'a had'e da dawowa ya aza kansa akan cinyarta. Shafa kansa tayi tace shikenan my son nahakura Amma kadena fadawa hafis sirrinka kaji?"Abdallah yace to, sannan suka cigaba da fira.;;;; Da misalin karfe 2:30pm mai adaidaita yasauke harira d riyanatu a kofar gidan alh kabir girma,byn sun sallamesa suka nufi k'atan get d'in gdn da riyanatu tashagala d kallo wani gefe na zuciyar najin faduwar gaba had'e da tsoro. Get man ne yazo yabude karamar kofar shiga ,Koda yaga harira bbu musu yabasu hanya sbd yasanta ta Saba zuwa gdn. Harira ta kalli riyanatu tace to yannan ki kama kanki kinjiko kada ki nuna kinada wayo kinji?" riyanatu tace to hade da mamakin miyasa harira tace haka. Tafiya sukayi mai Dan nisa, yyinda riyanatu ke yaba kyawun gdn a zuciyarta,har suka iso kofar da zata sadaka da babban parlourn gdn. Sallama sukayi kafin su shige ciki,bbu abinda ketashi a parlourn sai kamshin room frishners da turarukan wuta sai sanyin AC. Masu aikine keta Kai da kawowa ,su suka amsa sallamar su, sannan byn sun gaisa harira ta bukaci suyi Mata mgn da hjy ... Sunkai kusan minti20 zaune har zaman ya ishi riyanatu ta Kuma tabbatar matar gdn batasan darajar bak'o ba.. maganar mom ce da kamshin turarenta yadawo da ita tunanin ta d'ago kanta da sauri sukuyi 4eyes da mom ,suduka atare gabansu yafadi, yyinda riyanatu ta sunkuyar dakanta k'asa. Cikin yatsina had'e da izza mom tace wannan itace yarinyar?" Ta fad'a cikin gadara fuska bbu walwala, yyinda wani b'angaren zuciyarta ta tsorata da kyawun yarinyar. Harira tace eh" Riyanatu ta yi saurin dukawa tace hjy Ina wuni?" Lfy ,ta amsa atakaice"had'e da cewa to da farko dai inason ki bud'e kunnanki kijini da kyau game da aikin da zakiyi . Cikin girmama riyanatu ta ce to" Mom tace da farko dai ranar monday Zaki Fara aikinki,kitabbata karfe7am tamiki agdn nan,sbd my son karfe8:am yake tashi to kafin yatshi kin gyara masa parlourn sakin wanke Masa toilet kin hada Masa ruwan wanka. Inyashiga wanka ki gyara bed room d'in sa,kafin kije kitchen gun kuku ki karbo Masa break fast nasa kiyi serving nasa, sannan ki gyara Gurin da Kuma sake gyara bed room nasa sbd bayason k'azanta shi mai tsabtane sosai Dan in har bakida tsabta zaku Bata dashi gsky fuk in kika gama zuwa 9 am Zaki iya tafiya musammun inkina skul ,sai 2:pm kidawo sbd 2:30yake shigowa yyi wanka yaci abinci ,Zaki cigaba da kulawa dashi har4:00 pm sbd Yana fita Kinga inkina islamiya sai kije dg nan ki wuce gd sai wata safiyar. dg karshe my son bayason surutu had'e da shishshigi,nima haka, sannan ban hada Dana da kowaba muddin ki ka b'ata Masa rai can hukuntaki nakuma koreki , sannan kada ki yi zaton d'ana mutumin banzane kice Zaki ja raayinsa da kyawunki to ba haka ABDALLAH yakeba.nasake gayamiki ki kularmun da yaro kada ki bata Masa rai.... Jikin riyanatu yyi sanyi,jiki bbu lakka tace to insha ALLAH Zan kiyaye. Harira tace ai hjy batada matsala yarinyar nan....ban tambayekiba ,mom ta katse harira hade da zuge jaka ta fito da kudi ta mik'awa harira , sannan tace albashin ta a wata dubu 30 be,sai Monday din. Harira ta karba , sannan tayi godiya , sannan tace ai hjy anyi hutun boko itakuma sai islamiyya take,mom tace bbu damuwa akwai islamiya farkon layin nan zanma ya'u direba mgn asiya Mata foam intazo saita ruk'a zuwa. Godiya su riyanatu da harira sukayi kafin suyi sallama su fice,mom tabi bayansu da harara. Koda suka fita , adaidaita suka hau ,har gd harira ta raka riyanatu ta ma su umma bayanin komai da irin aikin da riyanatu zatayi da albashinta da sakata islamiya duk sunji Dadi