Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
Sadaukarwa gareki 'yaruwa rabin jiki Fatima (Uwani) Eshak, Allah ya jikanki ya kyautata kwanciyarki
1
Zaune take akan kujerar gaban madubi tana shafa man body shop. Bayan ta gama ta dauko humra da kulacca ta shafa a jikinta sannan ta dauki doguwar rigar baccinta mai santsi kalar purple ta saka. Hair spray din argan oil(ors) ta fesa a gashinta sannan ta daureshi a cikin ribbon ta kawo hula ta saka. Turaren sandra (al rehab collection) ta fesa, sannan ta daura zani akan kayan baccin ta saka hijabi, wayarta ta dauka ta fita daga dakin tana mai jawo kofar ta rufe.
A daidai corridor da zai sadata da dakin maigidan sukayi karo da Ummi wacce ta fito daga parlour mahaifinsu. Kallon sama da kasa tayi mata sannan ta doka tsaki tare da cewa "maciyiya amana har an fito za'a tafi dakin tsoho, a haka dai zaki kare cusa kai babu kwarjini kuma abinda kika zo donshi ba samu zakiyi ba don kuwa idan har muna nan ruwa ma sai ya gagare ki sha a gidannan. Kai ke kam kwata-kwata ma bakisan halacci ba, banda haka ace ki rasa miji aure sai Daddy, mijin Mami nefa? Idan kin manta na tuna miki". Bangazarta tayi sannan ta wuce ta barta a tsaye a wurin tamkar wacce aka dasa. Tafi minti biyar a tsaye bayan wucewar Ummi ba ta tafi ba. Dakyar dai ta janye kafafun data ji sun mata nauyi ta wuce zuwa dakin daddy. A hankali ta tura kofar tare dayin Sallama, a ciki ya amsa mata. Yana zaune a kan gado yana duba wasu takardu. "Sannu da hutawa daddy" tace mishi bayan ta ninke hijab da zanin data doro akan kayan baccinta don kuwa dokarshi ce idan harta shiga dakinshi baya son ganinta kunshe cikin hijabi. "Akwai abinda kake bukata kafin na kwanta", ta tambayeshi duk da kuwa bai amsa sannun data mishi ba. Kamar bazai amsata ba kuma can sai ya cemata "black tea nake so".
Zaninta ta mayar sannan ta saka hijabin ta fita. Kitchen ta nufa ta dora ruwan tea data saka lipton guda biyu da kayan kamshi wajen dahuwar sai teaspoon daya na strawberry flavour data zuba. Bayan ya tafasa ta juye a cikin flask ta dora akan tray hade da kofi da cokali da zuma don daddy baya shan sugar sai dai yayi amfani da zuma ta dauka ta nufi daki.
A zaune a inda ta barshi anan ta sameshi, akan bedsida drawer ta ajiye tray din sannan ta wuce bandaki ta hada mishi ruwan wanka. Bayan ta fito ne ta sanar mishi sannan ta hau kan gadon ta kwanta. Bata san lokacin daya tashi ba don kuwa har ta fara bacci tajishi yana mata abubuwa, dole ta wartsake daga baccin ta kula dashi.
UMM ASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
2
Tana yin sallar asuba ta wuce kitchen don kuwa al'adar maigidan ne iyalinshi basa cin abincin masu aiki. Kasancewar tun dare tayi shirin yin waina da sinasir ne yasa tana shiga ta fara haramar suya tare da hada miyar taushen data wadatu da tantakwashi da busashen kifi. Kafin karfe takwas tayi har ta gama shirya abincin a cikin warmers ta dora a dining table sannan ta wuce dakinta tayi wanka ta shirya cikin atamfar jullius holland kalar blue da yellow wadda akayiwa dinkin skirt da riga free fitted. Kasancewar kwalliya ba damunta tayi ba powder kawai ta shafa sai lipbalm data shafa a lebenta ta daura dankwalin atamfar ta nufi dakin Daddy. A gaban madubi ta iskeshi yana makala rank a jikinshi kasancewarshi soja mai mukamin major general.
Tsugunawa tayi ta gaisheshi. A ciki ya amsa kamar dai yanda ya saba amsa duk wata magana tata. Ita dai kam har yanzu ta kasa sabawa da Daddy a matsayin mijinta, tsoronshi data kaji tun fil'azal bai taba barinta ba kuma shima he's not helping matters don kuwa yanda yake treating dinta ada haka yakeyi a yanzu bambancin kawai yanzu ita matarshi ce akwai hakkukuwanshi dake kanta kuma take saukewa da ada babu. Tayi nisa cikin tunaninta har bata san ya fita daga dakin ba sai jin karar rufe kofa tayi. Da sauri ta tashi ta bishi don ta bashi abinci.
Akan table ta iskeshi tare da sauran yaran gidan. "Ina kwananku" tace musu tare da janyo kujera ta zauna. Tana gaidasu ne don tasan cikinsu babu maiyi mata magana idan har ba ita tayi musu ba. Yanzun ma Yaya Khalifa ne kawai ya amsa gaisuwar tata. Plate ta dauka ta sakawa Daddy waina da sinasir din ta zuba miyar a cikin soup bowl sannan ta zuba mishi kunun gyada a cikin cup ta tura gabanshi sannan ta debi nata ta fara ci.
Sunyi nisa a cin abincin ne sannan ta lura Mu'azzam ko taba abincin baiyi ba. Lura Daddy yayi da baya cin abincin ne yasa ya tambayeshi dalilin rashin cin abincin nashi. Budar bakin Mu'azzam sai cewa yayi "Fisabilillahi Daddy ya za'ayi da sassafe mutum yaci wani sinasir as breakfast idan dai baso akeyi cikinshi ya cushe ba, amma na lura matarnan abinda taga dama takeyi a gidannan". Wai maimakon Daddy ya tsawatar mishi akan rashin cin abincin tunda ba'a ranar aka fara yin waina da sinasir a matsayin abin kari ba hasali ma timetable ne dasu na duk abincin da za'a a rana tun daga safe har zuwa dare kuma tun lokacin Mami haka akeyi koda tazo gidan babu abinda ta canja, a'a sai ce mata yayi "meyasa kika dafa abinda kinsan ba kowa keso ba, daga yanzu idan zakiyi girki lallai ne ki tambayi abinda sukeso kafin kibgirka don kada ayi abinda wani bayaso, yanzu ki tashi ki dafa mishi wani abin don bazai yiwu ya tafi school bai karya ba".
Ba karamin kada maganar Daddy tayi ba sai dai ba yadda ta iya bayaga tayi abinda ya sakata. Kallon Mu'azzam tayi wanda fuskarshi ke kunshe da murmushin nasara tace mishi "me kakeso na dafa maka"? A yatsine ya amsata da cewa indomie da kwai. Kitchen ta wuce ta dora mishi indomie din. Lokacin data gama ta kawo babu kowa a parlour sai shi kadai. Wato Daddy ya fita kenan ba tare da ya mata sallama ba. Ajiye mishi tayi akan table ta juya, har takai stairs zata hau sama sai jivtayi yace mata "bakiji ba", juyiwa tayi tana kallonshi tare da sauraron abinda zaice. Murmushi yayi tare da cewa "kadan ma kika gani".
Juyawa kawai tayi taci gaba da hawa stairs din. Dakin Daddy ta wuce ta hau gyarawa tun daga cikin dakin har bathroom da sittingroom din.
UMMASGHAR
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
3
A yammacin wata asabar ne tana zaune a sitting room tana kallon movie a tashar mbc2. Farida da Ummie ne suka shigo suka zauna. Remote Farida ta dauka tare da canja channel zuwa musicplus. Dagowa tayi ta kalletaganin yadda sukazo suka iske ta tana kallo suka canja mata salon tayi magana suyi mata rashin kunya. "Fadi karta kasheki" shine abinda Farida tace mata. Dauke kai tayi tamkar bata san cewa da ita takeyi ba.
A guje Ruqaiya da Zainab suka shigo suna rige-rigen hawa kanta suka ce "Aunty Aisha mun dawo" da fara'arta ta dagosu tare da cewa "to sannunku da dawowa, sai aje a cire uniform ayi haramar yin sallah magriba ko". A tare suka ce to suna masu wucewa don su canja kayan islamiyyarsu zuwa na gida. "Kai kuzo nan" Farida tace musu "ban hanaku kula wannan matar ba amma shine dayake kunnuwanku na kashi ne ku bakwa ji kullum sai kunje inda take ko, kuna kallonmu amma ko sannu baku ce mana ba kun tafi wurin kanwar uwarku, to wallahi bari kuji na gaya muku daga yauidan na kara gani ko kallonta kunyi sai nayi muku shegen duka, ku wuce ku bani wuri".
Sum-sum suka wuce zuwa dakinsu. Su kam har kullum suna mamakin yadda yayyensu ke yiwa Aunty Aisha tamkar dai ba 'yaruwarsu bace. Ita kam Aisha suna fara yiwa yaran fada ta haya sama ta bar musu parlour. Dakinta ta nufa don yin sallar magriba don kuwa har an fara kiran sallah.
Koda ta idar da sallah bata tashi a wurin ba sai taci gaba da wuridi har aka kira sallar isha ta tashi tayi sannan ta sauka kasa don tayi serving dinner. Akan table ta iskesu sun fara cin abincin kasancewar Daddy baya nan yasa suka fara cin abincin ba tare da sun jirata ba. Tana bude warmers din taga wayam babu komai a ciki, takaici ne ya kamata ganin yadda suka cinye abincin ba tare da sun rage mata ba. Juyawa kawai tayi ta koma daki don bakin ciki bazai barta ta shiga kitchen don neman abinda zata ci ba.
Khalifa ne ya kalli kannenshi dake haramar barin table din yace "ina kuke tunanin tashi kuje ba tare da kun cinye abincinku ba, wannan din wa kuka barwa shi". Turo baki Farida tayi tace "to Yaya Khalifa mun fa koshi ne". Harara ya doka mata sannan yace "come on dawo ku zauna ku cinye, kunsan bazaku ciba kuka kwashe abincin gaba daya ita mai daguwar baku rage mata ba. Idan ma kunyi ne don kuyi mata mugunta to kanku kuka yiwa don kuwa sai kun cinye abincinnan tas ina kallonku".
Haka suka zauna suka tuttura abincin da kyar yana kallonsu har sai da suka cinye tukunna ya tashi ya bar wurin. Tuntsirewa Mu'azzam yayi da dariya har yana rike ciki ganin yadda suke ymutsa fuska kamar masu shirin yin amai. Tsaki Ummie tayi tace "to miye abin dariyar kuma". Wata dariyar ya karayi sannan yace "ai kune kuka sakani dariyar, ai idan kuna son yiwa matarnan tsiya bari zakuyisai Daddy na nan yanda duk abinda zakuyi ba maice muku uffan, amma Yaya Khalifa kam ai kinsan he always has a soft spot for her. Aurenta da Daddy ne ma yasa yaja baya da ita". "Wannan kuma shi ya jiyo, amma mudai ba'a isa a hanamu takurawa yarinya ba tunda dai ta yarda ta auri ubanmu" cewar Farida. Mu'azzam yace "lallai ma Farida bakida kunya, Aishan kike cewa yarinya agemate dina cefa don nasha jin Mami na cewa watanni 2 na bata".
Taking tayi tare da cewa "to shine me don sa'arka ce ko sa'ar Yaya Khalifa ce ai na kirata yarinya tunda kuwa dai a haife Daddy ya haifeta sannan kuma girman da tayi mana bai wuce na shekaru uku zuwa hudu ba. Ni ai tunda ta yarda ta auri Daddy naji na tsaneta ni inaga dama can tana sonshi ta rasa yadda zatayi ne sai kuma ta samu Hajiya ta bullo da maganar aure a tsakaninsu, bakuga ko musu batayi ba ta amince ita a dole ga mai biyayya".
TUSHEN LABARIN.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
4
TUSHEN LABARIN
Ja'afar Bello Danmaliki haifaffen garin kano ne a cikin unguwar gadon kaya sai dai iyayensu asalinsu mutanen karamar hukumar gaya ne. Su biyu iyayensu suka haifa shi da kaninshi Ismail. Daga Ismail mahaifiyarsu da suke kira da Hajiya bata kara haihuwa ba hakanan kuma mahaifinsu bai yi sha'awar kara aure ba ko don ganin ya samu wasu 'ya'yan.
Ja'afar yayi karatu tun daga primary anan kano har ya gama secondary, daga nan ya wuce Nigerian defence academy wato nda a kaduna inda ya karanci engineering a bangaren army ya fito da mukamin 2nd lieutenant. A shekarar daya fito daga nda ne ya auri dadaddiyar budurwarshi tun ta yarinta wato Zainab wacce ta kasance 'yar makotansu.
Watannin aurensu goma Zainab ta haifi danta na farko Muhammad Bello mai sunan mahaifin Ja'afar suna ce mishi Khalifa. Khalifa nada shekaru uku ta haifi Ibrahim Mu'azzam. Bayan Mu'azzam ne ta haifi Khadija (Ummie) mai sunan mahaifiyarta. Tsakanin Mu'azzam da Ummie ma shekaru uku ne. A shekarar da Zainab ta haifi Ummie ne Ismail kanin Ja'afar yayi aure a cikin kuma shekarar ne dai Allah yayi mishi rasuwa a dalilin hatsarin mota, ya rasu ya bar matar shi da cikin wata shida.
Mutuwar Ismail ta kada Ja'afar sosai don kuwa akwai shakuwa sosai a tsakaninsu. Bayan watanni uku da rasuwar Ismail matarshi ta haifi diya mace akasa mata suna Farida. A lokacin da Farida ta isa shiga makaranta nevya karbota ya kawowa Zainab sannan ya sakata a makaranta tare da Ummie. Farida da Ummie sun taso tamkar 'yan biyu kasancewar duk sunyi kama da iyayensu maza ne don sau tari mutanebna dauka 'yan biyu ne.
Tun bayan Ummie Zainab bata kara haihuwa ba sai da aka shekara goma don har ta fara cire rai da haihuwa sai kuma Allah ya kawo. A ranar wata litinin ne da safe tana zaune tana shayar da jaririyar data haifa Ruqaiya Hajiya wato surukarta tayi sallama a tare da wata yarinya da bazata wuce shekaru goma sha biyu zuwa sha uku ba.
Mikewa tayi tsaye tana cewa "Hajiya sannu da zuwa" "yauwa sannu Zainabu sai ke kadai ko yaran duk sun tafi makaranta" tace bayan ta zauna akan kujera. Zaman itama Zainab din tayi tana cewa "wallahi kuwa Hajiya kinji yanda gidan yayi shiru sai sun dawo kuma, barka da asuba Hajiya an tashi lafiya" tace tana mai rusunawa. "Lafiya lau ya kwanan yaran" "lafiyarsu lau Alhamdulillah". "To Masha Allah dama yarinyace na kawo miki, ina take ne ma kame Aisha" tace tana waigawa. Tasowa yarinyar tayi daga inda take a bayan kujera tazo ta tsugunna tacr "Hajiya gani". Gyara zamanta tayi sannan tace "kinaji ba Zainabu yarinya ce 'yar kanwata a kauye uwar ta rasu shine na dauko ta ganin ita kadai uwar ta bari to shine naga gara na kawota nan wurinku tunda dai akwai yara sai ki hadasu ki rike ko 'yan aikace-aikace ta taya ki, amma don Allah Zainab ki rike mini ita amana tamkar 'yarki tunda dai da na kowa ne ladanki na wurin Allah bare ma rikon maraya Allah ne kadai zai biyaki".
Dagowa tayi ta kalli yarinyar. Ba laifi kam yarinyar tsaf take babu wani alamu na kazanta ko kauyanci a tare da ita. Tace "to Hajiya nagode Allah ya kara girma, Allah kuma ya tayani riko yaya sunanta". "Aisha sunanta, abokan wasa muke da uwar ta jima bata haihu ba saida girma ya fara kamata sannan Allah ya bata Aisha daga ita kuma bata kara haihuwa ba". Ta juya ta kalli Aisha tace "kina jina Aisha ga Zainabu nan a wurinta zaki zauna ki dauketa tamkar mahaifiyarki kiyi mata biyayya, da nan gidan da can wurina duk daya ne don haka kar ki sanu wata damuwa kinji, Allah yayi miki albarka"
"Bari na tafi Zainabu idan yaran sun dawo ace ina gaishesu" tace tana mikewa. Har wurin mita suka rakata sannan suka dawo ciki. "Zo nan kusa dani ki zauna" Zainab tace mata. Tasowa tayi ta zauna a darare akan kujera inda ta nuna mata. Dafata tayi tare da cewa "ki saki jikinki dani kinji Aisha, ki daukeni tamkar mahaifiyarki duka abinda kikeso ki gaya mini In Sha Allahu zanyi miki shi idan har baifi karfina ba, kuma daga yau Mami zaki na ce mini kamar yadda 'yanuwanki suke kirana, basanan suna makaranta yanzu amma idan sun dawo zaki gansu".
A hankali ta gyada kai tace "nagida Mami In Sha Allahu zaki sameni mai bin abin da kika ce". Mami tace "to haka ake so yanzu tashi muje na nuna miki dakinku". Tashi tayi ta dauki ledar kayanta tabi bayan Mami suka hau sama zuwa dakinsu Ummie. Daki ne babba yana dauke da gado 6by6 sai wardrobe din jikin bango da madubi. A wardrobe din Mami tace ta ajiye kayanta sannan ta nuna mata bandaki ko tana da bukatar shiga ta juya ta fita.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
5
Ko da su Ummie suka dawo daga school sun iske Aisha ne a dakinsu. Farida ta rike kugu tare da kare mata kallo kafin tace "ke! Wacece ke kuma me kikeyi a dakinmu?" Farida kam akwai tsiwa ba kamar Ummie ba data kasance mai hakuri don sau tari idan Farida nayiwa Ummie tsiwa sai ka dauka itace babba. Aisha tayi murmushi sannan tace "sunana Aisha kuma yanzu a gidanku zan zauna so na zama 'yar gidanku kenan", cikin farinciki Ummie tace "kenan anan dakin zamu zauna dake, kai amma naji dadi wallahi, ko Farida?" "uhm" Farida tace tana yatsina fuska. Uniform ta cire ta zubar dasu a tsakiyar dakin sannan ta debi kaya ta saka ta fice daga dakin tana kwala kiran "Mami mun dawo". Ita kam Ummie ta saka Aisha a gaba tana ta mata tambayoyi, ita dai Aisha murmushi takeyi kasancewarta ba mai yawan magana ba. Shigowar Mami dakin ne yasa suka dago suka kalleta. "Ku taso kuci abinci ke Ummie kin saka Aisha a gaba da surutu ko, wai ko uniform din ma baki cire ba" tace bayan ta karaso cikin dakin sosai. Tashi Ummie tayi tana cewa "yanzu zan cire Mami". Tace "to maza ki cire ku fito kuci abinci don ku kadai ake jira" ta juya ta bar dakin.
Bayan Ummie ta canja kayan makarantarta dana gida ne suka sauka kasa don cin abincin. Ummie taja kujera ta zauna sannan tace Aisha tazo ta zaunaa kujerar kusa da ita. Tsaki Farida tayi don hakanan taji bakuwar da aka kira da Aisha bata kwanta mata ba. Ita kam Aisha duk a takure take jinta don bata saba cin abinci a table kuma a cikin mutane haka ba. Mu'azzam ne ya dago yana cewa "Mami wacece wannan kuma da zata zo ta zauna mana anan bata san nan duka family bane, me ya kawo bare cikinmu"
Cikin kakkausar murya Mami tace "Mu'azzam yi mini shiru anan, Aisha ba bare bace itama 'yar gida ce don haka kar na kara jin makamanciyar magana irin wannan a bakinka, kai gaba dayanku ma hope you understand?", gaba daya suka ce "eh Mami". Bayan gama cin abincinsu ne suka koma daki, suna shiga Aisha ta hau tattare kayan Farid data zubar a kasa. "Ina za'a saka wadannan" tace wa Ummie, "kai mata toilet ki saka a cikin kwandon kayan wanki" ta amsata.
Da daddare ne Mami suna zaune da Daddy a sittingroom dinshi na sama take ce mishi "dazu Hajiya tazo har ta kawo mini yarinyar da zata na tayani aiki tace 'yar wata kanwartace data rasu shine ta dauko yarinyar, to ina tunanin a sakata a school maimakon zamanta a haka ko ya ka gani". Shiru yayai bai amsata ba, ita kam wannan hali na J.B sau tari yana bata mata rai don idan baiso ba duk maganar da zatayi ba amsawa yakeyi ba shine ma ya saka idan ta mishi magana taga bai amsata ba bata maimaitawa sai ta kyaleshi, don kanshi kuma idan yaso saibya dauko maganar.