sosai , sannan harira ta dubi zuwaira tace ammainaganin kafin Monday din yaka Mata akoya Mata kamar... Wanke bayi da yadda ake hada ruwan wanka da turare d'aki dasu moping da sauransu dukda nasan xata iya amma gara ak'ara nuna gudun kuskure .. Zuwaira tace to shikenan Zan saka Fatima suje gdnsu yusra kawarta tunda suma masu haline sai ta kara ganin yadda ake amfani da komai . Harira tace to sannan suka yi sallama. A cikin kwanaki biyu riyanatu ta koyi duk abinda akeson ta koya, yyinda riyanatu ke ta faman Yaya zata kasance da ita gobe Monday agdn aikinta. Monday.... Innaga ruwan comments kujini da safe.... Happy juma at kareem❤ Share pls BY MMN FAREESA 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & written by mmn fareesa Dedicate to all my fans ana mugun tare😍😄 p6 Monday """"Tun gurin karfe 6:30 riyanatu ta shirya cikin doguwar riga bak'a y'ar kanti tasaka hijab Fara "bbu wata kwalliyar datayi dg powder sai kwalli ta shafa ,sukayi sallama da umma dasu Fatima dake Mata fatan alkhairi itada mama zuwaira" Adedeta tahau ,ya ajeta a unguwar nassarawa G R A.byn ta sallamesa tashiga ciki kasancewar get man yasan da zuwanta. Waiting parlourn gidan ta nufa gabanta na mugun faduwa,tasami mom da Yan aiki"har k'asa ta tsugunna ta gaishe d mom ,ta amfa fuska a tamke yyinda tasaka ladidi(d'aya dg cikin masu aiki) ta nunawa riyanatu part d'in Abdallah..,,, Suna zuwa kofar shiga part d'in ladidi ta juya ta tafi" Wani mugun tsorone fal aranta ,amma saitayi jarumta had'e da yin addua azuciyarta,kafin ta murd'a kofar tayi sallama"bbu kowa a parlourn" Tasbihi riyanatu tayi da ganin wannan kayataccen parlourn a zuciyarta ,ko Ina k'al amma Wai nan sai an gyara sai kamshi ketashi na room frishners aciki.. Kofar dake cikin parlourn ta kalla hakan yanuna Mata nan be bed room d'in. Tsintsiyar data shigo da ita had'e da mofa da wani towel ,tasaka ta Fara gyaran parlourn had'e da karkad'e kujerin d kayan kallo , sannan tayi moping. Ta duba taga komai yyi daidai. Sannan ta nufi kofar bed room gabanta na dukan Tara Tara,tayi Knocking yafi sau 3 shiru hakan yasa ta murd'a kofar tashiga ciki ahankali had'e da yin sallama,amma shiru"bed d'in tasaci kallo ta hango mutum kwance atsakkiyar yarufe jikinsa d alama bacci yake. Kofar dake da keda carpet takalla ganin harda silifas akan carpet din haka yatabbatar Mata da nan ne toilet.. Addua tayi ta shige ciki " sai zare ido take sbd atsorace take,Saida ta k'arewa toilet din kallo tukum sannan ta Fara aikinta , azuciyarta tana mamakin Wai bayine wannan aka zubawa kayan alatu haka tamkar baza a mutuba , lallai mutumin nan d'angatane sannan akwai muguwar tsabta gsky.... da wannan tunanin ta gyare toilet din k'al har tayis d'in jikin bango Saida ta wanke , sannan ta wanke hannunta ta fito.....tana fitowa taga mutum tsaye gaban mirro dg shi sai towel iya guiwa da alama wanka zai shiga ,yabada baya hakan yasa bataga fuskarsaba.. Ta tsorata ainun takuma razana sbd batatab'a ganin nmj hakaba "da sauri ta d'auke kanta had'e da cewa ranka yadad'e Ina kwana?" har sau2 jin yyi Mata banza sai ta nufi Gurin bed Dan ta gyara. Shikuwa Abdallah uffan beceba Kuma be kalleta ba yawuce toilet ya rufe,k'arar rufe kofar ya ankarar da ita baya cikin room d'in" Ajiyar zuciya tayi azuciyarta tace oh ikon ALLAH lallai mutumin nan baisan darajan d'an adam ba ... Cikin minti 25 tayiwa bed room d'in fas,ta duba kan mirro ta dauki air freshener ta feshe ko Ina harda parlourn tuni guri yakaure da k'amshi.. Bed room d'in ta koma ta ajiye air freshener din sannan ta