Yanzun ma ganin bazai amsata bane yasa ta mike don taje tayi shirin barci. Har ta kai wurin kofa taji yana cewa "duk yanda kikayi daidai ne". Murmushi kawai tayi sannan tace "nagode bari naje nayi shirin kwanciya don barci nakeji, akwai abinda kake bukata?" Cikin ginshira yace "yeah, only you". Wata kasalalliyar dariya tayi sannan tace "hmm Daddy kenan" ta juya ta bar parlour cikin rangwada. Hannu yasa ya shafa kwantacciyar sumarshi yana mai lumshe ido, murmushi dauke a fuskarshi. Shi kam Allah ya sani yana son Zainab sosai, after all these years yana jinta a ranshi tamkar yau ya fara sonta. Tashi yayi shima ya nufi dakin din yayi shirin kwanciya.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
7
A haka dai rayuwa taci gaba da tafiya. Ga Aisha dai ta dada kame kanta daga shiga harkar Farida da Mu'azzam don ta lura akansu zaman gidan zai iya gagararta. Ita kuwa a yanda takejin dadin zama da Mami ga kuma ingantaccen ilimi duka biyu wato na addini da boko da take samu baza taso tayi abinda zai rabata da zaman gaidannan ba.
Ga kuma baby Ruqaiya da sukayi wata irin shakuwa da ita don mafi yawan lokuta idan tana wurin Aisha ko Mami bata yarda ta dauketa sai da kyar. To shima Daddy a nashi bangaren bai kara maganar mayar da ita gidan Hajiya ba, kodayake a yanzu duk fitinar Farida da neman rigimarta ta kyale Aisha ganin bata shiga harkarta.
A yanzu haka Aisha tana ss1 ne yayin dasu Ummie suke jss3. Tun zuwan Aisha gidan sau daya taje garinsu tayi hutu na sati uku. A wannan lokacin ma hutun take son zuwa sai dai kuma kasancewar ciki ne da Mami tsohi yasa dole ta hakura. Ko babu komai tana taimakawa Mami da hidimar gidan don zuwa wannan lokacin babu wani abu da bata iya ba a kitchen.
Mafi yawan lokuta zaka sameta ne a kitchen tare da Mami da sauran ma'aikatan gidan, abinda bazaki taba ganin Ummie ko Farida sunyi ba. Yanzu ma aikin abincin dare sukeyi ita da Mami a kitchen. Yaya Khalifa ne ya shigo kitchen din yace "sannu Mami, mezan samu wallahi na gaji da yawa ga yunwa na kwaso, yau tunda muka fara lectures tun 12 sai six muka gama without any interval".
"Sannu Yay Khalifa ai kana kokari wallahi Allah dai ya bada sa'a". "Amin Aisha nagode, me kukayi ne da rana? Yace bayan ya zauna akan kujerar kitchen din. "Favourite dinka ne wato faten doya bari na zuba maka" tace bayan ta dauki plate ta zuba mishi abincin sannan tace mishi "anan zakaci ne ko na kai maka parlour". "Bari kawai na wuce dashi Aisha nagode" yace yana mai tashi daga kan kujerar. Karbar abincin yayi ya fita a kitchen din. Bayan sun gama hada abincin ne Mami ta fita ta barta a kitchen din ta karasa gyarawa. Sosai take tausayawa Mami ganin duk da tsufan cikinta hakan bai hanata yin hidimar gidanta ba.
A daren ranar suna kwance suna bacci Mami ta shigo dakinsu ta tashi Aisha. "Lafiya Mami?" tace bayan ta tashi zaune. "Saka hijabinki ki taso asibiti zamuje" tace mata a yayin da take barin dakin. A hanzarce ta tashi ta daura zani akan kayan baccinta ta dora hijabi ta fita zuwa dakina Mami. Akwatin da Mami ta hada don zuwa asibiti ta dauka suka fita. Koda suka fita harabar gidan tuni Daddy ya juyo da mota, gidan gaba ta budewa Mami ta shiga sannan ta koma baya ta zauna.
A lokacin da suka isa asibitin karfe daya da rabi ne na dare. Suna zuwa direct labour room aka wuce da Mami, su kuma suka samu wuri anan rwception din suka zauna. Nesa sosai da Daddy Aisha ta zauna, duk sai tana jinta a takure don ita dai hakanan take jin tsoron Daddy bata taba sakewa dashi ba shima kuma bai taba sakar mata fuska ba tsakaninta dashi gaisuwa ce kawai.
Basuyi zaman awa daya ba a wurin nurse ta fito ta fada musu Mami ta haihu diya mace. Gaba daya annurin farinciki ne ya sauka a fuskar Daddy, mamaki ne ya kama Aisha don kuwa bata taba ganin fara'arshi haka ba. Ba'a wani jima sosai ba aka fito da Mami da babynta zuwa wani dakin. Bin bayansu sukayi zuwa dakin da aka kwantar da ita. Daddy na rike da baby sai faman fara'a yakeyi yana ce mata "sannu Zainab", ya dade a asibitin kafin yayi sallama da Mami ya tafi gida don a lokacin kausan karfe uku da rabi ne na dare. Daga Mami har Aisha basu wani samu yin barci ba saboda baby bata barsu ba. Sauki daya suka samu ma shine da safe da likita yazo ya dubasu ya basu sallama. Anyi sallamar babu dadewa Daddy ya shigo dakin hannunshi rike da kwandon kayan abinci. Da sauri Aisha ta tashi ta karbi kwandon a hannunshi sannanta gaisheshi. Yana amsawa ya karasa kan gadon ya zauna yana yiwa Mami sannu tare da amsar baby a hannunta. Breakfast kawai sukayi suka koma gida kasancewar anyi discharging dinsu tun kafin zuwan Daddy. Da isarsu gida yaran gaba daya suka fito suna ihun Murna. Rige-rigen karbar baby sukeyi, Mu'azzam ne ya karbi babyn a hannun Aisha ita kuma ta fito da kayansu suka shiga cikin gidan. Cikin kankanin lokaci gidan ya cika da baki 'yan barka don haka nema hutun da Aisha take bukata bata sameshi ba saboda hidima da tayi mata yawa.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
6
Washegari suna kan table suna breakfast Daddy ya sauko daga sama a bayanshi Mami ce rike da briefcase dinshi. Kujera taja mishi ya zauna sannan taja kujerar dake gefen damanshi ta zauna. Yaran duka suka gaisheshi ya amsasu cikin kulawa. Itama Aisha gaisheshi tayi tana mai tsugunawa. "Lafiya" kawai yace ya cigaba da magana da yaranshi. Gaba daya sai taji ta muzanta, anya kuwa maigidan yana maraba da zamanta cikin iyalinshi. Duk sai taji abincin ma ya fita daga ranta. A haka dai ta daure ta tuttura. Bayan kowa ya gama ne suka tashi suka fita, yaran suka tafi school shi kuma Daddy ya tafi office. Ya rage daga Aisha sai Mami sai ko baby Ruqaiya. "Mami kawota" Aisha tace tana mai mikawa hannu don karbar Ruqaiya. A baya ta sakata ta goya sannan ta haya sama ta nufi dakinsu ta hau gyarawa. Kayan Farida ne duk a barbaje a tsakar dakin ga alama dai Farida bata san ta cire kaya ta adanasu ba. Daga zuwanta jiya zuwa yau ta lura Farida sakaltacciyar yarinya ce saki yayi mata yawa.
Bayan ta gama gyaran dakinsu ne ta shiga dakin Mami don ta gyara. Nan kam a gyare yake tsaf don haka juyawa kawai tayi ta sauka kasa. A parlour ta iske Mami tana kallon the doctors a mbc4. "Sannu Mami" tace a yayin da take zama a kasa. "Yauwa sannu Aisha, me yasa kike son zama a kasa ne, tashi ki koma kan kujera", tashi tayi ta zauna akan kujerar. Mami tace mata "su Ummie sun tafi makaranta sun barki ko, kema inaso ki fara zuwa ina fata daikin fara karatu acan garinku". Tace "eh Mami na fara ina jss2 yanzu haka". Mami tace "Masha Allah, akwai wata makaranta a kasan layinnan zanje na duba In Sha Allahu zuwa wani satin zaki fara zuwa". Durkusawa tayi tace "nagode Mami Allah ya saka da alkhairi".
Dariya Mami tayi tace "tashi da Allah daga durkuson nan, baki daukeni uwa har yanzu ko, miye abin godiyar to ai dolenmu ne muyi miki hidima tunda dai ke amana ce a hannunmu. Jeki kwantar da Ruqaiya sai kizo mu shiga kitchen ki tayani girki ko".
A cikin satin aka gama yiwa Aisha komai na makaranta anan wata private school dake cikin unguwar sun dauketa a jss2 din da take kasancewar sun gwadata sunga tana da kokari sai dai rashin samun ingantaccen ilimi yasa turancinta yake da rauni, ganin haka nema yasa Mami ta shirya da malamarsu ta english zatana yi mata lesson akan turancin. Duk da makaranta da Aisha ta fara zuwa, wannan baisa ta daina yiwa Mami hidimar da takeyi mata ba kamar gyaran dakinta da nasu dakin da kuma wankin kayan Ruqaiya. Hakanan kuma rainon Ruqaiya na cikin aikinta idan ta dawo daga makaranta.
Sosai Mami take jin dadin zama da Aisha don kuwa yarinyar bata da kyuiya duk abinda ta sakata shi takeyi. Itama kuma Aisha tana jin dadin zamanta da Mami don kuwa Mami mutum ce mai alkhairi da kuma son mutane, gashi kuma a komai bata yin bambanci tsakaninta dasu Ummie da suke 'ya'yanta komai tayi musu itama shi takeyi mata. Ko tana da matsala a zamanta a gidan to da Farida nel data takura mata ta hanata sakat don ko wasa sukeyi da Ummie idan tazo wurin to ta barshi. Sai ko Mu'azzam shima yana takura mata amma ba kamar Farida ba, shi kam Yaya Khalifa babu ruwanshi don baya na shiga harkarsu.
A yammacin wata lahadi ne bayan malamin dake yi musu karatun islamiyya ya tafi ne suka nufi filin wasansu. Kowa da kalar wasan da yake yi, Ummie da Aisha dai lilo suka hau Ummie tana tura Aisha. Farida da Mu'azzam kuma wasan guje-guje sukeyi. Abin tsautsayi Ummie tana shilla Aisha ne ita kuma Farida ta taho a guje Mu'azzam na binta kawai tayi karo da kafar Aisha ta hantsila ta fasa hanci.
Wata irin razananniyar kara ta saka. A guje duk sukayi wurinta suna mata sannu ganin yadda jini yake fita daga hancinta duk sai suka rude. Gaba daya suka nufi cikin gidan in banda ihu babu abinda Farida takeyi. A rude Mami ta taso tana tambayarsu lafiya. Mu'azzam ne yace yana mai nuna Aisha "gatanan itace ta hankadata ta fadi ta fasa hanci". Cikin daga murya Ummie tace "laa bafa haka akayi ba, Mami ina tura Aisha ne a lilo su kuma suna wasan guje-guje sukayi karo da Aisha ta fadi ta fasa hanci", "ke yi mini shiru da bakya magana a hankali" tace da Ummie. "kai kuma matsa ka bani wuri naje na wanke mata ciwon, ai duk laifinkane don kuwa na hanaku wasan guje-guje amma bakwa ji".
Mami taja Farida zuwa bathroom ta wanke mata jinin daya bata mata fuskar sannan ta bata paracetamol tace ta kwanta ta huta. A ranar kam da Daddy ya dawo ya tarar da abinda ya faru yayi fada kamar me har yana cewa Mami shifa idan rikon bazai yiwu ba sai a maida Aisha gidan Hajiya din bazai lamunci ganganci akan yaranshi ba. Shi Daddy wani irin mutum ne mai son yaranshi hakanan baya son wani ya rabeshi, ko rikon Aishacma abinda yasa baiyi magana ba saboda Hajiyarahi ce ta kawota gidan amma da babu abinda zai sa ya karbeta. Ita dai Mami hakuri kawai take bashi don kuwa tana matukar jin dadin zama da yarinyar.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
8
Tun bayan da Mami ta haihu gidansu bai rabu da jama'a ba. Don Aisha ma ko makaranta bata samun zuwa saboda hidima da tayi mata yawa. Ga aikin jego ga kuma hidimar Ruqaiya da kacokam ta dawo hannunta.
A ranar da akayi kwana biyar ne da haihuwar da safe Aisha na zaune a dakin Mami tana shirya kayan baby data wanke Mami ta shigo cikin dakin dauke da baby. Kwantar da ita tayi akan gado sannan tace da Aisha "idan kin gama shirya kayan kawo mini kunu sai kizo ki janyo mini wancan akwatin". Bayan ta gama shirya kayan ne taje kitchen ta damowa Mami kunun gyada sannan ta kawo mata. Akwatin data ce ta janyo mata tare da budewa ta fito da kayan ciki. Laces ne guda uku sai atamfar super holland guda hudu da voiles guda uku. Mami tace "miko mini na gani" tashi tayi ta mika mata kayan. Dagawa Mami tayi ta kalla sannan tace "wai nan kayan fitar suna ne Daddy ya mini sai kace wata yarinya, nikam ai na gaya mishi babu wani taron suna da zanyi".
Aisha ta kara daga kayan ta kalla sannan tace "ai kuwa dai Mami kayan sunyi kyau, Allah ya sakawa Daddy da alkhairi, amma Mami meyasa bazakiyi taron suna ba". Dariya Mami tayi tace "kayya Aisha taron suna ai na yara ne, haihuwa ta biyar ni kuwa wani suna zanyi, don wani abu irin na Daddy ma wai baby sunana ya saka mata nayi-nayi dashi ya saka sunan Hajiya yace a'a".
Cikin fara'a sosai Aisha tace "Allah ya rayata, kuma Mami me za'ace mata?" "Zainab dinta zaku kirata don banason boye sunannan" a cewar Mami. "Ina Ruqaiya ne duk yau ban ganta ba" Mami ta tambayeta. "Tana wurin Lami tun bayan dana mata wanka ta dauketa ta goyata to inaga bacci takeyi tunda kikaga shiru bata kawo taba". Aisha ta amsa mata.
A ranar suna ne baby taci sunan Mami wato Zainab. Kasancewar Mami ba taro takeyi yasa gidan bai cika da mutane ba amma duk da haka 'yanuwa na jiki duk sunzo don haka aiki yayi wa Aisha da sauran ma'aikatan yawa don sai faman dora abinci sukeyi suna saukewa. Ita dai Aisha har ta matsu dare yayi ko ta samu ta kwanta ta huta.
Bayan suna ne da kwana biyu suna zaune a parlour gaba gayansu yaran gidan suna hira Mami kece mata idan anyi hutu sai ta shirya taje garinsu ta kwana biyu. Sosai taji dadi sai dai kuma tana tunanin udan har ta tafi yadda hidima zatayiwa Mami yawa, bata dai yi magana ba don kuwa tana kewar Babanta zataso taje ta ganshi.
Murmushi tayi sannan tace "to Mami nagode Allah ya kara girma". Kallonta Ummie tayi sannan tace "umh Aunty Aisha sai murna kikeyi zaki tafi ki barmu ko tausayinmu bakya ji bayan kinsan zamuyi missing dinki sosai". Tsaki Farida tayi hade da tabe baki tace "kedai zakiyi missing dinta nikam da zamanta da rashinshi duk daya ne a wurina don rayuwata nakeyi tamkar babu ita a cikin gidannan".
Murmushi kawai Aisha tayi ta dauke kai. Ita dai ta rasa abinda ta tsarewa Farida a cikin gidannan don ko magana idan har ba ita tayi mata ba batayi mata shima kuma ba lallai ne ta amsa ba. Wannan kuma baisa ta daina yi mata magana ba koda kuwa kullum ta mata bazata amsa ba.
Tun bayan da Mami tayi mata maganar zuwa gida ta fara shiri don ta fitar dakayanta da yawa da zata bayar a garinsu wa 'yanuwanta haka ma kuma Mami ta hada mata kayan bayarwa nabyara da yawa da zata rabar acan. A daren da zata tafi ne tana zaune a tsakar dakinsu tana shirya kayanta a cikin akwati Mami ta shigo hannunta rike da bakar kedar viva. Zama tayi a bakin gadon sannan ta mika mata ledar , jarba tayi tana kallon Mami da alamar tambaya a fuskarta. " Na Babanki ne da kuma goggonki wato matar Babanki ga kuma wannan ki kaiwa babanki inji Daddy sai kije kiyi mishi godiya" ta mika mata envelope.
Russunawa tayi hadi da karbar envelope din tace "nagode Mami Allah ya saka da alkhairi ya kara budi". Bayan data gama hada kayan ne ta nufi parlour Daddy don tayi mishi godiyar alkhairin daya yiwa mahaifinta. Daga bakin kofa ta tsaya tayi sallama, sai bayan an amsa ne tare da bata izinin shiga sannan ta shiga. Durkusawa tayi ta gaisheshi sannan ta mishi godiya ta tashi ta fita. Ruqaiya dake wasa a parlour ta taso ta biyota tana rigimar sai ta goyata. A daren ranar dai baccin Aisha rabi da rabi ne don dokin zataje taga Babanta.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
9
Tun bayan da Aisha tayi sallar asuba sai bata koma bacci ba sai ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin atamfar mediym holland dinkin riga da zanu. Koda ta shirya sai ta hau gyaran gidan inda duk tasan ita ke gyarawa. Bayan ta gama ne ta shiga dakin Mami. Bata sameta a dakin ba don haka sai ta shiga gyaran dakin. Tana cikin yin shara ne Mami ta fito daga bandakin ga dukkan alamu wanka tayi.
"A'a Aisha har kin shirya" tace a lokacin da take zama a kan stool din dressing mirror. "Eh Mami, ina kwana" "lafiya lau, kin ma kuwa yi bacci irin wannan sakko haka" dariya tayi tace "nayi bacci Mami kawai dai tunda nayi sallah ban koma ba. Me za'ayi as breakfast naga kwana biyu ba'a bin timetable"? Mami tace ai kuwa dai, sabon timetable nakeso nayi har yanzu kuma ban samu lokaci na zauna ba. Ki bare doya a dafa sai ayi doya mai kwai hade da farfesun kayan cikin da mukayi jiya yana cikin fridge warming kawai za'ayi sai tea. Kije ki fara kafin na gama shiryawa na fito kitchen din".
Tattara sharar tayi sannan ta nufi kitchen don tayi aikin da Mami ta sakata. Sai dai ta kusa gama hada breakfast din sannan Mami ta shigo ta tayata suka karasa. Karfe goma batayi ba su Aisha suka dauki hanya ita da Mallam Adamu driver. Sosai Ruqaiya tayi kuka ganin Aisha zata fita babu ita. Ita kanta Aisha sai da ta zubar da hawaye ganin yadda Ruqaiya ke kuka.
Sun isa garinsu wurin karfe sha daya. Basu sami Babanta a gida ba har ya fita kasuwa sai Goggo kawai suka samu da 'yan jikokinta suna wasa. Karba sosai akayi mata. Ruwa kawai Mallam Adamu yasha ya juya ya bar Aisha sai bayan sati biyu zai dawo ya dauketa. Bayan taci abinci ta huta ne ta fita gidajen makwabta fon ta gaishesu. Duk gidan data shiga suna mamakin girmanta da wayewar da tayi. Ba ita ta koma gida ba sai goshin magriba, koda ta koma gida Babanta ya dawo. Sosai yaji dadin ganinta. Sai bayan anyi isha'i ne sannan ta fito musu da tsarabarsu suna ta murna tare da saka albarka. Bayan nanne suka zauna da Babanta suna hira, sai tambayoyi yakeyi mata akan zamanta dasu Mami ko tana da matsala duk da dai baiga alamar hakan a tare da ita ba amma zaiso yaji hakan daga bakinta. Sai da ta tabbatar mishi bata da wata matsala sannan suka shiga hirar duniya.
Anan nema yake ce mata shidai zaiso ace data gama secondary school idan har ta samu miji ta kawoshi gida ayi mata aure don mutuncin diya mace shine dakin mijinta don anan garinsu har an fara surutun rashin aurenta don ma ba ganinta akeyi ba.
Sosai Aisha taji dadin zuwanta gida don ta zagaya 'yanuwanta na wajen uwa da uba ta sada zumunci don haka ne ma taga sati biyun tayi saurin karewa. Koda safiyar da zata koma kano tayi ta gama shirinta tsaf kafin lokacin da Mallam Adamu yazo daukarta. Duk wani tsaraba da zata tafi dashi an hada mata shi wuri daya. Babanta ma bai fita kasuwa ba din yana so yaga tafiyarta kafin ya fita. Kafin karfe sha biyi Mallam Adamu har ya iso, babu bata lokaci tayi sallama da duk mutanen gidan ta fito tana sharar kwalla ta shiga mota suka dauki hanyar kano.
Suna hawa titi ta fara bacci wanda ba ita ta farka ba sai da suka iso gida taji Mallam Adamu nace mata ta tashi sun iso gida. Farkawa tayi da salati a bakinta ta kalli harabar gidan sai taga tamkar yaune ta bar gidan gashi har taje ta dawo. Da sallama ta shiga cikin parlour babu kowa a ciki don haka ta wuce kitchen don tasan a wannan lokacin acan zata samu Mami. Sosai Mami tayi murnar dawowarta. Bayan sun gaisa ne ta haya sama don ta ajiye kayanta. Data sauko ne take tambayar Mami inasu Ummie tace mata suna gidan Hajiya acan zasu yini. "Kuma Mami har Ruqaiya sukaje gidan Hajiya"? "A'a tana dakina tana bacci bata dade da kwanciya ba kika shigo".
Koda Ruqaiya ta farka taga Aisha ai sai ta makale mata ta hanata sakat duk inda ta saka kafa nan take maida tata. Ko gani takeyi zata kara tafiya ta barta ne. Su Ummie basu dawo gida ba sai wurin takwas na dare. A lokacin Aisha ce kadai a parlour don Mami tana sama tare da Daddy. Ganin Aisha a zaune da gudu Ummie tazo ta rungume ta tana murna cewa takeyi "Wallahi Aunty Aisha munyi missing dinki sosai kullum Ruqaiya sai tayi mana kuka ita akaita Aunty Aishanta gashi komai akayi mata sai tace sai ta gayawa Aunty Aisha idan ta dawo".
Ita kanta Aisha taji dadin ganinsu don kuwa tayi kewarsu sosai. Farida ce ta kalleta a sheke tace "huh lallai zaman kauye dai baiyi ba, Allah nagode maka da ban hada komai da kauye ba da ko yaya mutum yaje kauye ya dawo sai ya canja". Dariyar shakiyanci Mu'azzam ya saka sannan yace mata "ai wannan uwar kibar da kike narkawa kamata yayi a kaiki kauyen ko kya sabe, wuu wa yaga Farida a kauye" ya kyalkyale da dariya har yana rike ciki. "Amma dai wallahi Yaya Mu'azzam ka cuceni, aini ko ace daga kauye nake idan na samu na rabu da zaman kauye babu abinda zai maidani ballantana ma mi yayi gamin jirgi da mita" tace tana murguda mishi baki. Haka dai sukayi ta shakiyancinsu Aisha na jinsu tayi tamkar bata san ma sunayi ba.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
10
A haka dai rayuwa taci gaba, gashi Aisha har ta gama secondary school ta samu cigaba a makarantar Sa'adatu Rimi college of Education tana karantar catering wato fannin girke-girke.
A yammacin wata alhamis ne Aisha na kitchen tana taya Mami hidimar abincin dare, Mamin ce ta shigo kitchen din tace "sannu Aisha na tafi na barki da aiki ko, wai ina wajen Daddy muna maganar tafiya Umrah da zamuyi tunda yara suna hutu, inaga ko wajen jibi sai ki shirya ki koma wajen Hajiya kafin mu dawo tunda tafiyar zata kama ranar lahadi ne".
"Ashe tafiyar tazo, Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya. Mami ayi mana addu'a, In Sha Allahu zanyi shirin. Har kwana nawa zakuyi? "Inaga sati biyu ne" inji Mami.
Tunda Farida taji batun tafiyarsu Umrah taji kuma babu Aisha a tafiyar take ta faman yada mata da habaici. Ita kam Aisha ko kallonta batayi ba. Wani abu da Farida bata sani ba shine bata taba hada kanta dasu ba. Tasan matsayinta a gidan na 'yar cin arziki ta kuma san nasu matsayin na 'ya'yan gidan.
Wannan nema dalilin da yasa bata taba daga ido ta kalli wani abu da akayi musu da ba'ayi da itaba duk da dai Mami na kamantawa mawuyacin abu ne tayi musu wani abin batayi mata ba amma wasu lokutan tana yi din ita kuma Aisha hakan bai taba damunta ba.
A kowanne lokaci ta kasance mai godiyar Allah da bais ta zama mai kwadayin abin wani ba. Banda haka da tasha takacin Farida don kuwa sau tari Daddy yanayi musu kyauta ita da Ummie ba tare da ya hada da ita ba. Idan irin haka ta faru Farida ta dinga iyawa tana kafafa kenan duk don ta kular da ita.
Bata manta wani lokaci da Daddy yayi wata tafiya zuwa ingila ya kawowa su Ummie wayoyin hannu a matsyin tsarabarsu. Firirita da iyawar da Farida tayi mata a lokacin don ta kular da ita nada yawa. Ita kam ma dariya abn ya dinga bata don ganin ita dai wayar ma ba damunta tayi ba kuma ba wanda zata kira a waya gareta ba bare ta damu.
A yammacin asabar bayan ta gama hada kayanta zata tafi gidan Hajiya ne ta suka kasa don su kara yin sallama da Mami kafin ta wuce. Kowa na tambayarta abinda takeso su saya mata harda Zainab sai abinma ya bata dariya.
Da zata tafi ne Mami ta kawo kudi ta bata koda zata bukaci wani abu ba sai ta tambayi Hajiya ba. Godiya sosai tayi mata sannan ta dauki jakar kayanta ta kara yimata sallama ta fita. Har mota su Ummie suka rakata, ganin ta shiga mota sai Zainab ta fashe da kuka wai sai ta bita. Da kyar Ummie ta janyeta suka koma cikin gida.
Ta sani itama zatayi kewar Ruqaiya da Zainab sosai domin kuwa ta shaku da yaran ba kadan ba. Duk wata hidima tasu itace tun daga kan wankansu, cin abincinsu, shirinsu zuwa makaranta, kitsone da koya musu homework duk ita keyi. Mafi yawan lokuta ma tare suke kwana a dakin yaran.
Da sallama ta shiga cikin gidan tana janye da akwatinta. Baaba Indo mai aikin Hajiya na tsugune a bakin famfo tana wanke-wanke. Dagowa tayi tare da amsa sallamar tana cewa "maraba da takwara yanzu da yammannan kike tafe".
Cikin fara'ar da bata yankewa a fuskarta tace "eh Baaba Indo mun sameku lafiya" tace "lafiya lau hala dai zaki kwana mana biyu na ganki harda akwati". Aisha tace "eh sati biyu zanyi muku" tace "kai madalla kice muna da babbar bakuwa".
Murmushi kawai tayi ta wuce dakin Hajiya. Bata sameta a parlour ba sai ta wuce cikin dakin. A zaune akan sallaya ta tararda ita tana karatun AlQur'ani don haka akwatin kawai ta ajiye ta fito parlour ta zauna. Tayi kusan mintina goma a zaune kafin Hajiya ta fito daga dakin. Zamowa tayi daga kan kujerar ta gaisheta.
Bayan sun gama gaisawa ne Hajiya ke cemata taje kitchen ta debi abinci. "Wallahi na koshi Hajiya sai dai ko zuwa anjima" tace mata. Jefi-jefi suke hira da Hajiya har aka kira sallar magriba suka tashi don yin sallar.
Aisha dai bata tashi akan sallayar ba sai bayan da tayi sallar isha. Ko a gida ta saba bata tashi bayan magriba zama takeyi tayi tilawar karatun Alqur'ani har sai an kira sallar isha tukunna ta tashi tayi.
Bayan ta Isar ne ta fito ta debi abinci tana ci suna hira da Hajiya. Sallamar da Daddy yayi ne ya katse musu hirar da sukeyi. Yana zama Aisha ta gaisheshi ta tashi ta koma cikin daki taci gaba da cin abincinta.
Sallama ya shigo yayi wa Hajiya don jirginsu da safe zai tashi. Sun dade suna hira irinta tsakanin da da mahaifi.
Sosai yanda yake bawa Hajiya girmanta yake burgeta din kuwa kudinshi da mukaminshi basu saka ya banzatar da mahaifiyarshi ba, komai na jin dadin rayuwa ya wadata dashi.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
11
Sosai takejin dadin zamanta da Hajiya. Ko babu komai tana karuwa da ita sosai ta fannin ilimi don kuwa mawuyacin abu ne kaji Hajiya ta zauna tana sakin zance barkatai. Duk wata magana da zata fito daga bakinta mai ma'ana ce ko da kuwa a cikin hira ne.
Suna zaune a parlour suna kallon tashar Sunna TV wayar Hajiya dake ajiye akan tv stand ta dauki kara. Tashi Aisha tayi don ta dauko wayar. Intetnational number ta gani akan screen din.
Mikawa Hajiya wayar tayi sannan ta shige daki don ta bawa Hajiya wuri ta amsa wayarta ga alama mutanen saudia ne suka kirata.
Tayi kusan mintuna goma da shiga dakin sai ga Hajiya ta shigo ta mika mata wayar tace mata "karba Maminku ce akan layi". Da sallama ta amsa wayar sannan tace "Mami ina yini, ina Zainab da Rukieta?" "Lafiya lau Aisha, ya gida" Mami ta amsa mata. "Gida lafiya lau Mami, yasu Ummie da Farida dasu Ya khalifa. Wai yaushe zaku dawo ne Mami wallahi sosai nake cikin kewarku". "Muma muna kewarki Aisha, ga yaranki nan sun hanani sakat ni kaina na matsu mu dawo ko na huta kullum cikin rabon fada nake".
Dariya Aisha tayi tace "ayya Mami kice idan kuka dawo sai na basu purnishement tunda suka wahalar mini da Mamita".
Sun dade suna hira da Mami kafin sukayi sallama. Tashi tayi ta kaiwa Hajiya wayarta sannan ta zauna suka cigaba da kallon da sukeyi. Ji tayi Hajiya na magana don haka ta dawo da hankalinta gaba daya wurin Hajiya. "Na'am Hajiya me kikace" tsaki Hajiya tayi sannan tace "fadan Maminku nakeyi wai gaya mini takeyi ta gaji hidimar yara tayi mata yawa. Dama ni tunda suka yi maganar tafiya Ummara da yara banji sun saka dake ba shiru na musu ban yi magana ba tunda sun riga sun gama tsarinsu amma ko don ki tayata da hidimar yara ai da sun tafi dake. To shi Jafaru wani irin baudadden hali gareshi abinda yasa kanshi shi yakeyi ni kuwa ban cika son shiga sha'anin gidanshi ba. Ita kuma Zainab tsoronshi takeyi duk abinda yace ko baiyi mata ba bata iya musa mish. Yo dama wadannan malalatan yaran nata me suka iya bare har su tayata da rainon yara, su da basa iya tsinanawa kansu komai bare suyi wa wani".
Aisha dai shiru tayi tana sauraren Hajiya ba tare da ta tanka mata ba.sai dai cikin ranta mamaki ne takeyi wao kenan har Hajiya ma tasn halin Daddy na rashin son mutane su rabeshi, sai dai kuma ba abin mamaki bane tunda itan mahaifiyarshi ce. Ita kam ta sani ko ita karfin zamanta a gidannan Mami ce da don tashi ne da tuni ta dade ba barin mishi gida.
A ranar da tayi sati biyu a gidan Hajiya ya kama washegari su Mami zasu dawo ta shirya ta tafi gidan don ta gyara duk da dai akwai masu aiki a gidan to amma gyaran sama gaba daya aikinta ne 'yan aiki basa gyara musu dakunan barcinsu.
Aikin da tayi ya dauketa tsawon lokaci kafin ta gama. Gidan Hajiya ta koma ta kwana gari na wayewa ta koma gidan din ta shirya musu abinci. Fried rice tayi da coleslaw hade da peppered chicken sai tuwon alkama miyar kubewa busashiya da tayi saboda Daddy yafi son abincin gargajiya fiye da komai.
Karfe biyar da kwata na yamma su Mami suka shigo harabar gidan tare da Mallam Adamu da yayi kanin yini a airport yana jiran saukarsu. Aisha najin tsayuwar motarsu ta fito da sauri tana murna.
A guje Ruqaiya da Zainab suka taho suka rungumeta. Ita ma farincikin ganinsu duk ya cikata. Rike hannuwansu tayi ta karasa wurinsu Mami tana yi musu sannu da zuwa. Gaba dayansu suka dunguma zuwa cikin gida. Dukansu a parlour suka zauna sai Mami da Daddy ne kawai suka haya sama.
Ruwa da lemuna Aisha ta kawo musu tana yi musu sannu. Tana zama Zainab da Ruqaiya suka sakata a gaba da labari. Farida da Ummie kam kujera kowaccensu ta hau ta kwanta yayinda Yaya Khalifa da Mu'azzam suka wuce dining area don cin abinci.
Sai bayan kusan minti talatin sannan Mami ta sauko. Ga alama wanka tayi don ta canja kayan jikinta zuwa doguwar rigar atamfa. Table din ta nufa tana bude kwanuka.
Tashi Aisha tayi ta nufi table din. Durkusawa tayi ta gaida Mami tare da yi mata barka da dawowa. Bayan sun gaisa ne Mami kece mata "sannu a kokari Aisha Allah ya biyaki, duk ke kadai kikayi wannan aikin?" Dariya kawai tayi tace "amin Mami". Hada abincin Daddy Mami tayi sannan ta dauka ta koma sama ga alama dai yau a saman zaici abincin.
Da dare ne bayan anyi sallar isha'i Aisha taja Zainab don ta rakata ta gaida Daddy. A parlournshi na sama ta same shi yana kishingide akan doguwar kujera. Ganinta baisa ya tashi zaune ba. Durkusawa tayi ta gaisheshi tare da yi mishi barka da dawowa.
A dakile ya amsa mata gaisuwar da lafiya. Tashi tayi ta fita ta bar Zainab da tun shigarsu parlourn ta nufi wurin Babanta ta zauna.
Washegari da safe ne Mami ta bata tsarabarta. Dogayen riguna ne masu kyau guda biyu daga Mami sai wani agogon hannu inji Daddy. Sosai Aisha tayi murna da tsarabar da aka bata.
Ruqaiya da Zainab ma matetial suka bata sai Ummie da ta bata kayan bacci riga da wando. Yaya Khalifa kuma ya bata takalmi sai Mu'azzam da ya bata agogo, ta tashi da agogi biyi kenan.
Farida kam ko kallonta batayi ba bare kuma tasaka rai da tsarabarta. To ita dinma bata saka rai tunda dai tasan tsakaninsu da Farida, amma kuma duk ma'aikatan gidan babu wanda batayi wa tsaraba ba har masu gadi.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
12
A kwana a tashi nmbabu wuya wurin Allah. Gashi har Aisha ta gama dalilin da yasa ta cewa Mami tana son zuwa gida don kuwa ta dade bata jeba. Sati biyu taso yi amma sai Mami tace tayi sati daya don bata son tana yin nesa da ita. Ba don taso ba ta amince sai don bazata iya musawa Mami ba.
Bayan kwana biyu ne ta shirya ta tafi gaya. Sosai mutanen gidan sukayi murnar ganinta. Goggo ta sauketa da fura da nono da danwaken wake da rogo mai dan karen dadi.
Sosai taci danwaken don ta dade rabon da taci. A kano basayin danwake don yaran gidan duk basa so shi yasa Daddy yace a daina yi tunda babu maiso.
Tana gama cin abincin ta haye gadon Goggo ta kwanta barci inda ba ita ta farka ba sai da la'asar. Bayan tayi sallar ne ta fita zuwa gidan yayarta Huwaila wacce ta kasance babba a gidansu haka kuma 'ya a wurin Goggo.
Da murnarta ta tareta, bayan sun gaisa ne ta kawo mata kunun aya mai dadi tasha kasancewar sana'arta ce saida kunun aya. Suna cikin hira ne ta sako mata maganar aure tace "amma dai zuwa yanzun kin tsaida miji ko don tun dadewa ya kamata ace an aurar dake".
Yake Aisha tayi tace "Yaya Huwaila kenan". Hade rai Yaya Huwaila tayi tace "ban gane da ni kenan ba, kina nufin har yanzu baki tsaida miji ba Aisha kin kuwa san yadda Baba ya damu da batun aurenki? Shiru fa kawai yayi don yana jin nauyin Hajiya bayaso ya nuna musu ikonshi akanki amma banda haka ai da tuni yayi magana akan zamanki a haka don ba so yakeyi ba ko karatun da kikayi don babu yadda zaiyi ne amma da don tashi ne da kina gama secondary school za'a aurar dake".
Gaba daya jikinta taji yayi sanyi jin cewar Baba ya damu da zamanta haka babu aure. Banda abin Baba ma dai miye abin damuwa don takai yanzu ba tayi aure ba tunda dai ba wai ta wuce lokacin auren bane bare ace ta rasa miji. Shine fa dalilin da yasa wasu lokutan bata cika son zuwa gida ba don kuwa idan tazo an dunga yi mata surutu akan rashin aure kenan.
Bata bar gidan Yaya Huwaila ba sai bayan da tayi sallar magriba taci abinci tukunna. Koda ta koma gida ta tarar Baba bai dawo daga masallaci ba kasancewar idan ya fita sallar magriba baya dawowa gida sai yayi isha. Tana shigowa gida ana yin kiran sallar isha don haka ko zama ba tayi ba dauki buta tayi alwala sanna ta gabatar da sallah.
Tana zaune akan sallaya taji shigiwar Baba. Bayan kamar mintuna biyar da shigarshi dakinshi ne ta tashi ta bishi. Da sallama ta shiga dakin sannan ta zauna akan tabarma. "Sannu Baba ina yini" tace tana mai russunawa. "Lafiya lau Aisha, kinzo lafiya" "lafiya lau Baba". "Madalla, ya wajensu Alhaji Jafarun dasu Hajiya duk suna lafiya dai ko?" tace "duk lafiyarsu lau sunce a gaisheku" yace "Masha Allahu, to ya karatunnanki babu dai wata matsala ko".
Tace "Alhamdulillahi, ai Baba harna gama ma" yace "to Masha Allahu, Allah ya bada sa'a. Sai batun aure kenan ko tunda Allah yasa kin gama karatu". Shiru tayi tare da sunkuyar da kai. "Ya kika yi shiru Aisha, ko har yanzu mijin bai samu ba" cikin sanyin murya tace "kayi hakuri Baba".
Shiru ne ya ratsa na wasu 'yan mintuna zuwa can Baba yace "kina jina ko Aishatu, ni da kike ganina bazan yi miki dole ba hakanan kuma bazan zuba miki idanu kiyi ta zama babu aure ba don haka idan har kinsan akwai wanda kika tsayar kiyi gaggawar turoshi idan kuma babu to ki tabbatar da kin samu zaki gabatar dashi dimin kuwa har ga Allah zamannan naki a haka ba sonshi nakeyi ba".
Tace "In Sha Allahu Baba bazan baka kunya ba". Daga haka suka shiga hirar duniya. Bata bar dakin Baba ba sai kusan karfe sha daya. Dakin Goggo ta shiga tayi shirin kwanciya sannan ta kwanta.
Tunda ta fita da safe yawon gaishe-gaishe bata dawo gida ba sai gaf da sallar magriba. Sosai take cikin gajiya. Ko don ta dade ba tayi yawo irin haka ba gaba daya sai taji jikinta yana mata ciwo.
A ranar da ta kwana biyu da zuwa gida wurin karfe sha biyu na rana suna zaune da Goggi, gyaran zogalen da Goggo zatayi dambu takeyi. Yarone ya shigo yace wai ana sallama da ita. Mamaki ne ya kamata, waye kuwa zaiyi sallama da ita da safennan. Ita wa ma ta sani da har za'azo wurinta.
Ganin bata da niyyar amsawa ne yasa Goggo tacewa yaron kace tana zuwa sanna ta cewa Aisha "tashi kije ki ga waye, ai ba'a san inda za'a dace ba". Kasancewar tayi wanka tun tashinta, sanye take cikin atamfar Holland dinkin riga da zani. Hijabi kawai ta saka ta fita don ganin mai sallama da ita.