duba wardrobe din haggu cikin saa taga bed sheet da sauri ta dauka ta canza ,sbd Fatima ta Bata shawarar ta rik'a canzawa tunda ance shi mai tsabtane. Wayoyinsa data aza kan mirror taje da nufin ta dauka ta mayar Masa kan bed inda tagani... adedenan taji motsin zai fito da sauri ta janye hannunta ta nufi kofar fita dg bed room d'in... Waye zai fitomiki da kayan da Zan saka?" Yafad'a cikin husky voice,tamkarbashi yyi maganarba" Cak yatsaya hade d juyowa sukayi 4eyes dashi"Masha ALLAH tace azuciyarta sbd ganin baiwar halitta agun sa,tayi mamakin jin yyi hausa ,dabaiyi mgn ba saitace balarabene bayajin hausa....tsakin dayajane yasata janye idanunta dg barin kallosa. "Ahankali tace Ina kayan suke?" Tasake tambayarsa, yyinda shikuma yaketa duba body cream nasa ,yamata banxa...d hannu yanuna wardrobe d'in tsakkiya" azuciyarta tace oh ni nashiga3 ,Toni nasan irin kayan dazai sakane?" Jiki bbu kwari ta nufi wardrobe d'in ta bud'e, lumshe ido tayi sbd jin kamshin da kayan keyi....Saida ta ce Masha ALLAH sbd ganin tulin kayan sawarsa duk yawancinsu k'ananu ne" addua take ALLAH yasa kada tayi ba dai daiba "can idanunta suka hasko Mata wasu suit dark blue da sauri ta fito da su,kasancewar tare suke da wandon da komai ta aza kan bed ta fice da sauri sbd tunawarta da karb'o Masa breakfast.. A babban parlourn gdn ta koma ta Sami mom na break fast a dining area ,ta isa gunta cikin ladabi tace hjy na gama Ina ne kicindin?" Tsaki mom taja hade da nuna mata wata kofa da hannu sannan tace kije can ki karba inya gama kije can ki karbi naki sbd ba Wai nasa zakiciba ,abincin masu aiki dabn yake dg yanxun ban abukatar kisake tambayata in 4 tayi kije bakin get gun ya'u direba zai kaiki islamiya ga yunifaom nan ta nuna mata wata leda dake k'asa kusa da kafarta. Jiki asanyaye ta dauka had'e da yin godiya ta wuce kicin ta karb'o break fast nasata koma part d'in sa. Da sallama ta shiga ,zaune ta samesa a parlourn yasaka kayan agogo na hannunsa ,gefensa takalmi sawuciki kafarsa d safa. Gun dinning ta nufa "ahankali yace kawo nan yafad'a Yana latsa waya"ajiyewa tayi ,ta mik'e da nufin tafiya....waya Baki izinin tafiya?" Juyowa tayi ta kallesa,fuska daure yace last warning dazan Miki game da kallona"yafad'a had'e da mik'a Mata agogon sa " Da mamaki t karb'a tana dubawa ,sai Kuma taga ya Miko Mata hannunsa na dama danufin ta d'aura masa"cikin tsoro da mamaki tace Dan ALLAH banganeba ?" Kuma kayi hakuri innayi badaida b kada kafad'awa hjy sbd tace Inna maka laifi korata zatayi..... stop it yakatseta atsawace had'e da cewa surutu kikazo kimun ko aiki?" Da sauri tace aiki" Tsaki yaja had'e da saka takalminsa,yasake mik'a Mata hannu alamar tabasa agogon sa"cikin muryar kuka tace Kayi hakuri me zanyi d agogon?" Tamkar mai koyan mgn yace ki dauramun.... Zaro ido tayi tace.... Muhadu da marece pls kuyi manage da wannan🙏🏻 Share pls BY MMN FAREESA 🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾🐾🐾🐾 🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & written by mmn fareesa Wannan page din nakune halak malak AUREN WATA SHIDDA FANS &mmn fareesa fans page Ina mugun jidaku bbu laifi kunyi comments😍😇 p7 .....Zaro ido tayi tace ai ban iyaba!kayi hakuri Dan ALLAH"banza yyi da ita yasake mik'a hannu da nufin karba"zabura tayi had'e da sakin agogon k'asa tana hawaye had'e da cewa kayi hakur....are you mental?" Yafad'a atsawace had'e da mik'ewa tsaye yadauki agogon sa had'e da dubawa kota kashe Masa glass d'in" Saka abinsa yyi ganin baiyi komaiba"Saida yagama Shan k'amshinsa , sannan yace serve