Mallam Adamu ta gani zaune cikin mota. Cikin sassarfa ta karasa wajenshi, tana zuwa ki gaishe shi batayi ba ta tambayeshi lafiya. Murmushi yayi sannan yace "lafiya lau Mami ce tace nazo na daukeki" "Mami fa kace kuma lafiya Mallam Adamu ka tabbata" ta tambayeshi fuskarta dauke da mamakin jin cewar Mami tace a zo a dauketa ganin sun rabu ne akan zatayi sati daya kafin ta koma. Yace "lafiya lau kawai dai tace ne nazo na daukeki". To ina zuwa tace mishi sannan ta juya zuwa cikin gidan.
Sanarwa da Goggo tayi batun tafiyarta. Itama Goggo tarrarrabi takeyi cewa anya kuwa lafiya. Daki Aisha ta shiga ta hada kayanta sannan ta fito tayi sallam da Goggo tana cewa ta fadawa Babanta batun tafiyarta idan ya dawo. A sosron gidan sukayi kacibis da Baba, kafin tayi Mayans ya rigata da cewa "naga Mallam Adamu yazo daukarki ko, Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutanen gidan. Tace "amin Baba fatana dai Allah yasa lafiya" yace "lafiya lau kawai dai bata ji dadi bane Mamun taku amma yace jikin da sauki".
Sallam Ragusa Baba sannan ta wuce mota suka dauki hanyar kano. Hakanan taji gabanta na faduwa don haka ta fiddo da AlQur'ani daga jakarta tana karantawa. Sai da suka isa kano sannan ta rufe AlQur'anin ta mayar cikin jaka.
Suna shiga layin gidansu taga cincirondon motoci a kofar gidansu. Mummunar faduwar gaba ce ta sameta, cikin rawar murya tace "Mallam Adamu me je faruwa ne, don Allah ka gaya mini". Cikin dakewa Mallam Adamu yace mata "sai dai muyi hakuri Aisha Hajiya Mami Allah yayi mata rasuwa jiya da darea sanadiyar ciwon ciki".
Sandarewa kawai Aisha tayi a zaunen da take ta rasa gane ne kunnuwanta suka jiye mata. Wani irin kuka ne yazo mata, kifa kanta kawai tayi akan cinyoyinta tana kuka. Mami wai Maminta ce ta rasu. Mamin data tafi ta bari cikin koshin lafiya ashe bazata dawo ta tarar da ita ba. Wannan rayuwar abar tsoro ce, wato tsakanin rayuwa da mutuwa dan takin kalilan ne ( Allah yasa muyi kyakkyawan karshe, Amin).
Ta dade a zaune cikin motar kafin tayi karfin halin fitowa, gidan a cike yake da mutane 'yan karbar gaisuwa. Ta kofar kitchen tabi ta shiga cikin gidan. A parlour ta tarar dasu Hajiya da Hajiyarsu Mami da wasu daga cikin 'yanuwanta. Durkushewa tayi kawai a wurin tana wani irin kuka, mutanen wurin gaba daya suka hau bata hakuri.
Da kyar ta iya tsaida kukan tayiwa su Hajiya gaisuwa sannan ta tashi ta haya sama zuwa dakinsu. Su Ummie ne a dakin tare da kawayensu. Tana shiga Ummie ta taso ta rungumeta tare da fashewa da kuka, itama Aisha kukan takeyi.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
13
Mutuwar Mami ba karamin girgiza al'ummar gidan tayi ba tun daga kan maigidan zuwa yaran gidan da ma'aikatan gidan gaba daya. Ga Aisha kam ko mutuwar mahaifiyarta bata shigeta haka ba ko don lokacin da mahaifiyarta ta rasu bata mallaki hankalinta kanta ba.
A cikin kwanaki bakwai da akayi ana karbar gaisuwa sunga tururuwar jama'a 'yan zuwa ta'aziyya. Kodayake Mami ta mutane ce, fata dai a koyaushe shine halinta na gari ya bita.
A bangaren Aisha ma Babanta da Goggo da Yaya Huwaila ne suka zo musu ta'aziyya don Goggo ma da Yaya Huwaila zama sukayi har saida akayi sadakar uku sannan suka koma.
Bayan anyi sadakar bakwai ne kowa ya watse sai suka ji gidan yayi musu fadi. A wannan lokacin ji sukayi mutiwar ta dawo musu sabuwa tamkar a lokacin akayi ta.
Sauki daya da suka samu shine da Hajiya bata koma gidanta ba taci gaba da zama dasu to sai dai suma sun sani zamanta dasu ba mai daurewa bane.
A ranar da Mami tayi kwana ashirin da hudu da rasuwa ne Aisha na tare da Hajiya a dakin da Hajiyan ta sauka. Man zafi take shafa mata a kafafunta kasancewar tana fama da larurar ciwon kafa.
Daddy ne yayi sallama ya shigi ckin dakin. Amsa mishi Aisha tayi sannan ta gaisheshi ta tashi ta fita. Zama yayi a kasa ya jingina da jikin gadon sannan yace "Hajiya barka da dare an yini lafiya" "lafiya lau Alhamdulillahi" Hajiya ta amsa mishi "ya hidimomi, yanzu ka dawo hala?"
Yace "eh Hajiya komai lafiya lau mun gode Allah. Ya kafartaki, tana matsa miki ne har yanzu ko sai kun koma asibiti". Lankwashe kafafuwan tayi tace "a'a basa mini wani ciwo ai naji dadin maganin da aka canja mini a asibitin, sai dai dama akwai maganar da nakeso muyi".
Gaba daya ya tattara nutsuwarshi zuwa ga Hajiya don daga yanayin yadda ta mishi magana yasan maganar da zata fada mai muhimmanci ce sosai.
"Kana jiko dama akan maganar yarinyar nan ne Aisha, da iyayenta suka zo gaisuwa mahaifinta ya bukaci da ta koma gabanshi tunda ta gama karatu gashi uwar rikonta Allah yayi mata rasuwa. Ta na dai ce mishi ya dakaceni kadan In Sha Allahu zan nemeshi akan maganar".
Ta dan numfasa sannan ta cigaba da cewa " ni ina ganin mai zai hana ka aureta ta maye maka gurbin Zainab ko babu komai kasanta kasan halinta tunda tarbiyyarkuce kuma zata zamewa 'ya'yanka uwa tunda akwai shakuwa sosai a tsakaninsu, bama dai Ruqaiya da Zainab don sunfi sauran bukatar uwa amma kasancewar su da Aisha maraicin da zasuyi kalilan ne".
Tunda Hajiya ta ambata mishi aure yaji wata iriyar zufa ta keto mishi hankalinshi ya tashi yawun bakinshi gaba daya ya kafe ya rasa mai zaicewa Hajiya. Da kyar ya samu ya tattaro dauriya yace " Hajiya wani irin aure a yanzu kuma da yarinyar nan Aisha, ai 'yata ce kamata yayi ace ni zan aurar da ita ba wai ni na aureta ba".
Tsuke fuska Hajiya tayi ta bata rai sannan cikin kausashiyar murya tace "wace irin magana ce kakeyi haka, haram ne auren Aishar ko menene, kuma da kake maganar aure yanzu wuri yayi maka ko me. Idan bakayi aure yanzu ba sai yaushe zakayi. Kasan dai ni bazan cigaba da zama maka a gida don na kula maka da yaraba dole suna bukatar uwa bama dai kananun kuma a ganinka akwai wacce tafi dacewa da zame musu uwa fiye da Aisha ne. Yarinyar da tun haihuwarsu take faman hidima dasu. Kuma ni nayi maka sha'awar aurenta ne saboda yarinyar mutuniyar kirki ce sosai zakaji dadin zama da ita don bata da raini kwatakwata bata da rawar kai irin ta 'yanmatan yanzu. Amma bazan tursasaka akan abin da bakayi niyya ba tunda bakaso shikenan fatana Allah ya hadaka da abokiyar rayuwa ta gari, Allah ya jikan Zainab"
Tunda ya sunkuyar da kanshi ya kasa dagowa don gaba daya sai yaji mutuwar Zainab ta dawo mishi sabuwa, rashin Zainab da yayi ne yasa har Hajiya keyi mishi maganar aure a cikin kasa da kwana da talatin da mutuwarta kuma auren ma da karamar yarinya 'yar cikinshi da bata wuce sa'ar Mu'azzam ba danshi na biyu bama Khalifa ba.
Tunda ya mallaki hankalin kanshi bazai iya tuna wata rana da yayiwa Hajiya musu akan wata bukatarta ba don haka bazai fara daga yanzu ba.
Aure tace tana so yayi to In Sha Allahu zaiyi da kuma yarinyar da takeso. Kamar yadda tace ne yaranshi sunyi sabo da yarinyar sosai, sai dai har cikin ranshi yasan zaiyi auren nan ne kawai don farin cikin Hajiya bawai don yana ra'ayi ba, shikam matarshi daya ce Zainab babu wata diya mace da zata iya maye mishi gurbinta.
Dauke kai Hajiya tayi tayi tamkar bata san da dashi a zaune ba. Ta san har ga Allah bada wani abu tace yayi aure ba sai don sanin cewa auren ne zai sama mishi nutsuwa ya dauke mishi damuwar da yake ciki ta rashin Zainab.
Kuma da tace ya auri Aisha tasan itace kawai zata iya hakurin zama da yaranshi tunda ba yau suka fara zama tare ba amma mawuyacin abu ne yayi dace da matar kwarai da zata kula mishi da yara tsakaninta da Allah bare da ya kasance mai ido ne shi akan harkar yaranshi ba kiwacce mace bace zata iyayin hakuri da halinsu ba amma Aisha fa tasan halinsu ta kuma iya zama dasu tunda duk tsawon zamanta dasu ba'a taba jin kansu ba ta kuma dade da sanin cewa ba dadin zama dasu take jiba tun ma ba Farida ba da Mu'azzam dama kuma sune fitinannun.
Ganin shirun bazata kai msihi ko ina ba nevya sashu amsawa Hajiya da bukatarta. Farin ciki ne ya lullube Hajiya sosai, dama dai tasan da wuya ya tsallake maganarta ko da kuwa baya so. "In Sha Allah sai kayi alfahari da auren Aisha don kuwa yarinyar arziki ce ita, Allah yayi maka albarka yasa 'ya'yanka suyi bika fiye da yadda kake bina".
UMMASGHAR
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
14
Babu bata lokaci Hajiya ta nemi Baban Aisha da maganar auren da take son kullawa tsakanin Daddy da Aisha inda anan take ya amince da shawarar Hajiya don dama zaman Aisha a haka babu aure ba dadi yakeyi mishi ba.
Ba wani dogon lokaci aka yanke wa auren ba, sati uku kawai aka saka zai kama bayan anyi arbain din Mami da sati daya kenan. Za'a daura auren acan gaya sai a dauko amarya daga can.
Ita kam Aisha bata san wainar da ake toyawa ba har sai da ya rage saura kwanaki goma daurin auren sannan Hajiya ta sanar da ita.
A razane ta dago ta kalli Hajiya da kwata-kwata bata lura da halin da takevciki ba ta cigaba da yi mata nasiha akan hakuri da karbar kaddara aduk yanda tazi mata.
Sai dai sam Aisha bata san me take cemata ba don gaba daya kwakwalwarta daina aiki tayi na wucin gadi, bata san cewar hawaye takeyi ba sai da taji Hajiya ta tabata sannan taji danshin hawayen a fuskarta.
"Kuka kikeyi Aisha, bakiyi na'am da maganata bane yasa kike kuka? Idan kina ganin akwai damuwa sai a fasa don bazanso inyi abinda zan cutar dake ba domin kuwa ke din amana ce a wurina. Ni dama nayi sha'awar kasancewarki madadin Maminku ne saboda kyawawan halayenki da nagartarki zanso ace kin kasance tare da Jafaru ki zame mishi mace ta gari uwa ga 'ya'yanshi don nasan ke kadai zai aura da 'ya'yanshi bazasuyi maraicin uwa ba".
Cikin sheshekar kuka tace "kiyi hakuri Hajiya bawai ina kuka don banyi na'am da maganarki bane sai don ina ganin idan akayi haka tamkar naci amanar Mami ne data rike ni da zuciya daya tamkar 'yar data haifa, tsawon zaman da ita bata taba bambantani da yaranta ba.
Amma ya za'ayi na kasa bin umurninki bayan dukkan abin da kikayi mini a rayuwata komai zan zama a rayuwa kece sila ya kuwa za'ayi na kasa yin abinda kikeso.
In Sha Allahu zaki sameni mai yin biyayya ga dukkan umurninki matsawar bai sabawa Allah b, Allah ya tabbatar mana da abinda yafi alkahiri".
Sosai farinciki ya lullube Hajiya cewa takeyi "nagode Aisha In Sha Allahu alkhairi na tattare da rayuwarki, Allah yayi miki albarka ya azurtaki da zuri'a ta gari".
Har lokacin shocj bai saketa ba abin daure mata kai yakeyi yadda Hajiya tayi yunanin hada wannan auren sai dai bata bari Hajiya ta gane tana cikin damuwa ba tayi kokarin ganin ta saki fuskarta, sai dai bata iya cigaba da zama a dakin ba sallama tayiwa Hajiya ta koma dakinsu.
Tana shiga dakin toilet ta wuce ta rufe kanta a ciki ta fashe da kukan tausayin kanta. Ita kuma tata kaddarar kenan ta auren mutimin da yayi 'ya da ita. Ta jima cikin bandakin sai da taji ana knocking sannan ta wanke fuskarta ta bude kofar ta fita.
Farida ce a tsaye a bakin kofar. Tsaki ta mata sannan tace "wani sabon salo ne wannan ki shige bandaki ki rufe kinaji ana knocking kinyi banza da mutane".
Ko kallon Farida batayi ba ta wuce ta hau kan gado ta kwanta. Tunda taji maganar aurenta da Daddy ta koma wata sukuku da ita gaba daya ta rasa walwalarta. Kullum Ummie cikin tambayarta abin da ke damunta take amma amsa daya take bata itace babu komai.
Yaya Khalifa ma saida ya kirata yayi mata nasiha akan rashin walwalarta don a tunaninshi mutuwar Mami ce har lokacin ke nukurkusarta sai kawai ta bishi akan haka dinne.
Bata san a wurin wa su Ummie sukaji maganar ba a lokacin saura kwana shida durin auren. Farida da Ummie ne suka shiga dakin suka sameta tana shirya musu kaya a cikin wardrobe. Ummie ce tace mata "Aisha wacce magana naji anayi a cikin gidannan akanki da Daddy?"
Gabanta ne taji ya fadi jin maganar data fito daga bakin Ummie. Daurewa tayi ta amsa mata da "wacce magana kenan kikaji". Wani wulakantaccen kallo tayi mata sannan tace "kina nufin kice bakida masaniya akan batun aurenki da Daddy". Shiru Aisha tayi don bata san amsar da zata bata ba.
Shirun da Ummie taji tayi mata ne ya bata tabbacin cewa maganar da taji ba karya bace kenan da gaske ne Daddynsu Aisha zai aura, wannan wane irin cin amana ne Aisha tayi musu ta rasa mijin aure sai mahaifinsu.
Shi yasa dai mutane ba abin yarda bane, da uta ce maijin haushin yanda Farida ke treating dinta ashe dai akwai abin da Farida ta hango da yasa ta kasa yarda da ita.
Zamewa Ummie tayi ta zauna a kasa don ji tayi kafafunta baza su iya daukarta ba jikinta gaba daya rawa yakeyi.
"Mtsew... ni dama na dade da danin crwa wannan mai kama da bararon zamanta a gidannan ba alkhairi bane, kune dama kuka daukaketa kuka maidata wata tsiya. Na kuma tabbata ita tayi kulle-kullen da har Hajiya tayi tunanin hada aure tsakaninta da Daddy. To wallahi tun wuri kije ki kwance kullin da kikayi wa Hajiya don bazamu taba aminta dake a matsayin matar Daddynmu ba".
Haka suka saka Aisha gaba sunata yarfa mata rashin mutunci amma har sukayi suka gama bata daga kai ta kallesu ba. Ta sani cewa dolene ta aro hakuru ta kara akan nata don wulakancin da zata gani a wurinsu ba kadan bane.
Ko kadan kuma abin da sukayi mata bai bata mata rai ba don tasan dolene suji babu dadi akan sabon matsayinta a wurinsu itama ba dadin take ji ba don dai babu yadda zata yi ne to amma ya kamata su fahimci cewar itama ba yin kanta bane kuma komai yana tafiya ne akan kaddararshi.
Idan har Allah ya kaddara mata auren Daddy bata da yanda zatayi ta guje mishi hakanan idan har babu shi a cikin kaddararta babu abin da zaisa aurensu ya kasance.
Tun daga wannan ranar Aisha ta koma mujiya a cikin yaran gidan. Ko bi ta inda suke batayi don hatta da Yaya Khalifa da Mu'azzam sun daina amsa gaisuwarta. Ruqaiya da Zainab ne kawai basu canja mata ba watakila kuma don su din yara ne basu fahimci me ke faruwa ba.
Ana saura kwana biyu daurin auren ne Hajiya tace ta shirya Mallam Adamu ya kaita gida. Duk da ba taron biki zasuyi ba anan amma tasan acan 'yanuwanta baza su kasa yin yinin biki ba.
Bata debi wasu kaya ba sai kayan data ware zata bayar. Koda tayiwa su Ummie sallama ba wacce ta kalleta a cikinsu.
Ta iske gidansu a cike da mutane, su kam hidimar biki sosai sukeyi. Tana shuga aka fara mata guda ana ga amaryara ta iso. Ita dai yake kawai takeyi.
Dakin Goggo ta shiga gaba daya jikinta yayi sanyi. Sai yanzu data ga mutane a gidan ta kara yarda bikinta akeyi. Har ga Allah baso aurennan takeyi ba to amma bata da yanda zatayi, bazata iya cewa Hajiya bata son danta ba bayan dukkan abinda ta mata ga kuma Babanta da bayada wani buri bayaga na ganin aurenta.
An daura auren Ja'afara Bello Danmaliki wato Daddy da Aisha ranara asabar da misalin karfe biyu da rabi anan kofar gidansu dake garin gaya. A bangaren ango dai ba wasu mutane bane da yawa suka halarta don bazasu wuc mutum goma ba har shi angon.
An shirya nr akan cewa da an gama daurin aure za'a wuce da amarya. Mutum biyu ne aka shirya zasu raka Aisha gidanta duba da yanayin da bikin yazo musu.
Sosai Babanta yayi mata nasiha ya nuna mata cewa kyakkyawan halinta da nagartarya ne suka saka Hajiya yin sha'awar hadata aure da danta don haka yana so ta cigaba da portraying kyakkyawar dabi'arta ta rike yaran mijinta da amana.
An fito da ita tana kuka sosai don har yanzu ta kasa yardarwa kanta wai itace aka daurawa aure da Daddy. An sakata a motar da dama don tafiya da ita aka zo tare da 'yan rakiyarta.
Sun shiga gidan ana kiran sallar magriba. Ita dai banda faduwa babu abinda gabanta keyi. Tana lullube a cikin mayafi aka shiga da ita cikin gidan.
Gidan shiru babu kowa sai Hajiya da suka tarar a parlour. Ita tayi musu jagora zuwa dakin Aisha dake a sama. Bayan fitarta ne su Yaya Huwaila da Yakumbo Dije ( kanwar Babanta) da suka kasance 'yan rakiyarta suka fara haramar yin sallah.
Yakumbo Dijevce tacewa Aisha ta tashi tayi sallah. Sai a lokacin Aisha ta bude idonta, dakin tabi da kallo. Dakin da Mami take saukar bakinta ne sai dai an canja kayan ciki. Gado ne da wardrobe da madubi kirar italy.
Dama Babanta ya fada mata cewa Hajiya tace ita zatayi mata kayan daki, da gani babu tambaya don tasan Babanta bazai iyayi mata irin wannan kayan ba.
CIGABAN LABARI
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
15
Tsaye take a kitchen tana shirya abincin dare. Tuwon semovita takeyi da miyar kuka. Ta gama tuka tuwon ta kwashe a cikin warmer ta kada miyar kenan Farida ta shigo kitchen din hannunta rike da farar roba irin wadda ake zuba yaji, tukunyar miyar ta bude ta juye abinda ke cikin robar.
Kallonta kawai Aisha ta tsaya yi tana mamakin irin wannan hali na Farida. Ganin zata fita daga kitchen dinne yasa ta mata magana tace "miye wannan kika zuba mini a miya Farida?" Murmushi ta saki wanda da an gani an san na mugunta ne tace "oh wannan, wani spice ne da zai karawa miyarki dandano, shinshina robar kiji" ta tura mata robar hancinta tana dariya.
Cikin takaici Aisha tace "wai lalle nebkika zuba mini a girki Farida". Dariyar shakiyanci tayi sannan ta juya ta bar kitchen din. Tsabar takaici Aisha ji tayi kamar tayi kuka.
Wulakancin Farida ya fara isarta, idan banda wulakanci ya za'ayi ta zuba mata lalle a cikin abinci da gangan. A yau dai kam bazata kyaleta ba don ta lura shirun da takeyi musu ne yasa suke yi mata abinda suka ga dama.
A yau dai kam sai taji dalilin irin wannan cin kashi da suke mata. Kashe cooker din tayi ta nufi parlour don taji dalilin Farida nayi mata abinda tayi.
Turus tayi ganin Daddy tare da duka yaran a cikin parlour din. Bata san cewa ya dawo gidan ba. Sannu da zuwa tace mishi a yayin da take karasawa cikin parlour. A takaice ya amsa mata da yauwa ba tare da ya dago ya kalleta ba.
Komawa tayi kitchen ta hado ruwa da kemo ta dora akan tray hadevda cups ta kawo mishi. Sida stool ta janyo gabanshi ta dora tray din akai tare da tsiyaya mishi ruwan a cup. Tana dagowa taga yaran duka na banko mata harara.
Dauke kanta tayi ta samu wuri ta zauna cikin sanyin jiki. Tana jinsu suna hira shi da yaranshi tamkar babu ita a wutin haka sukayi mata. Dama kuma idan da sabo yaci ace ta saba don idan suna wuri tazo ta zauna yi sukeyi tamkar basu san da zamanta ba.
Cikin muryar shagawaba Farida tace "Daddy me ka sayo mana ne tun dazu nake hararar ledojin daka shigo dasu", gaba daya suka saka dariya. Mu'azzam yace "eh wallahi nima dai hankalina yana kan ledojinnan". Murmushi yayi jin abinda suke cewa, mika musu kayan yayi yace gashinan kowa daya. Ga matan dai laces ne ya saya musu mazan kuma voile.
Gaba daya suka hau murna hade da yi mishi godiya. Duk da kyautar da aka musu idanun Farida na kan ledar dake aje a gefe. Cewa tayi "Daddy wannan kuma fa ko naka ne" a yayin da take daga ledar don taga abinda ke ciki.
Laces ne a ciki guda biyu sai dai da gani a idon ansan babu tambaya yafi wanda ya basu kyau da tsada. "Daddy nidai wannan nake so don yafi wancan kyau ko kuma ka hada mana gaba daya kawai". "Ajiye Farida wannan na Auntynku ne" yace mata.
Wani banzan kallo ta watsawa Aisha sannan tace "please Daddy wallahi tunda naga wadannan naji sun shiga raina don Allah" cikin murya irinta shagwababbun yara tayi maganar.
To shikenan ku dauka ita sai a saya mata wani" yace a lokacin da ya mike don hawa sama. Ihun murna Farida ta saka suka tafa da Ummie suna murna.
Ummie tace "amma gaskiya Farida kin burgeni ni ai bazan iya abinda kikayi ba, ko da yake dama ke Daddy's pet ce he never says no to you shi yasa kikeyin abinda kika ga dama".
Ta wani kada idanunta ta juyasu sannan tace "ato da ni din ta wasa ce, ai wallahi yarinya kadan ma ta gani idan dai nice. Ita har ta isa ta saka wannan lace din shima Daddy da taya bera bari. Ban gaya muku na kara mata maggi da gishiri a cikin miyarta bako, ai yau zakuci delicious".
Sai a likacin Aisha ta tuna da abinda Farida ta mata. Tashi tayi ta koma kitchen din don ta hada wata miyar tunda dai waccan ta lalace bazata ciwu ba. Tana jin Farida na gaya musu ai lalle ta zuba mata a cikin miya suna dariya.
A ranar wata asabar da dare ne suna zaune gaba dayansu a parlour suna kallo. Ita dai Aisha homework taje koyawa Zainab. Daddy ne ya shigo da sallama. Dukansu suka amsa suna mishi barka da shigowa. Ledar dake hannunshi ya ajiye akan center table yace yana mai kallon Aisha "ga nan nama" "mun gode Allah ya saka da alkhairi" tace mishi.
Bai zauna ba sama kawai wuce. Yana hayawa Farida tayi zirif ta dauke ledar naman ta nufi kitchen, tashi Ummie tayi tabi bayanta. Kwalowa Ruqaiya kira sukayi, tashi tayi taje amsa kiran da sukayi mata.
Sai gata ta dawo da plates guda biyu a hannunta ta mikawa Yaya Khalifa da Mu'azzam sannan ta koma ta dauko nasu ita da Zainab. Tare suka fito dasu Ummie suma da nasu plate din a hannu.
Wato kenan su sukayi rabon naman ta kuma tabbata basuyi rabon da ita ba. Ko kallonsu batayi ba ta tashi taje ta hada kayan abincin Daddy ta nufi sama don bata tsammanin zai kuma saukowa.
Bata sameshi a parlour ba don haka ta wuce cikin dakin. A kwance'akan gado ta iske shi. "Daddy ga abincinka" tace mishi a lokacin da take ajiye tray din a kasa. Tashi yayi zaue sannan yace "kinga kwashe abincinnan ki kawo mini tea kawai sai ki hado mini da naman".
Tsaye tayi a wurin ta kasa gaba ta kasa baya ta kuma kasa gaya mishi cewa babu naman ya kare. Cikin daga murya yace "kinyi mini tsaye a ka bazaki kawo mini bane ko me"?
Cikin fargabar abinda zaice tace mishi "babu naman ne ya kare". "Ban gane da babu ya kare ba, kina nufin gaba daya kuka cinye ba tare da kin dibar mini ba. Ke wacce irin yarinya ce kwata-kwata bakida common sense baki san abinda ya dace ba".
Ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, fada kawai yakeyi kamar dama irin kiris dinnan yake jira. Sai da ya gaji don kanshi sannan yayi shiru. Hakuri kawai ta bashi ta sunkuya ta debi kwanukanta ta fita daga dakin.
Ajiye kayan tayi ta bude freezer ta fito da naman rago ta yankashi sirarata wanke ta dora a wuta. Sannan ta fito da dakakken kuli-kuli da tomatoes da attaruhu da albasa ta gyara. Tsiren tukunya ta hada mishi sannan ta dafa tea ta zuba a flask ta shirya cikin tray tana jiran naman ya karasa ta sauke.
Koda ta duba taga ya nuna sai ta sauke ta zuba a cikin bowl ta hada akan tray din. Tana cikin wanke tukunyar da tayi amfani da ne taji muryar Ummie a bayanta tana cewa "Farida gane mini ikon Allah, wai matarnan nama tazo ta gasa don bata samu taci wanda Daddy ya kawo ba.
Farida ce ta karaso kitchen din tace "ai kinsan duk wanda bai taso cikin arziki ba idan ya sameshi daga baya cin kwan makauniya yakeyi mishi". Hannunta ta kai zata dauki naman, Aisha tayi caraf ta rike hannun tace "wannan ne kuma baki isa ba, kun rabe wancan a tsakaninku kun cinye ban tanka muku ba ba kuma zakuzi kuce zakuci wannan ba. Duk wacce take so ta bude fridge ta dauka ta dafa amma ba wannan ba".
"Samun wuri, ke nan har kin isa muna son abu kice baza mu dauka. Naga dai ubanmu ne ya sayi kayan ba na wani ba" cewar Ummie kenan. Aisha dai ta kankane namanta ta hanasu tabawa tacec"kome zakuce ku fada nama ne dai bazaku taba mini ba".
Suna cikin hayaniya ne suka ji gyaran muryar Daddy. Gaba daya sai suka shiga taitayinsu don fuskarshi sam babu annuri. "Lafiya kuke mini hayaniya a gida da darennan, ke kuma bazaki kawo mini tea din bane" yace yana maida kallonshi ga Aisha. "Kayi hakuri yanzu zan kawo" tace tana mai daukar tray din.
Ya juya zai bar kitchen din kenan Farida tace"Daddy kaga wai nama muka gani muna so wai bazata nbau ba". Juyowa yayi ya kalleta yace "nama wane iri ba kince babu ba kun cinye". Cikin muryarta mai sanyi tace "eh wancan babu wani ne nayi maka dama".
Yace "kuma shine bazaki basu ba alhalin suna so, to a wanne dalilin. Ku dauka kuje kuci ni bana ci" yace wa su Farida. Bayan ya fita daga kitchen dinne suka kyalkyale da dariya Ummie tace "wayaga cusa kai babu kwarjini".
Ajiye musu bowl din naman tayi ta wuce ta kai mishi kayan tea din ranta a matukar bace. Don takaici a daren har kuka sai da tayi.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
16
A safiyar litinin ne bayan ta gama shirya su Zainab ta hada musu abincin break ta sallamesu zuwa school. Nasu breakfast din ta shirya a table sannan ta wuce zuwa dakinta ta yi wanka ta shirya a cikin doguwar rigar material, bata daura dankwali ba sai siririn gyale data yafa a kanta. Turaren ladies ta fesa a jikinta sannan ta fita zuwa dakin Daddy.
Da sallama a bakinta ta shiga dakin. Yana tsaye a gaban wardrobe yana fito da kaya yana ajiyewa a kan gado. A bakin gadon ta zauna bayan ta gaisheshi. Trolley ya dauko ya ajiye sannan yace mata "shirya mini kayannan tafiya ta kamani zuwa abuja zanyi kwana hudu, bari na shiga wanka". Tashi tayi ta shirya mishi kayan daya fitar cikin akwatin sannan ta hau gyaran dakin.
Bayan ta gama ne ta koma parlournshi na nan sama ta zauna, tv ta kunna ta kai tashar mbc2. Bawai kallon takeyi ba sai dai zaman shirun ne ya isheta. Tayi kusan mintu talatin a zaune kafin ya fito. Tashi tayi ta karbi akwatin hannunshi sannan tabi bayanshi suka sauka kasa. Ajiye akwatin tayi a gefe sannan suka nufi table don yin breakfast.
Kasancewar su Ummie suna hutu yasan suna can suna bacci ba da wuri za suyi breakfast ba yasa daga ita sai shi ne a table din. Sau tari tafi sakewa a irin wadannan lokutan da daga ita sai shi ba tare dasu Ummie ba don sukam idan suna wuri sai sunyi sanadin da Daddy ya bata mata rai.
Bayan sun gama breakfast dinne ya mika mata kudi wrpper 'yan dari biyar wato dubu hamsin kenan. Mikewa yayi yana mata sallama akan cewa sai ranar juma'a zai dawo. Har wurin mota ta raka shi tana dauke trolley din, sai bayan taga tafiyarsu ne sannan ta koma gida.
Colonel Ja'afar Danmaliki na kwance akan gadon dakin hotel din da yayi masauki a garin abuja a daren daya samu kwanaki biyu da barin gidanshi. Mamakin kanshi kawai yakeyi yanda tun barinshi kano ya kasance cikin kewar yarinyar.
Bai taba tunanin cewa zaiso wata diya mace a bayan Zainab ba sai gashi yanzu ba tare da yasan lokacin da hakan ya faru ba ya samu kanshi cikin soyayyar 'yar karamar matar tashi.
Yasan harda hakurinta da sanyin halinta wajen taimakawa wurin assasa mishi soyayyarta a zuciyarshi. Muryarta kawai yake so yaji ko zai samu nutsuwa sai dai kuma abin haushin shine ko numberta baya dashi.
To ko a wurin Khalifa zai nem number nata idan yaso sai ya fake da kira don jin lafiyarsu yaji muryarta. Kai a'a da kunya gaskiya ya nemi numberta wurin Khalifa sai dai ko a wurin Hajiya.
Kai yasan abu ne ma da bazai yiwu ba ya nemi numberta a wurin Hajiya idan dai baso yake ya bata mata rai ba. Kawai dai hakuri zaiyi har ya koma gida ai nan da kwan biyu ne babu wani dadewa. Sai dai kuma ganin kwanaki biyun yakeyi kamar watanni biyi koma shekaru don tsayi.
Ya dade a kwance yana juyi ba tare da ya iya yin bacci ba sai tunanin Aisha da ya sakashi a gaba. Da kyar bacci barawo ya lallabo ya saceahi, sai dai baccinnashi ma a cike yake da mafarkanta.
A safiyar alhamis ne Aisha ta tashi jikinta yayi matukar zafi zazzabi ya shigeta. Koda ta tashi ji tayi jiri yana dibanta, komawa tayi ta kwanta. Wayarta dake ajiye akan bedside drawer ta janyo ta kira Lami.
Ko mintuna biyar ba'a rufa ba Lami ta hayo, daga bakin kofa ta tsaya tana sallama. "Shigo Lami" Aisha tace bayan ta amsa mata sallamar. Karasowa ciki tayi sannan ta gaida Aisha.
Bayan sun gama gaisawa ne tace mata ta hadawa su Ruqaiya abincin makaranta sai kuma ta shirya breakfast saboda bata jin dadi bazata iya tashi ba.
Komawa tayi ta kwanta bayan fitar Lami daga dakin. Tana cikin bacci taji an yaye quilt din data rufa a jikinta. Koda ta bude ido Farida ta gani a tsaye a kanta tana huci. "Lafiya" shine abinda tace mata.
Cikin daga murya tacev"eh kin tambayi lafiya mana tunda kin samu wuri har kin nade akan gado kina bacci, idan banda kin samu wuri Lami zaki saka tayi mana abinci. Kevtunda kike a gidannan kin taba gani munci girkin 'yan aiki. To wallahi tun wuri gara ki tashi ki girka mana abinda zamuci idan ba haka ba na sanarwa Daddy".
Quilt dinta kawai taja ta rufa sannan tana daga ciki tace mata "idan kun ga bakwa son na Lamin sai ku shiga kitchen din ku girka amma ni yau bazan iya saukowa ba don kuwa bani da lafiya. Idan kin fita kija mini kofar".
Mamaki ne ya kama Farida don kuwa bata taba zaton Aisha zata iya maida mata martani ba. A nata tunanin shirun da Aishan keyi mata ta dauka tsoronta takeji bata san cewar tsabar rashin son fitina ne yasa take kyaleta.
Cikin sanyin jiki ta fita daga dakin. Dole hakanan abincin Lamin suka ci tundaha na safen har na rana dana dare. Da daren ne Farida ta dauki waya ta kira Daddy don ta kai mishi karar Aisha.
Yana daga wayar ko gaisheshi batayi ba ta fara mishi korafi tana cewa "Daddy karar matarnan na kawo maka yau throughout bata bamu abinci ba sai Lami ce ta girka mana kuma munyi mata magana tace idan baza muci ba mu barshi wai ita ta daina girka mana abinci".
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "jinan Farida, hakanan Aisha bazata hanaku abinci ba ko dai akwai abinda kukayi mata, nasan halinku fa". Jin abinda abinda Daddy yace ne yasa ta fara matsar kwallar karya tana cewa "wallahi Daddy babu abinda mukayi mata kawai dai bata ga damar yin girkin bane kuma fa dama Daddy kaine bakasan halinta ba amma ba kirki ne da ita ba".
Har cikin ranshi yaji baiji dadin kalamin Farida akan Aisha ba. Hakuri kawai ya bata yace idan ya dawo zai tsawatar mata.
Washegari ma Aisha a kwance ta yini a ranar ma kuma sai Lami ta saka tayi mata girkin gidan. Kasancewar a ranar Daddy zai dawo ne yasa ta daure ta tashi duk da jiri dake dibarta amma a haka ta shiga dakinshi ta gyara ta wanke toilet sannan ta jona turaren wuta a burner.
Dakinta ta koma tayi wanka ta shirya a cikin atamfa super holland kalar blue da ratsin yellow a jiki. Mai kawai ta shafa sai turare data fesa a jikinta ta sauka kasa. Tea ta hada tasha sannan ta fito da naman kaza ta wanke ta dora duk a kokarinta na hadawa Daddy abinci sai dai kuma dauriya kawai takeyi don tsayuwa ma neman gagararta takeyi.
Kamshin tafasar naman ne ya bugeta a take taji amai ya taso mata. Kafin tayi wani yunkuri aman ya taho gaba daya. Anan wurin ta durkushe ta hau sheka amai. Lami dake wanke-wanke a sink ta taho da sauri ta riketa tana mata sannu.
Bayan ta gama aman ne ta kuskure bakinta Lami ta kamata ta maidata daki sannan ta koma ta gyara wurin. Komawa tayi dakin ta tambayeta me take da niyyar dafawa taje ta girka. Cewa tayi kawai tayi shinkafa da miya da salad. Sanin cewa ba lallai ne ya ci ba yasa tace tayi shinkafar don tasan baya cin abincin masu aiki.
Ya shigo gidan ne wajen karfe bakwai da rabi. Bai tarar da kowa ba a parlour kasa don haka ya wuce sama maybe kuma suna dakunansu. Dakinshi ya wuce, sai da yayi wanka yayi Sallah sannan ya fito don yaci abinci. Zuciyarshi fal da tunani Aisha yana mamakin abinda ya hana ta zuwa yi misgi sannu da zuwa. A take maganr da Farida tayi mishi jiya ta fado mishi a rai.
Baiyi wata-wata ba ya nufi dakinta don ganin lafiya. Tunda taje gidanshi a matsayin matarshi bai taba shiga dakinta ba sai yau. Tana kwance a kudundune cikin quilt. Da sallam a bakinshi ya shiga sai dai ganinta a kwance ta lulluba har kanta yasa bai san lokacin da ya karasa gaban gadon ba yana cewa "lafiya Aisha kika kudundune cikin bargo a zafinnan gashi ko fanka ko ac baki kunna ba".
Jin muryarshi ne yasa ta yaye rufarta bude idonta da suka kada suka yi jawur. Tsikar jikinshi ce yaji ta tashi hada idon da sukayi. Zama yayi a bakin gadon sannanyace "baki da lafiya ne, tun yaushe ne bakida lafiya" ya tambayeta yana mai kai hannu jikinta.
Da sauri ya janye hannunshi jin yadda jikinta yayi zafi. "Bari na canja kaya sai muje asibiti" yace a yayin da ya mike daga kan gadon. Baifi minti biyar da fita ba ya dawo yana sanye da shadda getzner kalar light brown dinkin tazarce.
Bargon ya janye sannan ya saka hannu ya dagota. Zaunar da ita yayi ya janyo hijabinta dake ajiye akan sallaya ya saka mata ya mika mata takalmi ta saka ya mikar da ita.
Tana rungume a jikinshi suka fita. Har sai da ya zaunar da ita a cikin mota sannan ya zagaya ya shiga ya tashi motar suka fice. Asibitin da suke da family folder suka je.
Ba wani bata lokaci suka sami ganin likita. Tambayr ta yayi abinda ke damunta tace mishi zazzabi ne sai jiri da take fama dashi sai kuma tashin zuciya. Test ya rubuta ta malaria da kuma ptegnancy test yace suje lab ayi yanzu su kawo mishi.
Bayan sunje sunyitest dinne sun kawo mishi result din ya duba yace "its as i suspected she's 12 wks pregnant sai dai kuma akwai malaria a jikinta. Wani irin farinciki ne ya ziyarci Daddy jin cewar zai samu Baby.
Gaba daya fuskarshi ta cika da annuri har mamaki ya dinga bawa Aisha don bata taba ganinshi a cikin farinciki kwatankwacin wannan ba. Bayan sun karbi magungunanta ne suka tashi suka tafi.
Motsi kadan idan Aisha tayi sai yayi mata sannu, mamakinshi ne kawai ya kamata don bata taba sanin wannan side din nashi ba.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
17
Akan Aisha Daddy yayi watsi da policy dinshi na cewa iyalinshi bazasu ci abincin masu aiki ba don kuwa a yanzu kowa na gidan girkin Lami suke ci don laulayi ya sako Aisha a gaba komai taci sai ta amayar dashi.
Sosai take ganin kulawa da tarairaya a wurin Daddy abinda ya kara assasa wutar kiyayyarta a zuciyar yaran don sosai suke bakin cikin ganinta da ciki tun ma dai ba Farida ba.
Sai da cikinta yayi watanni hudu sannan ta samu saukin laulayin. A lokacin ne kuma ta karbi hidimar gidanta duk da dai Daddy yaso ta bari Lami ta cigaba da kulawa da komai amma ta dage akan zata iya don haka ya kyaleta.