me break fast yafad'a batare da yakalleta ba" Ita kuwa hawaye kawai take jin yace ita Wai mahaukaciyace , sannan Kuma dayace tayi serving nasa batafahimci me yace sbd(kunsan skul din kauye bbu wani karatu) Cikin muryar tace ranka yadad'e nifa ban f.....I say don't call me ranka yadad'e,call me ABDALLAH! Ni bana fahimtar turancin kayi mgn da hausa manah.... tsaki yaja ganin wannan yarinyace k'arama,yadago Kai yaga tana kuka wata uwar harara ya aiko mata da ita. cikin bada order yace kixo ki hadamun tea da sauran kayan , sannan kika sake mun kuka anan Zan nuna Miki calour d'ina yafad'a Yana yatsina fuska" Tashi tayi , zuciyarta bbu Dadi ganin wannan mai girman kan na juyata kamar bewarsa duk sai taji aikin yafita aranta ,zata jurene kawai sbd umma.,,,, Haka ta daure ta hada Masa tea din tana d'ar d'ar , sannan Bata cika suga ba sbd gudun laifi,amma tayiwa cup din dam da tea, sannan tasa Masa chieps ta hade da farfesun kaji🤣 d'auka tayi ta aje gabansa , had'e da cewa ranka yadad'e gashi... adedenan Hafiz yyi sallama yashigo cikin parlourn, riyanatu ta amsa had'e da cewa Ina kwana?" ganin yanata kallonta"sannan ta mik'e da nufin fita.hafix Yadubi Abdallah yace AK duk Kai daya zakaci wannan garar? da sauri Yadubi plate d cup din.... Keeeeee! I don't go"Abdallah yafad'a rai bace ganin kwabar da tamasa na hade chieps d farfesun kaji gu d'aya...cak ta tsaya had'e da juyowa taga yyo kanta ! saurin toshe bakinta tayi sbd kukan daya taso Mata azuciyarta tace naga ta kaina" Sai zare ido take....d sauri Hafiz ya danne dariyarsa yarik'e hannun Abdallah had'e da cewa calm down abokina!kaga ka tsorata ta ,pls kayi hakuri... Tsaki abdallah yaja had'e da nuna riyanatu yace you are very stupid! sannan ya fisge hannu sa dg na hafis Yadubi riyanatu dake kuka yace dama ciwon Kai kikazo kisamun b aiki kikazo yiba get out of my parlour"yafad'a atsawace.... Hafiz ta kallah fuska kalar tausayi tace Dan ALLAH kabasa hakuri ,hjy tace dana Masa laifi korata zatay....bazaki fitaba?" Cewar Abdallah batare da yakalleta ba. Hafit yace jeki bbu komai kinji,bazaa kore kiba! Jiki asanyaye ta fice" Abdallah ya ya tsina fuska had'e da cewa Kai mlm dakace baza a koreta ba, Kai zata bi ko saita ruk'a maka ko? Hafiz yyi murmushi yace Wai mutumin wannan fine baby dinfa dg Ina?" Kai gsky ta had'u akwai kyau tamkar aljana ai wlh I.....dallah mlm ya isa haka sai zuba kake bbu commer balle full stop,cewar Abdallah . Yana tsaki. Murmushi Hafiz yyi yace eh naji ka amsamun tambayata. Saida yagama Shan k'amshinsa sannan yace mai kula danice !amma dg yau kuma zatabar aikinta ,sbd bata iyaba . kaduba kaga wannan haukan datamun... relax Mana AK ,kaga yarinya ce sai ahankali zakaga yadda kakeso, sannan na lura tana tsoronka Dan ALLAH kabita ahankali saikasa mom ta nuna mata inda tayi kuskure saita gyara amma pls kada ka koreta sbd naga batason akoreta. Kuma tunda ta Fara aikinta duka duk ba daidai tayiba ko kuwa yanxun tayine b daidaiba?" Yatsina fuska yyi hade da cewa babu laifi tayimun gyaran daki yyi" Hafiz yace to pls maganar korarta ka ajiyeta gefe,sanny kada ka gayawa mom sbd na lura tana tsoronta itama. Ok kawai Abdallah yace atakaice, sannan ya hada tea ,yyi serving kansa . Shima Hafiz haka" Sai Gurin 9:14 am suka fito da nufin Abdallah yaje yagaishe da mom. Suna fitowa suka ganta zaune tayi tagumi idanuwa sunyi jajir alamar taci kuka" Cikin tausayawa Hafiz yace kaga kasaka bewar ALLAH damuwa k... kallon da Abdallah yyi Masa ne yasaka shi yin shiru Yana murmushi . Da hannu Hafiz yyi Mata alamar ta