A kwance take akan gadon Daddy sai shagwaba take zuba mishi wai jikinta na mata ciwo. Shi kuma ya biye mata yana mata tausa hade da yi mata mitar aikin da take yi ne ya saka mata ciwon jikin shine kuma dalilin da yasa tun farko ya hanata yin aikin taki ji.
Tun tana mamakin kulawar da take samu daga Daddy har ta dain don da farko ma kasa sakewa tayi dashi sai da taga dai da gaske yake janta ajikinshi sannan ta sake ta bar yin dari-dari dashi.
"Um Daddy kana jina" tace mishi cikin muryar shagwaba. Bata fuska yayi yaja kunnenta kadan yace "bana hana ki ce mini Daddy ba, ni ba Daddynki bane Daddyn baby ne" ya fada yana mai shafo cikinta. "Gara ma tun wuri ki daina kirana Daddy nan don banaso, kirani da sunana Ja'afar yafi mini, ok".
"Owch da zafi fa Dad... ow sorry, nifa gaskiya bazan iya kiran sunanka ba gatsau, haba ai babu ma tsari wallahi" ta fada tana mai cuno baki.
Sunkuyowa yayi yay kissing din lips dinta lightly sannan yace "to ki kirani da wani sunan amma ba Daddy ba". Tace to shikenan zanyi tunani, ni kasa na manta me ma zance maka, yauwa dama so nake nace'maka inason zuwa gidan Hajiya na gaisheta".
A take ya bata fuska yace "nifa bana son yawo, ke da baki da lafiya wane fita kuma zakiyi. Ina ce'kuma kusan sau uku Hajiyan tana zuwa dubaki bare kice kin dade baki ganta bane yasa kike son zuwa".
Jikinta ne yayi sanyi jin abinda yace sai dai kuma bazata iya mishi musu ba don kuwa bata saba musu dashi ba komai yace da to take amsa mishi. Sai dai kuma har cikin ranta bata ji dadi ba don har fuskarta sai da ta nuna bacin ranta.
"Fushi kikayi don nace bazaki fita ba" tace "a'a me ka gani" yace "gashinan kin bata rai kin daina magana bayan da hira mukeyi". Yake kawai tayi tace "a'a ba fushi nayi ba ai nasan hakanan bazaka hanani zuwa wurin Hajiya ba dole kana da naka dalilin kuma ma ai ka fada cewar bani da lafiya. Babu komai wata rana sai naje idan na kara samun sauki".
Dole ba don taso ba ta ware take janshi da hira don ta kawar mishi da shakku a zuciyarshi sai dai har ga Allah bataji dadin hanata zuwa gidan Hajiya da yayi ba. Tunda aka kawota gidan a matsayin matarshi bata taba fita ba sai lokacin da sukaje asibiti kusan watanni bakwai.
Tana son zuwa gaya ma amma sanin cewar ba lallai ne ya barta ba yasa ta kasa tambayarshi bare kuma yanzu data samu cikinnan komai takeyi idonshi nakai, ita har mamakin son yaranshi takeyi.
Da safe ne bayan sunyi breakfast yake ce mata ta shirya taje gidan Hajiya amma karya dade don baya son kaiwa yamma a unguwa. To itama tasan policy dinshi ne tun lokacin Mami nada rai bata wuce karfe biyar a waje.
Kitchen ta nufa ta hada abincin rana. Alkubus tayi da miyar taushe sai farfesun kayan ciki. Bayan ta shirya warmers ne ta zuba wanda zata kaiwa Hajiya ta hada a cikin basket sai toma dkinta don ta shirya.
Kafin ta shirya dama sai da ta tura Zainab don ta fadawa Mallam Adamu cewa zasu fita. A sitting room dinshi na sama ta iske shi ta mishi sallama sannan ta fita.
Lokacin da ta isa harabar gidan sai ta iske babu Mallam Adamu babu motar kuma, cikin daurewar kai ta tsaya tana kallon wurin daya saba ajiye motar. To ko dai Zainab bata gaya mishi cewa zasu fita ba.
Komawa tayi cikin gidan, a zzaune a parlour Ruqaiya da Zainab ne suna kallo a tashar disney. "Zainab baki fadawa Mallam Adamu cewa zamu fita ba ne" ta tambayeta bayan ta zauna akan kujera.
Tace "na fada mishi, su Yaya Ummie da Yaya Farida ne suka ce ya kaisu gidan kawarsu kuma ya fada musu cewa tare zaku fita suka ce idan ya kaisu ya dawo ya kaiki".
Ok kawai tacewa Zainab. Tasan da gayya suka fita bayan sun sanccewa fita zatayi don a gabansu ta tura Zainab ta shaidawa Mallam Adamu zata fita shinw suka rigata ficewa ta kuma san ba lallai ne su barshi ya dawo yanzu ba.
Tashi tayi ta haya sama don ta sanarwa Daddy cewa bata tafi ba. Tana shiga sitting room din yace mata "ya kika dawo ko mantuwa kikayi", gyada kai tayi tace "a'a na samu su Farida sun fita tare da Mallam Adamun ne". "Baki gaya mishi zaki fita bane suka fita ba tare da sun jiraki ba", tace "na aika Zainab ta gaya mishi maybe sunyi zaton ba yanzu zan fita bane".
Cikin fada yace "zancen banza kenan yasan zaki fita amma ya biye tasu Farida ya fita dasu, wa ma ya basu izinin fita. Ko sun sanar dake zasu fita. Girgiza kai tayi tace "um-um maybe kuma ba nisa sukayi ba shi ya saka basu sanr ba".
Tashi yayi ya shiga daki ya canja kaya zuwa kaftan ya dauko kwy din mota ya fito. "Tashi mu tafi" yace mata. Tashi tayi tabi bayanshi suka sauka kasa. Suna shiga parlour ta cewa Ruqaiya da Zainab su dauko takalmi da gyale suzo su tafi.
Juyowa yayi ya kalleta jin abinda tace yace "dama dasu kika shirya tafiya" tace "a'a na gani ne gidan babu kowa sai su Lami kaga ai bai kyautu a barsu su kadai ba".
Bai kara cewa komai ba sai dai kuma har cikin ranshi yana Jin dadin yadda take kula mishi da yaranshi yasan hadda wannan yasa mishi sonta a zuciyarshi.
Suna saukowa suka fita, yaran na baya ita kuma ta kame a gaban mota. Jefi-jefi suna hira har suka isa gidan Hajiya. Yana tsaida motar yaran suka fita da gudu don ko motar basu rufe ba.
Murmushi kawai Aisha ta dauki basket dinta ta fita ta nufi hanyar cikin gidan. Horn din da yayi mata ne ya sakata juyowa. Fitowa yayi ya kulle motar sannan yace "ki jirani mana mu shiga tare".
Ita dai kunya takeji yanzu kawai sai Hajiya ta gansu sun jero, shine fa dalilin da yasa tayi saurin fita don ta rigashi shiga amma ya tsaida ita.
Gaba ya wuce ta bishi a baya. A tsakar gida suka iske Hajiya a zaune akan tabarma su Ruqaiya sunyi matashi da cinyarta. Haka nan yau sai taji tana kunyar hada ido da Hajiya.
Cikin sanyin jiki ta karaso ta zauna akan tabarmar tana gaida Hajiya ita kuma tana tambayarta jikinta. Sai da ya bri suka gam gaiswa sannan ya gaida Hajiya ya tashi yana mi kallon Aisha yace "zan tafi sai da yamma zan dawo, inasu Zanab ne suzomu tafi kunsan yau akwai islamiyya" tace mishi "to nagode Allah ya kiyaye".
Bayan tafiyarsu ne Hajiya tace mata "tashi ki shiga cikinima yanzu nima yanzu zan shigo, tashi tayi ta koma parlour ta zauna.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
19
Yau kwanankin Aisha uku a asibiti kuma yau dinne ake saka ran za'a bata sallama. A cikin kwanakin nan gaba daya su Farida sai wasan buya suke yi da Daddy ko da wasa basu bari sun hadu dashi ba.
Shima kuma baibi takansu ba don a yanzu ba abinda ke gabanshi ba kenan. A yanzu ta lafiyar Aisha yakeyi, ya bari ne sai sun koma gida sannan ya zauna dasu dukkansu don yaji miye musabbabin hatsarin daya faru.
Baya so ya zurfafa zarginshi akan yaran sai dai kuma yanayinsu a lokacin ya nuna tabbas basu da gaskiya. Gashi kuma tun ranar bai kara sakasu a idanunshi ba abinda ya kara assasa zargin da yakeyi na cewar sune ke da alhakin kada Aisha har ta kusa tayi loosing yaranta.
Mutanen gaya ma sun samu labarin haihuwar Aisha don haka sukayita tururuwar zuwa dubata, Yakumbo Dije kuma ta zauna don ta kula da lafiyarta data jariran.
Koda aka sallameta gidanta aka wuce da ita duk da dai Hajiya taso ta tafi da ita gidanta amma Daddt yace a'a tunda dai ga Yakumbo Dije babu bukatar sai ta koma wurin Hajiya.
Koda suka dawo daga asibitin su Ummie basu je sun mata sannu ba bare suga babies, Khalifa ne kadai ya shiga ya dubata a daren ranar sai kuma su Ruqaiya da suka tare a dakinta basa motsawa ko nan da can.
Bayan kwana biyu da dawowarsu daga asibiti ne Daddy ya tara su a parlourshi na sama, tun daga kan Khalifa da ba ma ya nan abin ya faru har zuwa kan Farida. Ruqaiya da Zainab ne kawai babu.
Hatta da Hajia a ranar sai da tazo don tun suna asibiti ya gaya mata cewa yana so za suyi magana amma bai gaya mata akan miye ba sai kuma a yau yayi mata waya yace ya tura Khalifa ya daukota.
Gaba dayansu sun taru a parlourshi har Aisha. Ga Mu'azzam da Farida kuwa gaba daya sun rude don sun tabbatar da wannan zaman akansu akayi shi, hatta da Ummie a tsorace take.
Kallon wurin da suke Daddy yayi yaga yanda sukayi tsuru-tsuru kwata-kwata basa cikin nutsuwarsu.
Bayan wasu 'yan mintuna ne Daddy yayi gyaran murya yace "abinda yasa na taraku duka anan shine dan na sanar daku abinda ya faru kwanaki biyar da suka wuce na samun Aisha da nayi kwance a cikin jini bata cikin hayyacinta sai kuma wadannan da na samu a tsaye akanta wanda bana raba daya biyu sune sukayi sanadin dana sameta a halin dana tarar da ita" ya fada yana mai nuna su Mu'azzam.
Yaci gana da cewa "shine yasa na taraku anan don ina son sanin asalin abinda ya faru, Aisha ko zaki gaya mini yanda akayi kika fadi akan cikinki har yayi sanadin da sai da aka miki aiki aka ciro babies?"
Sunkuyar da kanta tayi ta kasa magana don sai yanzu da yayi maganar ne ma taji ciwon abin sosai. Bata taba sanin kin da suke yi mata har yakai yanda zasu yi mata lahani ba sai yanzu.
Tasan da gayya Mu'azzam ya cilla mata ball dinnan a cikinta abinda bata taba zaton zasu iya yi mata ba. Jin shirun nata yayi yawa ne yasa Daddy yace mata "Aisha kiyi magana mana, nace ko zaki iya fada mini abinda ya faru a ranar na tarar dake a kwance cikin jini".
Girgiza kanta tayi sannan tace "a gaskiya bazan iya tunawa ba na manta". Hajiya ce ta ce "wanne irin kin manta kina nufin baki san yadda akayi kika fadi akan cikinki ba da har yay sanadin da akayi miki aiki aka ciro yaran dake cikinki, kenan kin samu shafewar tunani da bazaki iya tuna rayuwarki ta baya ba".
Nanma Aisha cewa tayi "a'a Hajiya ban samu shafewar tunani ba kawai dai na manta abinda ya faru ne a ranar". Hajiya zata sake magana Daddy yayi hanzarin cewa "kyaleta Hajiya tunda tace ta manta shikenan saukinta ai ba ita kadai bace a wurin da abin ya faru don haka kai Mu'azzam kaine babba ko zan iya sanin abin d yaru da har nazo na iske Aisha a kwance yayinda kuke tsaye akanta kai da kannenka".
Mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci Mu'azzam don har ga Allah yana tsoron Daddy yasan cewa shine ya cilla mata ball a ciki duk da dai yana tunanin Daddyn yasan cewa sune shine ma dalilin da yasa ya tara su duka anan wurin.
Ganin yayi shiru ya kasa magana ne yasa Daddy ya juya akalar tambayarshi wurin Ummie, itama shiru tayi ta kasa bashi amsa haka ma Farida.
Ranshi yayi mummunan baci, shirunsu ya kara tabbatar mishida zarginshi na cewa sune sukayi sanadin da Aisha ta kwanta a asibiti.
Cikin masifaffiyar murya yace "kunsan me shirun ku yake nufi, yana nufin zargin da nake yi akanku ya tabbata don ko rantsuwa zan iyayi akan cewa kune kuka yi sanadin da Aisha ta fadi. Yanzun its either ku fada mini gaskiyar abinda ya faru ko kuma nayi bincike na gano yanda abin ya kasance don kada ku manta ba wai ku kadai bane a wurin a ranar da abin ya faru kun kuma san Zainab bazata gaya mini karya ba. So its better you start talking right now".
Mu'azzama ne yayi karfin halin cewa "Daddy don Allah kayi hakuri wallahi tsautsayi ne",cikin tsawa yace "comeon ka fada mini abinda ya faru don bawai na tara ku anan don kuyi mini yawo da hankali bane".
A haka dai Mu'azzam ya daure ya fadi abinda ya faru sai dai yayi kokarin ya nuna cewa laifin na Farida ne don ita ta kauce bata bari Aisha ta dafa ta ba abinda yayi sanadin data kifa akan cikinta.
Gaba daya Farida rikicewa tayi jin Mu'azzam na neman ya juya laifin kanta ita kadai bayan kuma da ace bai fara jefa mata ball dinba da duk haka bata faru ba.
Sosai ran Hajiya ya baci da jin abinda ya faru. Fada sosai ta hau yi tana cewa "wannan ai rashi imani ne ku jefi mace da tsohon ciki, me kuke so ku zama ne yarannan".
Khalifa ma ranshi ya baci dajin abinda sukayi, ya rasa me ke damun yarannan wai har Mu'azzam da yake babba kuma namiji ace yana abu irin na jahilai yana biyewa su Farida.
Daddy kam takaici ne ma ya hana shi magana sai zuwa can ya ce"yanzu magana guda daya ce zanyi bazan yi tolerating iskancinku ba acikin gidana dole ne kuyi respecting matata don disresoecting dinta yana nufin disrespecting dina. Aisha da kuke gani matata ce and its a must for you to accept her as a mother, babu ruwana da wani grudges da kuke holding against her wannan damuwarku ce.
Abinda na sani shine cewa nine mai gida kuma dukkanku a karkashina kuke so dole kuyi accepting ko waye na kawo na ajjiye a cikin gidannan, don haka this should be the first and the last time da wani abu makamancin wannan zai kuma faruwa.
Abu na gaba kuma shine ke Ummie da Farida ku fito da miji auren zan yi muku tunda na lura har da kyaleku da nayi kun zaune mini a cikin gida babu aure yasaka kuke mini iskancin da kuka ga dama, don haka sai ku shirya auren Khalifa da za'ayi tare da naku za'a hada".
Kai kuwa Mu'azzam babu abinda zan ce maka don kuwa a shekarunka idan har baka tsawatarwa da na kasa dakai ba bazaka biye musu kuyi abinda kukayi ba amma kuma unfortunately kai ne kake nuna musu ko miye ma sukeyi, abu daya zan gaya maka shine bazan dauki rashin da'a a cikin gidana ba. Bazan yadda da ganganci irin wannan ba ayi terming dinshi as tsautsayi".
"sannan kuma inaso dukkanku ku bawa Aisha hakuri tare da alkawarin makamancin irin wannan bazai kuma faruwa ba". Ummie ce ta dago kai tana sharar hawaye ta ce "Aunty Aisha don Allah kiyi hakuri In Sha Allahu wani abu makamancin wannan ba zai kuma faruwa ba" ita dai Ummie har cikin ranta tayi danasanin abinda ya faru duk da dai babu ita a cikin abin da ya faru amma kuma tasan cewa ita ma tanayi wa Aisha abubuwa.
Duk sai da suka bata hakuri sannan Daddy ya sallamesu, itama Aisha ta tashi ta koma dakinta.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
18
Daddy ne a zaune a parlour yana zuba idon ganin ta inda Ummie da Farida zasu shigo. Tun bayan daya dawo daga kai Aisha gidan Hajiya yake zaune a wurin sallah ce kawai ta tashe shi kuma yana dawowa daga masallaci ya cigaba da zama a wurin din baya so su dawo bai sani ba.
So yake yaji ina suka fita tun safe bayan sun san Aisha zata fita kuma da izinin wa, don duk da yana sake musu wannan baisa ya kyalesu suna abinda suke so ba komai zasuyi sai da saninshi hakanan idan zasu fita sai ya yardar musu.
Har yaje masallaci sallar la'asar ya dawo basu dawo ba. Yana son yaje ya dauko Aisha amma ba ya son su dawo ba ya nan. Yana zaune a wurin har kusan karfe biyar da kwata sannan suka shigo suna dariya, Farida na cewa "yau kam duk abinta wannan fitar kuma dolenta ta hakura da ita".
Turus sukayi ganin Daddy a zaune a parlour don basu zaci ganinshi ba. Allah yasa dai baiji suba. "Sannu da hutawa Daddy" suka ce mishi tare da russunawa. Banza yayi musu ba tare da ya amsa ba. Ganin haka yasa sum-sum suka wuce stairs zasu hau sama.
Wata irin razananniyar tsawa ya musu tamkar yana a barrack yace "ku zo nan". Jiki na rawa suka zo suka durkusa nesa dashi don sun bala'in tsorata da tsawar da ya musu.
"Daga ina kuke" ya tambayesu. Cikin in'ina Ummie tace "daga gidansu friend dinmu" yace "wa kuka tambaya da zaku fita" suka yi shiru. Wata tsawar ya daka musu yace "comeon ku bani amsa nacevda izinin wa kuka fita" suka ce "babu kowa".
Yace "kenan ku nan har kunyi girman da zakuyi gaban kanku ko, har kuna iya fita daga gida ba tare da kun sanar ba ko. Wai me kuke so ku zama ne a cikin gidannan, halayenku fa sun fara isata. Idan kuka cika mini ciki matakin dazan dauka akanku bazai yi muku dadi ba".
Fada sosai yayi musu irin wanda tunda suke dashi bai taba yi musu makamancinshi ba. Gaba daya Daddy ya canja musu tamkar ba shi ba. Tashi yayi ya fita don zuwa daukar Aisha amma kafinnan sai da ya jawa Mallam Adamu kunne akan abinda yayi yace don miye yasan zasu fita da Aisha amma ya biyewa su Farida suka fice yawo ba tare da ya sanar mata ba.
Tun daga ranar ta samu saukin iskancinsu, sunayi mata amma sai sun tabbatar Daddy ba ya nan don yanzu sun fahimci cewa bazai kyalesu su cigaba da wulakantata ba.
A yanzu cikin Aisha yana cikin watanni na takwas. Tana zaune a parlour tare da Zainab tana yi matavkarin karatu a cikin suratul jumu'at. Mu'azzam ne da Farida da Ummie suka shigo daga waje suna dariya. Ball ce suka shigo da ita suke passing a tsakaninsu.
Hayaniyarsu ce ta ishi Aisha ta tashi zata bar wurin kawai sai Mu'azzam ya saita cikinta ya cillo mata ball din. Wata iriyar azaba ce ta ziyarceta. Tayi taga-taga zata fadi tayi hanzarin kai hannu don dafa Farida dake kusa da ita sai dai kuma lura da Faridan tayi cewa zatayi garkuwa da ita ne yasa da sauri ta ja baya don haka Aisha ta fadi akan cikinta.
Wata irin razananniyar kara ta saki kafin numfashinta ya dauke. Gaba daya sun tsorata da jin karar da tayi bare kuma da suka ga jini yana bin jikinta. A gaggauce Daddy ya sauko daga sama don ihun da yaji anyi yasan bana lafiya bane sai dai ya kasa tantance muryar waye yaji.
Ganin Aisha kwance a cikin jini yasaka mishi mummunar faduwar gaba ga kuma yaranshi da sukayi tsuru-tsuru a wurin ko motsin kirki sun kasa yi baya raba daya biyu suna da hannu a cikin abinda ya faru sai dai yanzu ba lokacin da zai tsaya bin ba'asu bane.