biyosu,da sauri kuwa ta taho ,tana satar kallon Abdallah caraf suka hada ido yabanko Mata harara had'e da miko Mata wayoyin hannunsa Yana Jan tsaki. "Karba tayi tabisu a baya har suka iso part d'in mom" aikoda mom ta gansu tuni ta had'e rai aciki ciki ta amsa gaisuwar Hafiz, sannan ta watsowa riyanatu mugun kallo had'e da cewa kefa lfy Zaki wani kwaso jiki ki biyosa?"shin tamayi komai yadda yadace ko kuwa tayi wani gidadancin ?"" Girgiza Kai Abdallah yyi alamar ah ah" Kallon su tayi had'e da cewa to kuban waje nayi mgn da yarona ko" Murmushi Hafiz yyi yace to momi, sannan Yadubi riyanatu yace muje ko" bbu musu ta bisa suka fice" Hanyar part d'in Abdallah Hafiz ya nufa hakan yasa tabisa,ahanya yace kiyi hkri kinji meye sunanki?" Tace RIYANATU" Yace ok ,muje na nuna Miki inyace kiyi serving nasa abinci ,sai kiyi Masa. Murmushi tayi tace nagode sosai. Shima murmushn yyi da haka suka isa part d'in. Tea yafara hadawa yadda yasan abdallah naso ,yace ta sha , sannan yyi serving aplate da sauran abinda suka rage, sannan yace Mike baki ganeba?" Shiru tayi sannan ta ce inyayi mgn da turanci wani lokacin bani ganewa"murmushi yyi yace ko Zaki iya tunakal mar daya fad'a bakiganeba?" Cikin jin kunya ta fad'a Masa, y'ar dariya yyi yace cewa yyi kidena kiransa da ranka yadad'e ki rik'a kiransa da Abdallah" Ahankali tace to amma injin nauyin Kiran sunansa Kai tsaye..... ringing d'in wayarsa ta katse Masu mgn,da sauri ta shi da nufin Kai Masa. Hafis kuwa yace Kinga kijirasa zaizo tunda mom tace mu basu waje,nima na wuce inyazo ki fad'a masa. Bata kallesaba tace to shikenan nagode, murmushi yyi yace pls kici abincin nan kinji sbd ya koshi karshe ma badashi zaayi....da sauri ta ce ai hjy tace kada na ci ,naje can na karb'o acikin na masu aikin gdn. Shiru Hafiz yyi,Yana tunanin hali irin na mom,sbd gudun kada ta disgata yace kada takai wayar"Kai Anya matar nan akwai gsky alamarinta?" Kallon riyanatu yyi yace ki ciki kinji inkin gama ki Kai kayan gun masu wanke wanke ,baza tasan kinciba sbd in ya rage abinci masu gadi yake ba. bejira amsarta ba yafice dg parlourn. Ita kuwa riyanatu bbu bata lokaci taci ta koshi ta gyara parlourn tas , sannan ta fito da kayan da sukayi break ta nufi part din ma'aikatan gdn,ta tambayi gun masu wanke wanke aka nuna Mata takai masu. Komawa tayi part d'in Abdallah,da nufin dauko Masa wayarsa ta Kai Masa,tasamesa zaune hakimce kan 2 seeter yana latsa waya, sallama tayi ...ya amsa akan labb'ansa " Ahankali tace dama zantafi gd! banza yyi da ita dg karshe ma sai ya rufe ido "tab'e Baki tayi had'e da dage kafad'a alamar ko ajikinta "saidai batasan duk Yana kallon ta ba"hijab nata ta gyara ta nufi kofa da nufin fita....keeeeeee!cak ta tsaya cikin k'uluwa ganin raininwayonsa yyi yawa besan tana d'aga masababa"tagaji haka nan,shiru tayi ita batayi mgn ba ,Bata Kuma juyoba" yyinda shima yyi shiru.takuma yi alkawari muddin bazaiyi mgn ba to itama bazatayi ba saidai sudauwama a haka . Shikuwa gogan yacika yyi fam da rainin hankalin wannan ta tsitsiyar yarinyar nan,wani gefe Kuma Yana tunanin magan ganun mom na d'azun byn tafiyar su Hafiz,yarasa me Hafiz yakashewa mom, sannan miyasa batadamu da Abbansa yadawo gd ba koma maganar sa bataso yyi shin Wai Mike faruwa ne haka ?"" Sake duban riyanatu yyi dake tsaye tun d'azun databashi baya ,tsaki yyi azuciyarsa yace me wannan tsakuwar yarinyar nan ke nufi?" wato ita bazatayi mgn ba kenan ,aiko in har sainayi mgn zata yi to saidai ta kwana anan,kuma ta tafi to bakin aikinta..... Riyanatu kuwa... Share pls
0 Comments