Bai bi ta kansu ba ya sunkuya ya dauki Aisha yayi waje da ita yana kwalawa Mallam Adamu kira. Bude motar yayi ya sakata a gidan baya sannan ya shiga ya zauna ya tallabeta a jikinshi. Mallam Adamu kuma ya zagaya bangaren ya shiga suka nufi asibiti.
Suna isa asibitin yayi hanzarin fita yana dauke da ita ya shiga ciki. Likitoci sun rufa akanta suna kokarin ceto rayuwarta data abin dake cikinta. Sunyi nasarar tsaida jinin saidai kuma akwai bukatar ayi aiki a cire. Sun nemi Daddy da yayi signing inda bai bata lokaci ba ya cije dukkan takardun da ake bukata.
An shiga da ita theatre ya dawo reception ya zauna sai dai kuma zaman ma gagararshi yayi don kwata-kwata hankalinshi ba'a kwance yake ba. Yana nan a tsaye a wurin ne nurse ta fito ta bukaci daya kawo kayan baby.
Khalifa ya kira a waya yace mishi yaje wurin Lami yacevta duba dakin Aisha zata ga akwatin data shirya na zuwa asibitu ta bashi ya kawo.
Tambayarshi Khalifan yayi ko ta haihu ne Aishan. Bai tsaya amsa mishi ba kawai ya kashevwayarshi. Baifi mintuna goma da kiran Khalifa ba sai gashi ya shigo dauke da akwati.
Yana shigowa abinda ya fara tambayar Daddy shine ta haihu, Daddy yace mishi "a'a suna mata c.s ne su ciro baby".
Rufe bakinshi kenan sai ga nurse din ta dawo karbar kayan ta kuma shaida musu cewa anyi nasarar ciro mata yara biyu mace da namiji. "Ita kuma Aisha fa" shine abinda Daddy ya fara tambayarta. Tace mishi " don't worry she will be fine" ta dauki akwatin ta juya.
Sosai Daddy yayi farin cikin jin cewa ya samu twins, sai yanzu hankalinshi ya kwanta har ya samu ya kira Hajiya a waya ya shaida mata batun haihuwar.
Lokacin da Hajiya ta iso asibitin har an fito musu da jariran ita kuma Aisha an kaita wani dakin zuwa lokacin da zata farfado.
*****
Kuyi hakuri jiya kun jini shiru thruout jiya wayata babu caji ne.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
20
Anyi taron suna lfy yara sunci suna Maryam da Abdallah, sosai Daddy ya kashe kudi a hidimar sunan. Mutanen gaya suka tafi suna ta murnar yadda suka tarar da Aisha cikin daula gashi mijinta ya wadata ta da komai na bukata.
A yanzu haka shirye-shiryen aurensu Ummie ake yi. Dama dukkansu akwai masu zuwa wurinsu don haka da Daddy ya ce su fito da miji shine kowacce ta turo maneminta gida.
Ita dai Ummie wani lecturer dinsu ne ke sonta, bai taba aure ba amma yanada shekaru don akalla zaiyi shekara talatin da takwas.
Ita kuma Farida me mata ne ta samu, ya dade yana sonta tana share shi duk da son data ke mishi sai dai kuma rashin son auren mai mata yasa bata wani kula shi. Ganin Daddy ya dibar musu takaitaccen lokaci don su fitar da miji yasa ta amince da aurenshi.
Duka manemannasu sun turo magabatansu an tsaida magana don haka aka yanke lokaci watanni uku masu zuwa daidai da lokacin da aka yanke na auren Khalifa.
Tunda lokacin bikinnan ya matso Aisha bata samu zama ba don kuwa hidima tayi mata yawa. Komai na harkar bikin a hannunta Daddy ya damka shi duk da dai amaren basu so hakan ba to amma babu yadda zasuyi.
Kullum cikin fita sayyaya suke tun daga kan furniture zuwa kayan kitchen dasu rugs da labulaye har kan kayan decoration na gida da kuma kayan da zasu saka na biki.
Ita ma kuma Aisha bata bashi kunya ba don kuwa ta tsaya taga anyi musu kaya na fita kunya duk da dai kowacce ra'ayinta aka bi wajen sayen kayan.
A wajen karbar kudin events din biki ne Daddy yayi musu jan ido don kuwa kudaden da suka nema a wurinshi sunyi yawa don events suka shirya zasuyi na rashin hankali a kalla sun tsara yin events sunkai shida. Dole suka rage events din zuwa guda uku.
Kowanne event sun fitar mishi da anko tun daga kan kamu da yini jar luncheon da dinner da zasuyi kuma duka masu tsada nan ma da kyar Daddy ya yarda yayi wa su Ruqaiya don yace abin yayi yawa su kuma yaran ba tausayinshi suke yi ba sun manta cewar hidimar auren 'ya'ya uku ne a gabanshi.
An fara bikin ne da kamu inda suka shirya yinshi anan cikin gidan inda amare sukayi shigar atamfa super exclusive akayi musu dinkin zannuwa falle biyu sai polo shirt da suka hada da zanin suka rufa da dayan zanin. Suma 'yammata ankon Zanin atamfar Julius holland sukayi da polo shirt din.
Anci abinci na alfarma an zubarwa da makada naira inda amare suka zage sukayi ta tikar rawa tamkar dai ba amaren ba.
Kasancewar kamun da yamma akayi yasa Maman Farida ta shirya musu mothers night a meena event center.
An kawo wa Aisha cards guda biyar nata dana wadanda zata gaiyata, Farida ce ta tura Zainab ta kai mata cards din a lokacin tana kitchen tana aiki tana jin Faridan na fadawa Ummie cewa wai wallahi da Mummynta tayi shawara da ita bazata bawa Aisha kati ba don har yanzu da takaicinta a ranta duk lokacin data tuna cewa Daddy bai taba daga musu murya ba sai akanta.
Dariya kawai Aiaha tayi don tasan dama Farida ta sama mata lafiya daga rashin mutuncinta ne don tasan yanzu Daddy bazai yadda da iskancinsu ba.
Ko lokacin data basu gudunmawarta ta sarka gold kirar dubai data saya musu Farida karba kawai tayi babu godiya sai cewa da tayi ai dole ne ma ta saka tunda dai tasan da kudin ubanta aka saya, ko a lokacin Aisha bata kalleta ba don tasan duk abinda zata yi mata na dan lokaci ne.
Anyi mothers night din inda amare sukayi shiga cikin bridal lace da sukayi dinkin doguwar riga. Komai da suka saka iri daya ne sai colour data bambanta. Ita Farida tayi amfani da colour fari da blue yayinda Ummie tayi olive green da orange.
Tunda aka fara bikinnan Aisha bata zauna ba ga hidimar yara gata Daddy da kullum cikin yi mata korafi yake yana cewa tunda ta fara hidimar auren 'ya'yanta ta manta dashi.
Gaba daya hidimar bikinnan ta gajiyar da ita. A ranar asabar ne bayan an daura aure ta shirya musu walimah inda aka gaiyato malamai sukayi wa'azi sosai akan hakkin miji akan matarshi da kuma hakkin matar akan mijinta da zama da abokiyar zama.
Da yamma ne aka kai amare gidajensu. Ita dai Ummie an kaita redbricks ne yayinda Farida aka kaita lamido crescent. Ita kuma amayar Khalifa nan unguwarsu aka kawota gidanshi babu nisa da gidan iyayenshi.
*****
Asghar da Sajjad nayi muku barka da sallah da fatan Allah ya maimaita mana ya amshi ibadunmu. Sorry for the long silence wallahi tunda na Sligo kano sallah ban samu zama ba.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
21
A yanzu da akayi wa su Farida aure Aisha bata da wata matsala a cikin gidanta don sosai Ruqaiya da Zainab ke yi mata biyayya kuma dama dai a yadda yaran suka taso tare da ita bata da matsala dasu.
An gama biki da sati biyu Daddy ya kwashi Aisha da yaranta masu watanni biyar suka tafi umrah sai Zainab da Ruqaiya kasancewar Yaran na hutu.
Mu'azzam kawai aka bari a gida don har lokacin Daddy ba wai ya huce daga fuahin da yakeyi dashi bane. A lokacin da Daddy yayiwa Aisha maganar tafiyarsu Umrah sosai tayi murna sai ta tuna lokacin da Farida tayi ta mata kafafa akan zasuyi tafiya su barta to itama yanzu gashi nata lokacin yayi don dama komai yana da lokacin.
Sosai Ruqaiya da Zainab ke taimaka mata wajen rainon twins, duk da Daddy na fadan yawan bawa yaran twins da take yi wai kar su kada su. Idan yana fadanshi kawai sai dai tayi dariya tana mamakin son 'ya'ya irin na Daddy shi komai a harkar yaranshi idonshi yana kai.
Sai dai ta sakawa ranta cewa ita kam bazata yadda ya bata mata yara ba irin yadda yayiwa su Ummie shine kuma dalilin da yasaka suke taka kowa ba tare da fargaba ba don sun san komai sukayi a wurin ubansu ba laifi bane.
Sai da sukayi sati uku sannan suka dawo gida nigeria, gaba daya a wannan lokacin Aisha ta canja ta kara yin kyau saboda kwanciyar hankali data samu ga uwa uba soyayya da kulawar mijinta data samu.
Bayan sati daya da dawowarsu ne Daddy yace ta shirya ta rakashi gidajensu Ummie yaje yaga dakunansu don tun da akayi auren bawai yaje bane.
Tayi shirinta cikin atamfar super exclusive kalar navy blue da ratsin fari da light yellow a jiki sai tayi amfani da farin mayafi da takalmi. Bata dauki jaka ba sai wayarta data rike a hannunta.
A gida ta bar twins qurin masu rainonsu kuma ganin su Ruqaiya na gidan yasa bata damu sai ta fita dasu ba.
Gidan Farida suka fara zuwa, Daddy yace ta shiga ta sanar musu da zuwan shi. Ta shiga cikin gidan da sallama, a main parlour su ta tarar da uwargidan Faridan tare da yaranta da maigidan.
Cikin girmamawa sosai matar ta karbeta duk da cewa zata iya girmewa Aisha. Bayan sun gaisa ne Aishan ke tambayar Farida tace mata tana dakinta ta saka yarinyarta ta raka Aisha.
Kafin su wuce ne Aisha ke sanar musu cewa tare da Daddy suke ai kuwa maigidan naji yayi hamzarin tashi yana cewa bari yaje ya shigo dashi.
Ta shiga dakin Farida tana ta kwala sallama amma ba'a amsa ba don haka ta zauna a parlour tacewa yarinyar ta shiga dakin ta yi mata magana. Ta shiga babu dadewa ta fito ta ce mata wai gata nan zuwa.
Tayi zaman fiye da mintuna goma kafin Farida ta fito tana yatsina fuska ta zauna. A dakile tace mata ina yini, lafiya kawai Aisha tace mata tace "tare muke da Daddynku yace na rakoshi yaga gidanku so yana kasa idan kinga dama kina iya zuwa ki gaisheshi".
Jin cewa yare suke da Daddy ya sa tayi saurin tashi ta fita. Ta dan jima kafin ta dawo, kamar bazata yiwa Aisha magana ba sai kuma tace mata "Daddy yace kije ku tafi" mikewa tayi ta ajiye mata ledar tsarabarta tace mata "to Allah ya bamu alkhairi" bata jira amsawarta ba ta fice.
Daga gidan Farida gidan Ummie suka nufa. Anan ma Daddy bai shiga ba. Ita kam Ummie ta karbeta da mutunci da murnarta har tana tambayarta twins tana cewa me yasa ba'a zo dasu ba.
Bayan sun gaisa ne take sanar mata cewa tare suke da Daddy. Sosai tayi murnar jin Daddy yazo gidanta. Tashi tayi ta shiga part din maigidan ta sanar mishi, babu wani dadewa kuwa ya fito.
Har kasa ya tsugunna ya gaida Aisha sannan ya fita don ya shigo da Daddy. A parlourshi ya saukeshi don haka can Ummie ta bishi ta gaidashi. Sun danfi dadewa a gidan Ummie sannan Daddy yace ta fito su tafi.
Itama ajiye mata tsarabarta tayi sannan sukayi sallama ta fita. Har wurin mota suka raka su sunata godiya. Ummie na rokon Daddy don Allah ya bari su Ruqaiya suzo mata don tunda akayi auren ya hanasu zuwa.
A hanyarsu ta komawa gida ne ya biya da ita grand square sai dai be yadda ta shiga ba, bayan ya fito ne ya miko mata leda mai dauke da turaruka designers guda uku. Sai kuma chocolates da biscuits na yara.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
22
Tunda ta tashi yau bata zauna ba. Aiki takeyi kamar bazata gama ba. Ita kam wannan abu ya isheta ace aikin kenan kullum ta tashi bata da hutu, tace tana bukatar cook ance a'a ta bukaci house help nan ma yace mata a'a. Gashi yanzu ya kawo mata aikin girki wai zaiyi baki bayan duk wannan wahalar data keyi ta kuma san ba appreciating zaiyi ba don kullum tayi girki sai ya kushe. Ita kam har ga Allah bazata iya ba don ko a gidansu bata saba da aikin wahala ba kitchen kuwa kwata-kwata basa shigar shi da sunan girki.
Yanzu wannan aikin abincin ya zatayi dashi fisabilillahi tunda dai yasan ba iyawa tayi ba. Tana tsaye a kitchen din ta tasa kayan aikin a gaba tana kallo ya shigo ya kare mata kallo ganin yadda ta doka tagumi tana kallon kayan ya kara bata mishi rai. Tsaki yayi abinda ya maido da hankalinta gareshi. Cikin dakewa yace mata "su Maryam zasu zo su tayaki aikin amma na yau kawai, gara tun wuri kisan me kike ciki don bazan dauki wannan sakarcin ba. Ace kina 'ya mace amma baki iya komai ba, I've had enough of ur nonsense. Duk yadda zaki yi ki koyi tsaftar muhallinki da girka abincin gidanki kije kiyi don na gaji da barnar Kudina kina mini asara" wani tsakin ya karayi kafin ya fita ya bar mata kitchen din.
Har cikin ranta taji dadi da yace su Maryam suzo su tayata aikin sai dai kuma bata san ya yake so tayi ba wajen koyon girki. Ita yanzu wa zata samu da zata na koya mata girki har ta iya, mts ita fa harka da kitchen ma kwata-kwata batayi mata ba. Ita kam Farida taji dadinta wallahi komai tana kwance za'ayi mata shi amma ita nan gata an saka ta a gaba kullum cikin fadan wani kuskure nata yake.
Da taimakon kannenshi Maryam da Amina suka hada lafiyayyen lunch inda suka yi musu arabian zirbiyan da farfesun kayan cikin rago da potato salad sai zobo drink din daya wadatu da cucumber da kayan kamshi.
Sun shirya table tsaf sannan suka kara kimtsa gidan sukayi wa Ummie sallama cewa zasu koma gida don suna zuwa islamiyya. Sosai taji dadin aikin da suka mata, da zasu tafi ta musu kyautar kayan kwalliya da turare.
Tun bayan tafiyarsu take tunanin abinyi akan matsalarta, kamar tace musu su rinka zuwa suna koya mata abubuwan da suka danganci girki sai kuma taji kunyar yin hakan kannen mijinta nefa, to ko Farida zata kira ta bata shawarar yadda zatayi. Kai a'a tasan halin Farida sarai bawai zata bata wata shawarar arziki bane.
Idanunta ne taji sun cika da hawaye, sai yau ta kara tabbatar da tayi rashin uwa don kuwa da Mami na nan tasan da bata shiga cikin matsalar da take ciki ba yanzu tasan babu yadda za'ayi ayi aurenta ba tare da Mami ta koyar da ita kula da hidimar gidanta ba.
Ta jima tana kuka kafin ta rarrashi kanta tayi shiru, gashi Abdulhalim tunda suka ci abinci da abokanshi suka fita bai dawo ba. Wayarta ta janyo ta kira Yaya Khalifa.
Yana amsa wayar ta saka mishi kuka, sosai ta tayar mishi da hankali jin kukanta. Da kyar ya lallasheta tayi shiru sannan ya bukaci yaji damuwarta. Cikin rishin kukan ta sanar dashi duk abinda Abdulhalim yace ta karasa da fadin "ni bansan ya zanyi ba Yaya Khalifa wallahi na gaji komai nayi a gidannan baya appreciating sai yayi ta fada bayan kuma yasan cewa ban iya ba".
Shiru Khalifa yayi ya ma rasa me zaicewa Ummie, ganin shirun shi bazai taimaketa da komai ba yada yace mata "why not da bazaki nemi Aunty Aisha ba ina ganin idan har kika gaya mata zata san yadda zata bullo wa al'amarin kuma kinga catering ta karanta so ko ita ma ai zata iya koya miki girkin, amma
ke me kike gani".
Tasan Aunty Aisha bazata ki koyar da ita ba to amma tana jin kunyarta ganin irin rashin mutuncin da suka dinga mata. Jin tayi shiru bata amsa ba yasa Khalifa yace "bafa nace lallai ne sai kin nemeta ba na ga ne kamar ita yafi dacewa ki nema don ina ganin bazata ki taimaka miki ba".
"Banki ta taka ba Yaya Khalifa kawai dai ina jin kunyarta ne akan abubuwan da suka faru amma zan kirata a waya In Sha Allahu, nagode Yaya Khalifa". Sosai yayi mata nasiha kan hakuri da juriya a dukkan al'amuranta.
Ta jima tana juya wayarta tana contemplating kiran Aisha a waya ko kar ta kirata. Daurewa kawai tayi tayi dialling number, bata jima tana ringing ba taji amsawarta da sallama.
Cikin dauriya sosai ta iya amsa mata sallamar sannan ta gaisheta tare da tambayar lafiyar twins dasu Zainab. Da kyar ta iya yi mata bayanin dalilin kiran datayi mata. Shiru Aisha tayi tana saurarenta ba tare da ta katse ta ba har saida ta lura cewar ta gama maganar sannan tace mata "ina ganin abinda za'ayi shine ki nemi izininshi sai ki rinka zuwa gida muna yin girkin tare har ki kware batun gyaran gida kuma Ummie dole ne ki cire lalaci da kyuiya ki zage damtse kike gyaran muhallinki, kuma ma idan banda abinki ke da ba yara gareki ba ya za'ayi ki dinga barin gidanki yanayin datti ai bazai yiwu kice wai sai gidanki yayi datti sannan zaki gyara shi ba. Idan kina kula da gyaranshi akai-akai ko ace wata rana zaki tashi baki gyara ba ba za'a gane ba don yana samun kula. Kiyi kokari ya barki kina zuwa gidan sai ku tsara ranakun da zaki na zuwa idan d weekends ne to idan kuma ranakun aiki ne ma dai duk ina gida amma ina ganin kamar weekdays din zaifi tunda lokcin yana wajen aiki sauran bayani kuma sai kinzo gidan".
"Nagode sosai Aunty Aisha Allah ya saka da alkhairi In Sha Allahu zanyi mishi maganar nasan ma bazai ki ba duk yadda mukayi kuma zan kiraki a waya sai na shaida miki".
Sosai taji dadin maganar da sukayi da Aunty Aisha, In Sha Allahu kuma zata gyara al'amuran gidanta don kuwa tana son mijinta sosai bata so tana yawan bata mishi rai kuma ita ma tana so taga tayi abinda zata burgeshi har ya yaba mata.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
23
Kusan sati biyu kenan kullum da safe Ummie ke zuwa gida wurin Aisha don koyon girki. Zuwa yanzu kam Alhamdulillahi tana iya shiga kitchen tayi girkin abincin kuma a cinye ana santi. Ita kanta tana jin dadin yadda kullum tayi girki Abdulhalim ke yabawa don tun baya yadda cewa ita keyi har ya yadda don Aunty Aisha tana directing dinta ne kawai amma komai ita keyi aikin Aisha kawai ta saka ido.
A yammacin wata talata ne Aisha na zaune tare da Daddy a parlournshi na sama, yana karatun jaridar daily trust ne ta ranar ita kuma tana kallon tashar Africa magic hausa sai dai ba duka hankalinta ne akan kallon ba tana kula da twins da suke wasa.
Zainab ce ta shigo parlour da sallama sannan ta durkusa tacewa Aisha "Mummy Yaya Farida ce tazo tana parlour a kasa", jim Aisha tayi cikin tunanin lafiya Farida tazo yanzu da yamma don magriba ma ta kusa kuma ita din tun bayan aurensu zuwanta gidan baifi a kirga ba shima kuma bata fin mintuna goma take tafiya.
Tashi tayi ta sauka zuwa parlournsu na kasa. Farida na zaune akan kujera double seater ta hada kai da gwiwa. Koda Aisha ta shiga parlour bata dago ba ga alama bata ma san ta shigo parlourn ba har saida Aishan ta mata magana sannan ta dago kanta. Fuskarta tayi jajawur alamun taci kuka ta koshi.
Ganinta a haka gaba daya sai Aisha ta rude cewa takeyi "Farida lafiya wani abu ya faru ne ko baki da lafiya, ina maigidan? Me ke faruwa ne, kiyi mini magana mana". Gaba daya Aisha ta manta wacece Farida da irin zaman da sukayi tare yanayin data ganta a ciki ya sanyayar mat da jiki sosai.
Ita dai Farida banda kuka babu abinda takeyi tun Aisha na bin kanta don taji damuwarta harta gaji ta kyaleta. Suna zaune a wurin akayi kiran sallar magriba don haka Aisha tace mata "ko meye yake damunki hakuri zakiyi ki fawwalawa Allah al'amuranki ita wannan rayuwar da kike gani hakuri shine jigonta dolene ki koyi hakurin zama da mutanen da Allah ya hada ki dasu. Yanzu ki tashi kiyi sallah in yaso sai ki samu Daddy kuyi magana".
Bata jira jin amsawar Farida ba ta haya sama don yin sallar magriba. Sai da ta fara shiga parlour Daddy ta dauki 'yanbiyu ta mika su wurin nannysu sannan ta wuce dakinta tayi sallah. Koda ta idar bata tashi ba sai bayan da tayi salkar isha sannan ta fito.
Ta samu su Zainab da Ruqaiya akan table suna jiransu don yin dinner amma har lokacin Daddy bai fito ba. "Zainab je ki kira Farida tazo taci abinci" Aisha tace mata. Tashi tayi ta nufi aiken da akayi mata, dawowa tayi tace mata wai tace ta koshi.
Cewa tayi da yaran suci abincinsu kawai ba tare da sun jira Daddy ba. Bayan sun gama cin abincin ne ta koma sama don ta tambayi Daddy ko akwai abinda yake son ci ta mishi don tunda taga bai sauko dinner ba tasan ba cin abincin zaiyi ba.
Koda ta shiga parlour ta iske shine tare da Farida tana zaune a kasa akan rug din tsakiyar kanta a sunkuye a kasa sai dai hakan bai hana kukanta fitowa ba. Juyawa tayi zata bar parlour Daddy ya tsaida tare da cewa "ya zaki fita ko ba wurina kika zo ba" yace yare da kashe mata ido daya😉.
Murmushi kawai tayi amma sosai Daddy ya bata kunya. Cewa tayi "na gani ne dama baka sauko kayi dinnwr ba shine zan tambayeka ko akwai wani abu da kake so na shirya maka kafin dare yayi". "Thanks for the gesture amma bana bukatar komai sai tea sai ki hada mini da cake, ai akwai ko?" tace "um akwai" ta juya ta bar parlour.
A lokacin da suka zo kwanciya ne Daddy ke fada mata dalilin zuwan Farida wai mijin ne ya korota saboda tana da matsala da matarshi da yaranshi yace bazai iya zama da matar da bata son 'ya'yanshi ba. Ita kuma Farida tace wai yaran ne keyi mata rashin kunya kuma wai uwarsu ke saka su ba kuma tayi magana ba sai yace ita fitinanniya ce bata son zaman lafiya shi yaranshi nada tarbiyya baza suyi mata rashin kunya ba.
Shiru kawai Aisha tayi bata ce komai ba sai dai cikin ranta cewa takeyi alhaki ai kwikwiyo ne hakanan kuma sharri dan aike ne duk inda yaje zai dawowa maishi. Tana tuna yanda Farida ta takura mata a zaman gidannan ta kuma yi sa'a komai tayi daidai ne a wurin Daddy bata laifi yanzu gashi abin ya dawo kanta.
Sai dai bazata iya fitowa ta gayawa Daddy hakan ba don haka tace mishi "to yanzu wanne mataki zaka dauka don kasan bazai yiwu ja yanke hukunci ba tare da kaji ta bakin maigidanta ba ko", yace "hakane nayi tunanin kiranshi muyi magana sai naga dare yayi amma In Sha Allahu gobe zan nemeshi don naji ta bakinshi amma idan har abinda tace mini gaskiya ne shima bai kyauta ba ai yaran yanzu ba abin yarda bane bazai yiwu ka bashi shaida ba farat daya".
Wannan rayuwar da abin mamaki take, shine kawai abinda Aisha ke cewa a cikin ranta don sosai Daddy ya bata mamaki jin cewar da yakeyi wai mijin Farida bai kyauta ba tunda yabi bayan yaranshi bayan shi dinma haka halinshi yake akan yaranshi sam su basa laifi sai dai kai ka saba musu amma badai su suyi maka ba.
Washegari ne bayan Daddy ya dawo daga office mijin Farida yazo. A parlourn bakinshi ya sauki surikinnashi. Sai bayan sun gama gaisawa ne sannan suka fara tattaunawa akan maganar inda yake shaidawa Daddy cewa Farida bata so ko yaya taga yaranshi sun rabeshi sai ta hau harare -harare tana zare musu ido shine yasa ma ko dakinta basa shiga haka nan kuma ta raina matarshi ko gaisheta batayi gashi sai tace wai bata yadda yayi hulda da matarshi ba shi kuma ya gaya mata cewa yana son matarshi bawai ya daina sonta bane yasa ya aureta shi kuma baiga diya macen da zai aura ya wulakanta Matarshi akanta ba, idan taga bazata iya zama da ita ba to sai dai ita ta fita ta bar mata gidanta.
Shiru Daddy yayi yana saurarenshi sai dai ranshi idan yayi dubu ya baci da rashin arzikin da Farida keyi a gidanta don kuwa shi ta zubarwa da mutunci don duk wanda yaji abinda takeyi a gidanta zaice ne bata samu tarbiyyar arziki ba a gidansu.
Hakuri ya bawa mijinnata yace mishi kuma In Sha Allah hakan bazai kuma faruwa ba don sosai zai ja mata kunne akan hakan. Sun rabu akan cewa sai gobe zata koma gidan.
*****
Kuyi hakuri da wannan wallahi kaina ciwo yakeyi dauriya kawai nayi nayi typing wannan, sannan kuyi hakurin rashin jina kwana biyu bana samun caji ne a wayata kusan kullum a kashe take yini lokacin dazan samu cajin kuma dare yayi.
UMMASGHAR.
[11/26, 22:16] Umm Asghar (Fatima Eshak): 👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
'YA'YAN MIJI
👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦👩👩👧👦
Na Umm Asghar
24
Ranshi a bace ya shigo gidan. Tun daga kasa yake kwalawa Farida kira. Gaba daya jikinta ne ya dauki rawa jin yanayin da Daddy yake kiranta. Allah yasa dai ba wani laifin tayi ba don tun jiya dama a tsorace take da Daddy ganin bai wani bata goyin baya ba akan rikinsu da maigidanta.
A kasalance ta fito daga dakin don zuwa amsa kiran Daddy. Bata taba zaton akwai wata rana da zata ji tsoron haduwarta da Daddy ba irin yau don yanayin kiran da yake mata sosai ya kidimata. A bakin kofar dakin sukayi kacibis da Aisha da tazo kiranta. Ce mata kawai taje Daddy na kiranta ta wuce zuwa dakinta.
Da kyar Farida ta iya jan kafafunta ta wuce zuwa parlour Daddy. A hankali tamkar bata so tayi sallama, sai bayan daya amsa sallamar ne ta shiga cikin parlour. Durkusawa tayi tace "Daddy ina yini, gani ance kana kirana". Shiru ne ya ziyarci parlour tamkar babu kowa. Shi dai Daddy kallon Farida kawai yakeyi yana mamakin irin halayen yarinyar da abubuwan da mijinta yace tana yi mishi. Sai dai kuma yasan shine babban mai laifi a duk wani hali da Faridan ta kasance a ciki.
Tun tasowarta ya kasancevmai nuna bambanci tsakaninta da 'yanuwanta baya son laifinta ko kadan komai tayi a wurinshi daidai ne. Wani irin so yake yi mata da baya yiwa 'ya'yan daya haifa. Sosai yake tausayinta da maraicinta yana ganin duk duniya bata da sai shi tunda bata san ubanta ba. Kullum cikin nuna bambanci yake tsakaninta da 'yanuwanta don ko abu ne ya hadasu to baya taba bata laifi koda kuwa itace bata da gaskiya sai yace au aukw tsokanarta.
Akan haka sun sha samun sabani da Zainab don tana yawan gwada mishi cewa ba daidai bane abinda yakeyi. Bazai yiwu tayi tsokana ba sannan a bawa wanda t tsokana laifi ba wannan ba adalci bane amma sai ya rufe ido ya hau fada yana cewa don ba 'yarta bace yasa take ganin abin da yakeyi a kanta a matsayin rashin kyautawa amma da 'yarya ce yasan ko daga kai baza tayi ta kallesu ba.
A duk sanda irin haka ta faru sai tace mishi "wannan sangartawar fa da kake yiwa Farida ba gata ne kake yi mata ba domin kuwa ita din 'ya mace ce kuma wata rana gidan aure zata je, babu kuma mijin da zai dauki rashin da'a da rashin tarbiyyarta. Wannan wacce irin rayuwace ace yaro duk abinda yayi daidai ne baza'a mishi fada ba idan nayi magana kace na takura mata saboda ba 'yata bace nana tausayin maraicinta".
A yau ga wata rana din da Zainab ke yawan gaya mishi tazo gashi miji ya koro mishi Faridanshi akan halayenta marasa kyau. Allah ya jikan Zainab yayi mata Rahama, har kullum yana jin kewarta tana damunshi ya sani a zamansu bai kyuata mata ba don kuwa bai bata dama tayiwa yaranta irin tarbiyyar da take so ba. Dagowa yayi ya kalli Farida da jar lokacin take a durkushe tana sharar hawaye. A lokacin daya shigo daga ganawarsu da mijinta ranshi a matukar bace yake shine ma dalilim da yasa ya shigo yana kwala mata kira abinda ya fito da Aisha daga kitchen tana tambayarshi lafiya. Zaunar dashi tayi ta kawo mishi ruwa yasha sannan tace mishi bawai zai samu Farida da fada bane, nasiha zaiyi mata ya nuna mata cewa baya son munanan halayenta baiji dadin yadda take tafiyar da al'amuran gidanta ba a cikin nutsuwa ba wai da fada ba.
"Yanzu maigidanki ya bar nan mun kuma tattauna akan yanayin zamanki dashi da kuma iyalinshi. Banji dadi ba yanda yace wai bakya girmamashi bakya girmama matarshi sannan kuma bakya son 'ya'yansgi ba kyaso kiga yana kyakkyawar mu'amala dasu. Wanne irin sonkai ne dake Farida, yaya zakije gidan mata da 'ya'yanta kice wai mijinta bazai yi hulda da ita ba, to a ina aka taba irin haka.
Ai kema kinsan bakiso a zauna lafiya ba. Kin kuma dauki hanyar nesanta kanki ne da mijinki don ko ni nan bazan taba son matar da bata son iyalina ba. Don haka ina horonki da idan kin koma gidanki ki sake tsarin mu'amalarki da maigidanki da kuma iyalinshi.
Dole ne kiso 'ya'yanshi ki kuma yi kyakkyawar mu'amala dasu domin kuwa jema 'ya'yanki ne tunda kina auren ubansu kuma idan har son gaskiya kike yi mishi dole ne kiso duk wanda ke tare dashi don haka tsakaninki da matarshi girmamawa ne ban yarda naji ance kin raina ta ba.
Sannan kuma Farida dole ne ki kasance mai yin biyayya ga dukkan wani umarni na mijinki idan har bai kasance sabon Allah ba. Rashin da'a da tsiwa ba zai sa ki samu soyayyar mijinki ba sai dai ma ya nesanta ki dashi don haka inaso ki ajiye duk wani hali naki marar kyau ki aro kyawawan halaye ki yafa don kema ko zama tauraruwa a wurin mijinki.
Idan kinyi hakan kuma ba wani kika mutunta ba saini don wannan zai nuna cewa kin fito daga gida na tarbiyya tunda gashi kinyi ba daidai ba an gyara miki kuma kin dauka. Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwar aurenki, tashi kije sai ki shirya gobe In Sha Allahu zaki koma gidanki".
Tunda Daddy ya fara magana Farida ke kuka har lokacin daya sallameta. Tashi tayi ta koma daki ta kwanta. Maganganun Daddy ne kawai suke dawo mata a ranta. Ta sani tana son mijinta sai dai kuma tana tsananin kishinshi da ko yaranshi bata so taga yana basu lokacinshi bare uwarsu.
Gashi kuma akayi dace yaran ba da'a ne dasu ba wannan ne yasa ta karaji yaran basuyi mata ba. Kasancewar ta saba a gidansu komai take sobshi take samu yasa tayi tunanin a gidan mijinta ma haka ne zai kasance sai taje ta tarar kwata-kwata rayuwar ba iri daya bace.
Mijinta wani irin mutum ne me son kanshi, bata usa tace anyi mata wani abu ba kama daga yaran har uwarsu sai ya rufe ido ya hau zazzaga mata masifa yana cewa bata isa ta rabashi da familynshi ba don sune rayuwarshi. Kuma fa sunayi mata abubuwa na rashin kirki amma kwata-kwata baya gani saima zuwa da yayi ya hadata da Daddy ya hada da laifinta da wanda ba nata ba duk yace nata ne.
Sai dai In Sha Allahu zata bashi mamaki don kamar yadda Daddy yace ne bada tsiya zata samo kanshi ba, ta kuma sha alwashin sai yaga canji a tare da ita sai ya sota ya mutunta ta a idon duniya kamar yadda yake yiwa matarshi. Zata zame mishi tamkar yadda Aisha ta zamarwa Daddy, zata zamanto mai sonshi mai tattalinshi da farin cikinshi. Zata yi hakuri da duk wani batanci da zata gani daga gareshi ne ko matarshi duk zata jure har sai ya sota tamkar koma fiye da matarshi don ta lura ba wani sonta yake yi ba tafi danganta shi da sha'awarta yakeyi, idan ma kuma akwai son to sha'awar ta rinjayeshi don haka zata koya mishi yadda zai sota ya kuma kaunaceta.
Dole ne ta sauke girman kai ta nemi taimakon Aunty Aisha (rana ta farko da Farida ta yardarwa zuciyarta cewa ta cancanci ta kirata da Aunty) wurin koyon girke-girke da yadda zata kula da muhallinta da mijinta dama wasu abubuwan. Don Ummie ta gaya mata irin problems din data fara fuskanta a wurin mijinta da taimakon Aunty Aisha komai ya zama normal.
Tasan cewa mijinta yafi na Ummie wadata don komai da suke bukata 'yan aiki ne keyi musu, hatta da girki cook ne dasu da yake yi musu shi yasa ita bata samu matsala irin wacce Ummie ta samu ba. Amma yanzu dole ne ta tashi ta koyi abubuwan da ada take ganin ba komai bane tunda tana da masu yi mata, dole ne ta fara ciyar da mijinta abincin da ta dafa da hannunta don bature ma yace the way to a man's heart is through his stomach, to kuwa zata shiga zuciyar mijinta tayi kane-kane ta hanyar ciyarda shi daga abincin da ta sarrafa da hannunta.
BAYAN SHEKARA DAYA
Sanye take cikin leshi daya amsa sunanshi na lace mai matukar kyau da tsada. Kalar cream ne sai akayi mishi ado da zare kalar coffee da golden. Golden costumes tayi amfani da sai dai anyi musu kwallaiya da kananun pearls kalar coffee da cream. Sai mayafi, takalmi da jaka da tayi amfani da kalar coffee. Dinkin rigar buba ne da zani, cikinta dan kimanin watanni shidda ya turo ta cikin rigar.
Taku take yi daidayharvta isa wurin motarta kirar hyundai (elantra) dake ajjiye a harabar gidan ta shiga ta bata wuta sannan ta fita. A bakin gate ta tsaya suka gaisa da maigadi har tayi mishi kyautar dubu daya sannan ta wuce.
Duk da ba nisa ke tsakaninsu da gidan sunan ba amma hakanan taji bazata iya tafiyar kafa shine ma yasa ta fito da mota. Tafiyar 'yan mintuna ce ta kawota gidan. Horn ta danna maigadi ya bude mata gate ta shiga ta samu wuri tayi parking motar.
Cikin takunta na nutsuwa ta nufi cikin gidan. Da sallam a bakinta ta shiga parlour gidan, Farida dake zaune tana bawa yaronta nono tace "oyoyo Mummy, gaskiya munyi fushi tunda sai yanzu kike zuwa sunan ga alama dai bakayi da wannan Daddyn namu". Cikin dariya tace "to me zanzo nayi muku, ai na zauna a gida nima na kula da nawa mijin . Nida ba yanzu ma nyi niyyar zuwa ba Ummie ce ta isheni da waya, tana ina nema?" ta fada tana keken ta inda zata hango Ummie.
Bata zauna ba har sai da ta shiga ciki suka gaisa da maijegon sannan ta dawo ta zauna a parlour. Duk wani nau'i na abincin da akayi a wurin sunan sai da aka kawo mata. Kallon abincin tayi ta cewa Farida "kwashe abincinnan ki maida snacks din kawai sun isheni sai ko alala".
Bayan ta kai abincin ne ta dawo take cewa "Mummy kin kawo mana sakon (suna kiranta Mummy ne yadda su Zainab ke kiranta) don wallahi bakga yadda na matsu kizo ba don kamar na biki gida haka nayi taji".
"Yana mota sai na tashi tafiya sai ku bini ku karba". Daidai lokacin Ummie ta shigo, kusa da Aisha tana cewa "Mummy sannu da zuwa , wallahi ban san kin zo ba ina can Inbtisam ta hanani sakat da rigima, Allah yasa dai kin kawo mana sakon".
"Kai ku dai Allah ya shiryeky wallahi, ji yanda kuka bi kua dameni akan sakonku, to duk me son kayana sai ta ajjiye kudi". "Kai mummy kefa uwace idan ba ke ba wurin wa zamu muce ayi mana, ba girmanki bane kice sai mun biyaki" ta fada tana mai rungumo Aisha.
"Ina su Ruqaiya ne Mummy, da naga ban ganzsu b na dauka tare zaku zo" Farida tace. "Umhh kunsan halin Daddynku cewa yayi baza suzo ba tunda yau akwai islamiyya, ransu a bace suka tafi makarantar".
Bata wani jima ba ta tashi tayi sallama da maijegon (matar Khalifa ce ta haihu, yaron yaci sunan Daddy wato Ja'afar) sannan su Ummie suka rakata har wurin motar, bayan sun karbi sakonsu ne suka yi sallama taja motarta ta koma gida.
A kullum cikin godiyar Allah take idan taga yadda my'amalarta da 'ya'yan mijinta ta canja daga marar kyau zuwa mai kyau. Don a yanzu sosai suke bata grmanta na matar ubansu itama kuma ta rike girmanta da Allah ya bata tana hulda dasu cikin mutunci da mutuntawata kuma yi sa'a Daddy ya kauda idonahi daga harkarsu, komai ya gani a tsakaninsu baya magana don yasan bazata taba cutar dasu ba.
TAMMAT BIHAMDULILLAH
*****
Anan na kawo karshen takaitaccen labari na da nayi wa laqabi da 'YA'YAN MIJI. Ina rokon duk wanda na batawa yayin rubutunnan da ya yafe mini, a kullum dan adam ajizi ne nimakuma na yafewa kowa duk da dai babu wanda ya bata mini.
Har Kullum sadaukarwar ta 'yaruwata ce Fatima (Uwani) da Allah yayi wa rasuwa ina barar addu'a ga duk wanda ya karanta littafin nan a gareta da fatan Allah ya jikanta yayi mata Rahama ya kai hasken Rahamarshi kabarinta ya tasheta a inuwarshi ranar tashin Alqiyama. Mu kuma idan tamu tazo Allah yasa muyi kyakkyawan karshe.
Jinjinar ban girma ga daukacin members na groups din Umm Asghar Novels, Dakin Hausa novvels, Dandalin Hausa Novels, Khaleesat Hydar Novels a facebook da kuma Hausa Novel.
UMMASGHAR.
0 Comments